HausaTv:
2025-04-19@05:29:08 GMT

 Sojojin HKI Suna Ci Gaba Da Kai Hare-hare A Kudancin Lebanon

Published: 17th, April 2025 GMT

Sojojin HKI suna cigaba da kai hare-hare a yankunan kudancin Lebanon da ya zama ruwan dare a cikin kwanakin bayan nan.

A jiya Laraba jiragen yakin HKI sun kai hare-hare a gari “Aytas-sha’ab. Haka nan kuma tankokin yakin ‘yan mamayar sun kai wasu hari a kan wasu gidaje a garin na Aytas-sha’ab.

Haka nan kuma sojojin mamayar sun gina wata Katanga da ta raba tsakanin Ayta da Khillatul-wardi.

Har yanzu sojojin na HKI suna ci gaba da zama a cikin wasu wurare biyar da ta ki ficewa daga cikinsu bayan zuwa karshen wa’adin kwanaki 60 daga tsagaita wutar yaki.

Kamfanin dillancin labarun Lebanon ya bayyana cewa; Jirgin yakin HKI maras matuki ya kai hari akan gidajen tafi da gidanka da wadanda aka rushewa gidaje suke ciki a kusa da garin Shaihin. Sai dai babu wani rahoto akan rashin rai,ko jikkatar mutane, sai dai gidaje da dama sun rushe.

Wadannan hare-haren suna a matsayin sabon bude wuce gona da iri na HKI a kudancin Lebanon.

Kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon din ta sha yin kira ga gwamnati da ta yi aiki da nauyin da ya rataya a wuyanta na tilasata wa ‘yan mamaya janyewa daga wuraren da suke ciki.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

An taƙaita zirga-zirgar babura da haramta kiwon dare a Filato

Gwamnan Filato, Caleb Mutfwang, ya sanar da haramta kiwo da daddare tare da taƙaita amfani da babura a faɗin jihar sakamakon yawaitar hare-haren da ake kai wa a wasu sassan jihar.

A cikin wani jawabi da ya yi a jihar a ranar Laraba, Mutfwang ya bayyana hare-haren a matsayin “ayyukan ta’addanci” da ke da nufin tarwatsa mazauna yankin da kuma tauye hakkinsu na kasancewa cikin lumana a yankunansu.

Gwamnan ya kuma haramta safarar shanu cikin ababen hawa bayan karfe 7 na dare.

Ya kuma hana amfani da babura daga karfe 7 na yamma zuwa karfe 6 na safe a faɗin jihar har na wani tsawon lokaci inda ya ce umarnin zai fara aiki ne nan take.

Ya ce ” Ina jinjinawa masu ba da agajin gaggawa da jami’an tsaro bisa gaggarumin matakin da suka ɗauka, ina kuma gode wa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya umurci jami’an tsaro da su tabbatar da adalci cikin gaggawa.”

Muftwang ya ce dole ne al’ummomi su ba da himma wajen kare kansu a cikin iyakokin da doka ta tanada.

Ya ce ”Ina kira ga sarakunan gargajiya da shugabannin matasa da su sake farfaɗo da sintiri tare da haɗin gwiwar jami’an tsaro. Dole ne mu haɗa kai don kare ƙasarmu, domin tabbatar adalci yayin da mu ke la’akari da kiyaye dokokin ƙasa.”

Aƙalla mutane 50 ne rahotanni suka ce an kashe bayan wasu ƴan bindiga sun kai hari ƙauyen Kimakpa da ke gundumar Miango a ƙaramar hukumar Bassa ta jihar a ranar 14 ga watan Afrilu.

Harin ya zo ne makonni biyu kacal bayan da wasu ƴan bindiga suka kashe mazauna ƙauyuka biyar a ƙananan hukumomin Bokkos da Mangu.

Hukumomin ƙasar dai na ci gaba da ƙoƙarin ganin sun daƙile hare-hare a jihar da aka daɗe ana fama da rikicin kabilanci da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Sojojin Kasar Yemen Sun Kai Hare Hare Kan HKI Da Jiragen Yakin Amurka
  • Ya kashe masoyin tsohuwar matarsa bayan sakinta a Neja
  • Benuwe: Har yanzu ba a gano wasu mutanen ƙauyuka ba – Gwamna Alia
  • Sojoji Sun Kashe ‘Yan Ta’adda a Sambisa da Kudancin Tumbun
  • Matar gwamna ta ɗauki nauyin ragon suna da hidimar duk matar da ta haifi ’yan uku a Sakkwato
  • Ba a taɓa Dimokraɗiyya mai tsafta a Najeriya kamar mulkin Tinubu ba – Matawalle
  • Batawa Sin Suna Ba Zai Taimaka Kawar Da Tambarin Amurka A Matsayin Daular Kutsen Intanet Ba
  • An taƙaita zirga-zirgar babura da haramta kiwon dare a Filato
  • A Kalla Mutane 9 Ne Su Ka Yi Shahada A Gaza