Najeriya da gwamnatin sojin Nijar sun sasanta
Published: 17th, April 2025 GMT
Gwmanatin Sojin Nijar ta sanar da cewa sun sasanta da gwamnatin Najeriya.
Hakan ta faru ne bayan ziyarar aiki da Ministan Harkokin Wajen Najeriya, Yusuf Tuggar ya kai birnin Yamai, fadar gwamnatin Nijar.
Bayan sanya hannu kan takardar, Ministan Harkokin Wajen Nijar, Bakary Yaou Sangare, ya bayyana cewa, “da ma Najeriya ’yan uwanmu ne, duk wanda ya ce zai raba Nijar da Najeriya, shi da kansa ya san ba gaskiya ba ne, abu ne na Allah.
Takwaransa na Najeriya, Yusuf Tuggar, ya bayyana cewa nan gaba Shugaba Bola Ahmed Tinubu za su gana da shugaban gwamnatin sojin Nijar, Janar Abdurrahman Tchiani, a matsayin ci gaban wannan daidaitawa.
Ya bayyana cewa yarjejeniyar da ƙasashen biyu suka sanya hannu a kai, ta zama, “darasi ga duk wasu ƙasashen duniya, domin yanzu an shiga wani lokaci da ake fama da tashe tashen hankali. To yanzu mu abin da a muka a tsakaninmu ya zama abin koyi.”
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: gwamnatin sojin Nijar Najeriya Nijar Tuggar Yamai
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Jigawa Za Ta Yi Garambawul A Fannin Kiwon Lafiya
Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya sake jaddada kudurin gwamnatinsa na yin garambawul a fannin kiwon lafiya ta hanyar sanya tubalin gina sabbin cibiyoyin lafiya guda uku, da suka hada da Cibiyar Gwaji ta zamani, da Cibiyar kula da lafiyar Zuciya, da cibiyar samar da iskar numfashi (Cryo-Oxygen Plant) a Fanisau, da ke Dutse, babban birnin jihar.
Wadannan ayyuka, wadanda za su ci biliyoyin nairori, wani bangare ne na hangen nesan gwamnatin na mayar da Dutse cibiyar yawon bude ido kan kiwon lafiya a yankin.
A yayin bikin, Gwamna Namadi ya bayyana cewa wannan rana ta shiga kundin tarihi a ci gaban jihar.
Ya bayyana cewa an tsara wadannan cibiyoyin ne domin kara karfin jihar wajen samar da ingantaccen kula da lafiya da rage dogaro da wasu jihohi ko kasashen waje, domin neman lafiya.
Namadi ya bayyana wasu daga cikin nasarorin da gwamnatinsa ta samu da suka hada da shigar da mutane masu bukata ta musamman sama da dubu 143 cikin shirin inshorar lafiyar al’umma, da kuma farfado da asibitocin matakin farko da na biyu.
Malam Namadi ya bayyana cewa kudin farko zai fito ne daga baitul malin jihar, amma a tsawon lokaci, ana shirin tafiyar da cibiyoyin a karkashin hadin gwiwa tsakanin gwamnati da masu zaman kansu (PPP).
Ya ce wannan tsari zai tabbatar da dorewa mai inganci, tare da kawar da bukatar tafiye-tafiye zuwa wasu jihohi domin yin gwaje gwaje kamar su MRI da ke nuna hoton jikin mutum baki daya da kuma cutar da ke damunsa da kuma yin gwajin cutar sankarar Mama wato mammography.
Malam Namadi ya ce masana’antar samar da iskar numfashi ta Cryo-Oxygen za ta rika samar da kashi 100 bisa 100 na iskar oxygen mai tsafta don asibitoci, da kuma na nitrogen don amfani a masana’antar takin zamani a Najeriya.
Gwamnan ya kuma yi bayanin wasu ayyuka da ake yi a fannin lafiya da suka hada da asibitin kashi na Gumel, da asibitocin kwararru a Hadejia da Kazaure, da kuma fadada ayyukan wanke koda kyauta.
Ya bayyana cewa gwamnati ta amince da bayar da magani kyauta ga masu ciwon siga, da hawan jini, da masu cutar sikila.
Dangane da inganta ma’aikata, Gwamna Namadi ya sanar da daukar ma’aikatan lafiya sama da 920 a matakin farko, da ma’aikatan jinya 200, tare da na wucin gadi 1,000.
Ya bukaci ma’aikatan lafiya da su nuna kishi da sadaukarwa, inda ya gargadi cewa ba za lamunci sakaci da aiki da rashin da’a ba.
Gwamnan ya kuma yaba wa manyan abokan cigaban jihar kamar su UNICEF, WHO, USAID, FCDO, da gidauniyar Bill & Melinda Gates, tare da shugabannin gargajiya da na addini bisa goyon bayan da suke ci gaba da bayarwa wajen wayar da kan jama’a a fannin lafiya a fadin Jihar Jigawa.
Usman Muhammad Zaria