Aminiya:
2025-04-19@05:29:09 GMT

Zargin Ganduje: Za mu sanar da lokacin yanke hukunci —Kotu

Published: 17th, April 2025 GMT

Mai Shari’a Amina Adamu Aliyu ta Babbar Kotun ta Jihar Kano ta ce za ta yanke hukunci nan gaba a shari’ar cin hanci da rashawa da ake yi wa Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa, Abdullahi Ganduje, da matarsa Hafsat, da wasu mutane da kamfanoni shida.

Gwamnatin Jihar Kano ta tuhumi waɗannan mutane da kamfanoni da laifuka guda takwas da suka haɗa da karɓar rashawa, yin amfani da kuɗin jama’a ta haramtacciyar hanya, da kuma satar kuɗin gwamnati.

Ganduje ya yi gwamnan Jihar Kano daga shekarar 2015 zuwa 2023.

Lauyan Ganduje ya roki kotu da ta ba shi karin lokaci a shari’ar amma lauyan gwamnati ya soke wannan roko kuma ya bukaci kotu da ta yi watsi da shi.

Ka dawo Najeriya ka magance matsalar tsaro —Obi ga Tinubu Gwamnatin Tarayya ta buƙaci ’yan jarida su daina kawo rahoton ayyukan ’yan ta’adda Hisbah ta kama matashi yana ‘lalata’ da Akuya a Kano

Lauyoyin wasu mutane da kamfanoni da ake tuhuma a shari’ar sun kuma gabatar da wasu batutuwa kuma sun roki kotu da ta na su gaskiya tare da umartar gwamnati da ta biya su diyya.

Mai Shari’a Amina Adamu Aliyu ta dakatar da sauraron ƙarar kuma ta ce za ta sanar da dukkan waɗanda abin ya shafa ranar da za ta yanke hukuncinta daga baya.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: rashawa zargi

এছাড়াও পড়ুন:

An taƙaita zirga-zirgar babura da haramta kiwon dare a Filato

Gwamnan Filato, Caleb Mutfwang, ya sanar da haramta kiwo da daddare tare da taƙaita amfani da babura a faɗin jihar sakamakon yawaitar hare-haren da ake kai wa a wasu sassan jihar.

A cikin wani jawabi da ya yi a jihar a ranar Laraba, Mutfwang ya bayyana hare-haren a matsayin “ayyukan ta’addanci” da ke da nufin tarwatsa mazauna yankin da kuma tauye hakkinsu na kasancewa cikin lumana a yankunansu.

Gwamnan ya kuma haramta safarar shanu cikin ababen hawa bayan karfe 7 na dare.

Ya kuma hana amfani da babura daga karfe 7 na yamma zuwa karfe 6 na safe a faɗin jihar har na wani tsawon lokaci inda ya ce umarnin zai fara aiki ne nan take.

Ya ce ” Ina jinjinawa masu ba da agajin gaggawa da jami’an tsaro bisa gaggarumin matakin da suka ɗauka, ina kuma gode wa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya umurci jami’an tsaro da su tabbatar da adalci cikin gaggawa.”

Muftwang ya ce dole ne al’ummomi su ba da himma wajen kare kansu a cikin iyakokin da doka ta tanada.

Ya ce ”Ina kira ga sarakunan gargajiya da shugabannin matasa da su sake farfaɗo da sintiri tare da haɗin gwiwar jami’an tsaro. Dole ne mu haɗa kai don kare ƙasarmu, domin tabbatar adalci yayin da mu ke la’akari da kiyaye dokokin ƙasa.”

Aƙalla mutane 50 ne rahotanni suka ce an kashe bayan wasu ƴan bindiga sun kai hari ƙauyen Kimakpa da ke gundumar Miango a ƙaramar hukumar Bassa ta jihar a ranar 14 ga watan Afrilu.

Harin ya zo ne makonni biyu kacal bayan da wasu ƴan bindiga suka kashe mazauna ƙauyuka biyar a ƙananan hukumomin Bokkos da Mangu.

Hukumomin ƙasar dai na ci gaba da ƙoƙarin ganin sun daƙile hare-hare a jihar da aka daɗe ana fama da rikicin kabilanci da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnati Ta Ware Wata 14 Don Kammala Aikin Hanyar Abuja Zuwa Zariya
  • Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar Da Taron Ƙarawa Ma’aikatan Jinƙai Sani A Jihar Kano
  • EFCC Ta Kama Wasu Mutane 40 Da Ake Zargi Da Yin Damfara Ta Intanet A Neja
  • ‘Yan tawayen Sudan sun kafa tasu gwamnati
  • An taƙaita zirga-zirgar babura da haramta kiwon dare a Filato
  • Yadiot Ahranot: Amurka Ta Bayyana Lokacin Ficewarta Daga Syria
  • Matashin Da Ya Ƙware Wajen Kashe Mutane Da Ƙwace Ya Miƙa Kansa Ga ‘Yansanda A Kano
  • Kotu ta yanke wa tsohon Shugaban Peru ɗaurin shekaru 15 kan laifin rashawa
  • Kotu ta yanke wa tsohon Shugaban Peru ɗaurin shekaru 15