Babban Jami’in Diblomasiyyar Iran Ya Je Birnin Mosco Don Isar Da Sakon Imam Khaminae Ga Putin
Published: 17th, April 2025 GMT
Ministan Harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya je kasar Rasha a safiyar yau Alhamis don isar da sakon jagoran juyin juya halin musulunci Imam Sayyid Aliyul Khaminaei zuwa shugaban kasar Rasha Vladimir Putin.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa wannan sakon na zuwa ne rana guda da amincewar majalisar dojojin kasar Rasha ta dangantaka ta musamman tsakanin kasashen biyu, mai tsawon shekaru 20.
Har’ila yau da kuma kwanaki biyu kafin a gudanar da tattaunawa na biyu tsakanin Iran da Amurka dangane da shirin ta na makamashin Nukliya a birnin Roma na kasar Italiya.
Masana dai sun bayyana cewa kasashen Rasha da Iran suna kara dankon zumunci a tsakaninsu ne a dai-dai lokacinda al-amura da dama suke sauyawa a yankin Asiya da kuma duniya.
Har’ila yau a jiya Larabace ministan ya gana da shugaban hukumar makamashin Nukliya ta duniya Raafael Grossi dangane da shirin makamashin nukliya na kasar Iran
A ranar Asabar mai zuwa ne za’a gudanar da tattaunawa karo na biyu tsakanin Iran da Amurka.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Iraki Ce Zata Amfana Da Tattaunawa Tsakanin Iran Da Amurka: Inji Sayyed Ammar Hakim
Sayyid Ammar Hakim shugaban jam’iyyar ‘ تيار الحكمة الوطني’ na kasar Iraki ya bayyana cewa kasar Iraki ce kasa ta farko wacce zata amfani da tattaunawa tsakanin Iran da kasar Amurka.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto sayyid hakim yana fadar haka a jiya, ya kuma kara da cewa kasashen Iran da Iraki suna da gangantaka da musulunci makobtaka da kuma al-adu masu yawa. Don haka a duk lokacinda Amurka suka kyautata tsakanin Iran da Amurka kasashen biyu suna iya bude kan iyakokinsu don mu’amala da juna ba tare da Amurka ta shiga tsakanin ba.
A wani waje a cikin jawabinsa Hakim ya amince da ruwan da gwamnatin kasar Amurka ta taka wajen kauda tsohuwar gwamnatin kama karya na sadam Husaini. Da kuma kawo tsarin democradiyya wanda ya bawa mutanen kasar Iraki sararawa daga musibun sadam Husain a kan mutanen kasar.
Ya kuma kammala da cewa ‘amminsa shahid Bakir Hakim’ ya taba fadar cewa akwai bukatar mutanen kasar Iran su tattaunawa tsakaninsu da kasar Amurka don tabbatar da zaman lafiya a yankin Asiya ta kudu.