Iran Ta Damu Akan Mummunan Yanayin Da Mutanen Al-Fasha Na Sudan Suke Ciki
Published: 17th, April 2025 GMT
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Dr. Isma’ila Baka’i ya bayyana cewa; Yanayin da mutanen garin al-fasha na Sudan suke ciki ya yi muni, tare da yin kira da a kawo karshe killace garin da aka yi da kuma bai wa fararen hula kariya.
Mayakan “Rundunar Kai Daukin Gaggawa” dake fada da sojojin Sudan ta shimfida ikonta akan sansanin ‘yan hijira na “Zamzam’ bayan kwanaki na barkewar fada a kusa da birnin al-fasha.
Daruruwan mutane ne su ka rasa rayukansu yayin da wani adadi mai yawa na ‘yan hijirar ya jikkata.
Dr. Isma’ila Baka’i ya bayyana matsayar jamhuriyar musulunci ta Iran na nuna cikakken goyon bayan Sudan a matsayin dunkulalliyar kasa.
A bisa kididdigar MDD a kalla mutane 300 aka kashe a kusa da wannan sansanin na Zamzam a fadan da aka yi a ranakun Juma’a da Asabar.
Har ila yau MDD ta kuma ce,wani adadin na mazauna yankunan Zamzan da Abu Shok da garin al-Fashar da sun kai 400,000 an tilasta musu ficewa daga gidajensu. Haka nan kuma wasu mutanen da sun kai miliyan 13 sun gudu, zuwa inda za su sami aminci a cikin gida da kuma wajen kasar.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Wakilin Sin Ya Yi Kira Da A Yi Aiki Tare Don Daidaita Mummunan Yanayi A Yankin Manyan Tabkuna Na Afirka
Zaunannen wakilin kasar Sin a MDD, Fu Cong, ya bayyana a gun taron kwamitin sulhu na MDD game da yankin manyan tabkuna na Afirka a ranar 16 ga wata cewa, sakamakon ci gaba da kai hare-hare na kungiyar M23 a baya-bayan nan, ya ta’azzara yakin gabashin Kongo DRC, kuma daukacin yankin manyan tabkuna sun fada cikin rudani. Dole ne kasashen duniya su yi aiki tare kuma su hada kai don kawar da wannan mummunar yanayin cikin gaggawa.
Fu Cong ya jaddada cewa, dole ne a gaggauta tsagaita bude wuta domin hana shi ci gaba da ruruwa. Babu wata hanyar soji da za ta magance rikicin gabashin Kongo DRC, kuma tattaunawa ta siyasa ita ce kawai mafita. Dole ne kasashen duniya su dauki kwararan matakai don tallafa wa kasashen yankin manyan tabkuna wajen magance tushen matsalolin da ke haifar da gazawar shugabanci da rashin daidaituwar ci gaba a yankin. (Mai fassara: Mohammed Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp