Majalisar kasa ta kasar Rasha ta amince da yarjeniyar dangantaka ta musamman tsakanin kasar da JMI a ranar 8 ga watan Afrilun da muke ciki sannan ana saran shugaban kasa Vladimir Putin zai sanyawa yarjeniyar hannu a nan gaba.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa yarjeniyar ta musamman mai kuma dogon zango na shekaru 20 zai bawa kasashen biyu damar tallafawa juna da kuma aiki tare da bangarori daban-daban wadanda suka hada da tsaro makamashi kimiyya da fasaha da sauransu.

Labarin ya kara da cewa idan yarjeniyar ya fara aiki kasashen biyu suna da damar kyautata dangantaka a tsakaninsu, wanda zai rage dogaro da suke yi da kasashen yamma a bangarori da dama.

Dangantakar Tehran da Mosco tana kara karfi ne a dai dai lokacinda al-amuran tsaro suke kara tabarbarewa a yanking abas ta tsakiya. Har’ila yau a dai dai lokacinda kasashen biyu suke fama da takunkuman tattalin arziki mafi muni daga kasashen yamma saboda yaki tsakanin Rasha da Ukraine da kuma shirin makamashin nukliya na kasar Iran da kuma siyasarta a kudancin Asiya.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Pezeshkian: Hadin gwiwar Iran da Saudiyya zai zama abin koyi ga dukkanin kasashen yankin

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya ce Jamhuriyar Musulunci ta Iran da Saudiyya za su iya zama abin koyi ga hadin gwiwar yankin, yana mai jaddada cewa hadin kan kasashen musulmi wani lamari ne da ake bukata don samun zaman lafiya, tsaro, da ci gaban tattalin arziki mai dorewa a yankin.

Pezeshkian ya bayyana hakan ne a yayin ganawa da ya yi da ministan tsaron kasar Saudiyya Yarima Khalid bin Salman da tawagarsa a birnin Tehran, bayan da ministan na Saudiyya ya isa babban birnin kasar Iran domin tattauna batutuwan da suka shafi yankin da alakar kasashen biyu.

Shugaban na Iran ya jaddada zurfafa dangantakar addini da al’adu da tarihi a tsakanin kasashen musulmi, yana mai jaddada wajabcin karfafa hadin kai a duniyar musulmi.

Shugabar kasar ta Iran ya ce: al’ummar Saudiyya ‘yan uwanmu ne, kuma tun farkon kama aikin gwamnatinmu, mun yi kokarin karfafa alakar ‘yan uwantaka a tsakanin dukkanin kasashen musulmi. Ya kara da cewa, idan kasashen musulmi suka cimma matsaya ta bai daya da hadin kai na hakika, to gwamnatin yahudawan  sahyoniya ba za ta sake haifar da bala’i irin na kisan  bil’adama a yankin ba kamar yadda suke yi yanzu a zirin Gaza.

Ya kuma tabo batun muhimmancin ajiye bambance-bambance a gefe, da inganta hadin gwiwa a yankin.

Pezeshkian ya jaddada cewa, “Shugabannin kasashen musulmi za su iya yin aiki tare, kuma su gabatar da wani abin koyi na rayuwa tare, da wadata, da ci gaba ga sauran al’ummomi na duniya.

Ya kuma yaba da ra’ayin kafa kungiyoyin aiki na hadin gwiwa a bangarori daban-daban na siyasa, tattalin arziki da tsaro tsakanin Iran da Saudiyya.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Jagora: Iran a shirye take domin aiki kafada da kafada tare da  Saudiyya
  • Pezeshkian: Hadin gwiwar Iran da Saudiyya zai zama abin koyi ga dukkanin kasashen yankin
  • Araqchi ya mika rubutaccen sakon Jagora ga Shugaba Putin na Rasha
  • Sin Da Malaysia Za Su Samar Sabbin Shekaru 50 Masu Muhimmanci Na Dangantakar Kasashen Biyu
  • Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Bayyana Makasudin Rubuta Sakon Jagora Ga Shugaban Kasar Rasha
  • Babban Jami’in Diblomasiyyar Iran Ya Je Birnin Mosco Don Isar Da Sakon Imam Khaminae Ga Putin
  • Kasar Pakistan Ta Kara Jaddada Dokar Rashin Amincewa Da HKI A Matsayi Kasa
  • Rasha ta ce tana bibiyar tattaunawar Iran da Amurka matuka
  • An Watsa Shirin Bidiyon “Bayanan Magabata Masu Jan Hankalin Xi Jinping” A Kasar Malaysia