HausaTv:
2025-04-19@05:27:55 GMT

Kasar Pakistan Ta Kara Jaddada Dokar Rashin Amincewa Da HKI A Matsayi Kasa

Published: 17th, April 2025 GMT

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Pakisatan ta kara jaddada matsayinta na rashin amince da HKI a matsayin kasa tana kuma goyon bayan Falasdinawa a gwagwarmayan da suke yi na kwatar yencinsu da kuma kasarsu daga hannun HKI da kuma kasashen yamma musamman Amurka masu goya mata.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran wannan sanarwan tazo ne bayan da hukumar kare hakkin bil’adama ta MDD ta samar da wani kuduri dangane da rikicin da ke faruwa a gabas ta tsakiya.

  A dai-dai lokacinda aka kara yawan tashe-tashen hankula a kasar Falasdinu da aka mamaye tsakanin HKI da kuma Falasdinawa masu gwagwarmaya. Kungiyar kasashe masu musulmi mafi rinjaye wato OIC ta yanke  shawara kan cewa bai kamata kasashen su samar da huldar Diblomasiyya da HKI ba.  Ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Pakisatn ta bayyana cewa, kafafen yada labarai da dama sun watsa labaran cewa kasar ta Canza matsayinta dangane da kudurin hukumar kare hakkin bil’adama ta MDD dangane da rikicin nag abas ta tsakiya, ta kuma kara da cewa wannan labarin ba gaskiya bane. Saboda kasar Pakistan tana tare da kungiyar OIC dangane da goyon bayan al-ummar Falasdinu. Don haka Pakisatan bata amincea da samuwar HKI ba. Har’ila yau majalisar kasa ta kasar Pakisatn ta amince da babban rinjaye ko kuma gaba dayan yan majalisar da rashin amincea da HKI da kuma goyon bayan Falasdinawa.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Bayyana Makasudin Rubuta Sakon Jagora Ga Shugaban Kasar Rasha

Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Sakon jagora ga shugaban kasar Rasha yana da alaka da ci gaban kasa da kasa da na yanki

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya bayyana hakan ne a yau Alhamis a birnin Moscow na kasar Rasha cewa: Abu ne da ya dace a rubuta sakon da Jagoran juyin juya halin Musulunci ya aikewa shugaban kasar Rasha dangane da ci gaban kasa da kasa da na yanki da kuma batutuwan da suka shafi kasashen biyu.

Araqchi ya bayyana hakan ne a lokacin da ya isa filin tashi da saukar jiragen sama na Vnukovo da ke birnin Moscow a yau, yayin da yake amsa tambayar da wakilin IRNA ya yi masa kan abubuwan da ke cikin sakon jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei zuwa ga shugaban kasar Rasha Vladimir Putin.

Ministan harkokin wajen kasar Iran ya kara da cewa: Ziyarar tasa tana da manufofi daban-daban, yana mai bayanin cewa, tun da farko an shirya ziyarar ne domin isar da rubutaccen sako daga Jagoran juyin juya halin Musulunci ga shugaban kasar Rasha, kuma ta zo daidai da abubuwan da suka faru a baya-bayan nan da kuma tattaunawa ta kai tsaye.

Ya kara da cewa, tun a baya, har ya zuwa yanzu, a ko da yaushe Iran tana gudanar da shawarwari na kut-da-kut da abokanta na kasar Rasha kan batun makamashin nukiliya, yana mai cewa, suna kuma tattaunawa da Rasha da China, kuma a yanzu da aka samu damar da ta dace, za a iya yin shawarwari tare da jami’an Rasha.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kwararru Sun Yi Musayar Ra’ayoyi Dangane Da Wayewar Kan Sin Da Afirka 
  • Yadda Hukuncin Kotun Koli Ya Kara Dagula Rikicin Shugabanci A PDP Da LP
  • Sojojin Kasar Yemen Sun Kai Hare Hare Kan HKI Da Jiragen Yakin Amurka
  • Jagora: Iran a shirye take domin aiki kafada da kafada tare da  Saudiyya
  • Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Bayyana Makasudin Rubuta Sakon Jagora Ga Shugaban Kasar Rasha
  • Majalisar Kasa Ta Rasha Ta Amince Da Yarjeniyar Dangantaka Ta Musamman Tsakanin Iran Da Kasar
  • An Yi Kira Ga Jihohi Da Su Kara Samar Da Ingantacciyar Hanyar Kiyon Lafiya
  • An Watsa Shirin Bidiyon “Bayanan Magabata Masu Jan Hankalin Xi Jinping” A Kasar Malaysia
  • Barcelona da PSG sun tsallaka zagayen kusa da na ƙarshe a Gasar Zakarun Turai