Rurum Ya Shawarci Mafarautan Arewa Da Su Daina Zuwa Kudu Farauta
Published: 17th, April 2025 GMT
Ya bayyana cewa shiga wani yanki da ba a fahimtar yaren juna ɗauke da makamai na iya janyo fargaba da tashin hankali.
“Ka yi tunanin idan wasu daga Kudu sun shigo ƙauyanku ɗauke da makamai kuma ba ku fahimtar yaren juna — za ku ji tsoro. Haka nan idan mutanenmu suka shiga yankin Kudu da makamai, su ma za a ji tsoro,” in ji shi.
Rurum ya ce zai gana da shugabannin ƙungiyoyin masu farauta a jihar domin daƙile wannan ɗabi’a, ya kuma buƙace su da su nemo hanyar nema wa kansu asiri .
“Wasu su tafi farauta su dawo ba tare da sun kamo ko ɓeran daji ba. Bai dace su ci gaba da haka ba. Ya kamata mu nemi wata hanya ta zaman lafiya da kwanciyar hankali,” in ji shi.
Haka kuma, ya bayar da gudunmawar naira miliyan biyar ga iyalan waɗanda suka rasu, sannan ya sha alwashin gina makaranta a garin domin girmama su.
Rurum ya kuma ce zai haɗa kai da Sanata Kawu Sumaila domin su kai ƙudiri a majalisa a kan kisan da aka yi wa mafarautan jihar a garin Uromi don ganin an yi wa waɗanda abin ya shafa adalci.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Tarayya ta buƙaci ’yan jarida su daina kawo rahoton ayyukan ’yan ta’adda
Gwamnatin Tarayya ta nemi kafafen watsa labarai da su daina kawo rahoton ayyukan ‘yan ta’addan da ke tada hankali a jihohin Filato, Borno, Zamfara, Binuwai, da sauransu.
Aminiya ta rawaito cewa jihohin na fama da tashe-tashen hankula musamman a baya-bayan nan in da aka yi asarar rayuka da dukiyoyin al’umma.
Dangote ya karya farashin fetur karo na biyu a mako guda Hisbah ta kama matashi yana ‘baɗala’ da Akuya a KanoWannan ya sanya wasu ‘yan Nijeriyar da suka haɗa da sarakuna, ‘yan siyasa, ƙungiyoyin cikin gida da na waje tuhumar gwamnati kan aikinta na kare ‘yan ƙasa.
Sai dai gwamnatin ta bakin Ministan Yaɗa Labarai da Al’adu, Mohammed Idris, ta ce yaɗa labaran ayyukan ’yan ta’addan da ’yan jarida ke yi ne ke ƙara kawo barazana ga tsaron ƙasar.
Ministan ya bayyana hakan ne a hedikwatar rundunar soji da ke Abuja a yayin a wani taron masu ruwa da tsaki a harkokin kafafen yaɗa labarai.
Ministan wanda babban daraktan kafar Muryar Nijeriya, Jibril Ndace ya wakilta, ya ce gwamnatinsu na ƙoƙari wajen kawo ƙarshen matsalar tsaro, ta hanyar samar wa jami’an tsaro kayan aiki, horo, da tattara bayanan sirri.