Majalisar Dokokin Zamfara Ta Dawo da Dan Majalisa Basko da Aka Dakatar
Published: 17th, April 2025 GMT
Majalisar dokokin jihar Zamfara ta mayar da dan majalisar dokokin jihar Zamfara da aka dakatar, Shamsudeen Hassan Basko, mai wakiltar mazabar Talata Mafara ta Arewa, bayan da ya nemi gafarar majalisar.
Hakan ya fito ne a wata sanarwa da sakataren yada labaran majalisar Bello Madaro ya raba wa manema labarai a Gusau.
A zaman da aka yi, Kakakin Majalisar, Alhaji Bilyaminu Ismail Moriki, ya karanta abin da ke cikin wasikar neman afuwar Basko, inda daga nan ne ya nemi shawarar majalisar ta gamayya inda ‘yan majalisar suka amince da dage dakatarwar.
Shugaban majalisar ya jaddada bude kofar majalisar na karbar irin wasikun neman afuwa daga sauran ‘yan majalisar bakwai da aka dakatar, inda ya ce irin wadannan matakai za su ba su damar dawo da su tare da samar da hadin kai a cikin majalisar.
Mambobin sun kuma yi masa maraba da komawa zauren majalisar, sannan sun bukaci sauran mambobin da aka dakatar da su yi koyi da ayyukansa domin tabbatar da zaman lafiya da ci gaban mazabarsu da jihar baki daya.
A takaitacciyar jawabinsa, Shamsudeen Hassan Basko ya bayyana matukar godiya ga majalisar bisa damar da ta samu ta mayardashi.
Basko ya yi alkawarin ci gaba da bin ka’ida, da’a na Majalisar, ya kuma sha alwashin nisantar da kansa daga duk wata kungiya ko yin tasiri da ke yunkurin bata mutunci da ikon majalisar.
Idan dai za a iya tunawa, a ranar 26 ga watan Fabrairun 2024 ne majalisar, bayan wani kudiri da shugaban masu rinjaye, Bello Mazawaje ya gabatar, ta dakatar da mambobinta takwas bisa saba wa kundin tsarin mulkin majalisar (Oda 10, Doka ta 9).
Matakin ladabtarwar dai ya samo asali ne daga zarge-zargen da ake yi masa, wanda ya hada da shigar karfi da yaji a ofishin magatakarda da zama ba bisa ka’ida ba, da dakile ayyukan majalisa, da kuma gudanar da ayyukan da ake ganin bai dace da ‘yan majalisar ba.
REL/AMINU DALHATU.
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Zamfara da aka dakatar
এছাড়াও পড়ুন:
Dalilin da Kwankwaso zai dawo APC — Ganduje
Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dokta Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa ƙiris ya rage madugun jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya dawo jam’iyyarsu ta APC.
Gamduje ya bayyana hakan ne yana mai cewa jam’iyyar NNPP ta mutu murus, kuma jana’izarta kaɗai suke jira a gudanar a nan kusa.
Gwamnatin Tarayya ta ayyana hutu ranar Juma’a da Litinin Barcelona da PSG sun tsallaka zagayen kusa da na ƙarshe a Gasar Zakarun TuraiGanduje ya bayyana haka ne a ranar Talata yayin ziyarar da wata ƙungiya mai goyon bayan Shugaba Bola Tinubu (TSG) ta kai sakatariyar APC ta ƙasa da ke Abuja.
Ganduje ya ce APC a kodayaushe tana cikin shirin karɓar jiga-jigan ‘yan siyasa ciki har da Kwankwaso “idan har ya yanke shawarar dawowa gida.”
Ganduje ya bayyana cewa jam’iyyar NNPP ta rasa duk wani karfi da tasiri da take da shi, musamman a Jihar Kano, inda ya ce ‘yan jam’iyyar da dama sun bar ta.
Ya ce: “NNPP ta mutu. Kuma ba da jimawa ba za a birne ta. Amma abin da ya rage shi ne a haƙa kabari, kuma har an fara hakan. Muna jiran a kammala shiri ne kawai.”
A cewarsa, “Kwankwason ya fara yunƙurin dawowa APC saboda ya fahimci cewa ya rasa komai a jam’iyyar da ya tallata.”
“Ƙofa a buɗe take ga duk wanda ya shirya dawowa APC”, yana mai cewa Kwankwaso zai samu tarba mai kyau idan ya dawo gida.
“Za mu karɓe shi idan ya dawo, domin gida zai dawo,” in ji Ganduje.
Ya ƙara da cewa APC ta na ci gaba da karɓar fitattun ‘yan siyasa daga sassa daban-daban, wanda hakan ke ƙara ƙarfafa jam’iyyar a faɗin ƙasar.
Haɗakar ’yan adawa ba za ta yi tasiri ba — GandujeShugaban jam’iyyar ta APC ya kuma ce haɗakar da wasu ‘yan siyasa ke ƙoƙarin yi domin ƙalubalantar Shugaba Tinubu a Zaɓen 2027 ba za ta yi tasiri ba “domin kuwa rushewa za ta yi kafin a je ko’ina.”
Ganduje ya ce: “Wannan haɗakar da ake ta surutai a kai, za ta tarwatse kafin ta gama haɗuwa. Yawancin su za su dawo cikin APC, domin sun san cewa nan ne gida.”
Ganduje ya jaddada cewa jam’iyyar APC za ta ci gaba da jan ragamar mulki a Nijeriya saboda ingantattun manufofi da kuma salon shugabancin Tinubu.