Hukumar UNICEF ta MDD mai kula da yara ta bada sanarwan cewa kimani yara 3,500 suka rasa rayukansu a kokarin ketara tekun Medeteranina a cikin shekaru 10 da suka gabata.

Kamfanin dillancin labaran Spunic na kasar Rasha ya nakalto hukumar tana fadar haka a wani rahoton da ta fitar dangane da hakan.

Labarin ya kara da cewa, wannan ya nuna cewa akalla yaro guda ne ya ransa ransa a ko wace rana.

Kuma kashi 7/10 daga cikinsu sun halaka ko sun bace ne su kai ba ba tare da rakiyar iyayensu ba. Har’ila yau rahoton ya kara da cewa akalla mutane 20,803 suka halaka a tsakiyar tekun na Mediterranean a kokarinsu na tsallakawa zuwa kasashen na turai.

Daga karshe hukumar tace ba za’a iya sanin hakikanin adadin wadanda suka halaka ba saboda a cikin wasu kwale-kwalen babu wanda ya rayuwa da za’a sami labara daga wajensa ba.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

An kashe sojoji, fararen hula da dama a Borno

Wasu ’yan ta’adda da ake kyautata zaton ’yan Boko Haram ne sun kai hari a sabuwar unguwar Yamtake da ke Ƙaramar hukumar Gwoza a Jihar Borno, inda suka kashe sojoji biyu tare da wasu fararen hula da ba a bayyana adadinsu ba.

Majiyoyin tsaro da na cikin gida sun tabbatar da harin, inda suka ce maharan sun mamaye unguwannin ne da misalin ƙarfe 11:15 na daren Alhamis.

Gwamnatin Yobe ta sayo hatsi don tunkarar kakar bana Matan da suka tsira daga Boko Haram na buƙatar tallafin musamman

Ɗaya daga cikin majiyar sojojin ta ce, kafin a aike da wata tawagar sojoji daga Gwoza, maharan sun riga sun afkawa jama’a  da sansanin sojan Yamtake.

“Muna jiran tawagar masu ƙarfafa musu su dawo, amma mun sami labarin cewa mutane biyu daga cikin jami’anmu da wasu fararen hula harin ya shafe su. Ina ba da shawarar mu jira har sai sun dawo,” in ji shi.

Sai dai Sanata Ali Ndume, ya ce tun lokacin da lamarin ya faru yana tuntuɓar al’ummar unguwar Yamtake.

“Abin takaici ne cewa mutanenmu a ƙauyen Yamtake sun fuskanci mummunan harin Boko Haram a daren ranar Alhamis, ɗaya ne daga cikin unguwannin da suka karɓi ’yan gudun hijirar kwanan nan, gwamnatin Jihar Borno ta sake tsugunar da su.

“Abin baƙin ciki ne yadda sojoji biyu suka rasa ransu a bakin aiki, yayin da wasu fararen hula da ba a san ko su wanene ba na daga cikin waɗanda suka jikkata, Allah Ya gafarta musu.

“Amma kuma na yabawa Birgediya Janar Nasir Abdullahi, Birgediya Kwamanda na runduna ta 26 Task Force da jiga-jigan sojojinsa kan sadaukarwar da suka yi ba tare da ƙaƙƙautawa ba wajen daƙile hare-hare da dama, musamman waɗanda aka yi yunƙurin kaiwa farmakin a garin Gwoza.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Yadda Hukuncin Kotun Koli Ya Kara Dagula Rikicin Shugabanci A PDP Da LP
  • Yawan Mutanen Da Suka Yi Shahada A Harin Amurka Na Jiya A Yemen Ya Kai 74
  • An kashe sojoji, fararen hula da dama a Borno
  • Sojojin Haramtacciyar Kasar Isra’ila Sun Kona Yara Da Mata A Harin Da Suka Kai Khum Yunis Na Gaza
  • ’Yan bindiga sun sace makiyaya 5, da shanu 1,200 a Kaduna
  • An Yi Kira Ga Jihohi Da Su Kara Samar Da Ingantacciyar Hanyar Kiyon Lafiya
  • Mizanin Hada-hadar Tattalin Arzikin Kasar Sin Ya Karu Da Kashi 5.4% A Rubu’in Farko Na Bana
  • KADGIS Za Ta Yi Amfani Da Sabuwar Manhajar Biyan Diyyar Filaye A Kaduna
  • KADGIS Ta Samar Da Sabuwar Manhajar Biyan Diyyar Filaye A Kaduna