Matar gwamna ta ɗauki nauyin ragon suna da hidimar duk matar da ta haifi ’yan uku a Sakkwato
Published: 18th, April 2025 GMT
Uwargidan Gwamnan Sakkwato Hajiya Fatima Ahmad Aliyu ta ɗauki nauyin ragon suna da abinci da kayan barka ga duk wata mata da tahaifi ’yan uku a jihar.
Hahiya Fatima ta sanar da haka ne a ranar Laraba nan a lokacin da ta yi takakkiya takanas zuwa garin Ƙaurar Yabo da ke Ƙaramar Hukumar Yabo domin kai ragunan suna da kayan barka da na suna ga wata mai jego mai suna Malama Bela’u, wadda ta haifi ’yan uku a garin.
Daga cikin kayan da ta kai wa mai jego kyauta, har da buhun abinci goma da akwatunan tufafi da tsabar kudi Naira dubu dari biyar.
A bayanin da mataimaka wa gwamna kan harkokin kafofin sada zumunta, Nasir Bazza, ya fitar, ya ce mutanen ƙauyen sun yi farin cikin ganin matar gwamna a garin, wanda shi ne karo na farko da suka ga matar gwamna a yankin nasu.
Ya ce matar gwamna ta yi alkawalin ci gaba da bayar da irin wannan tallafi ga duk wata mata da Allah ya albrkace ta da samun karuwar ’yan uku a lokaci guda a jihar.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Uku ragon suna matar gwamna
এছাড়াও পড়ুন:
ISWAP sun ruguza gadar Mandafuma babbar hanya a Borno
Wasu ’yan ta’addan da ake zargin suna da alaƙa da ISWAP sun tayar da wata na’ura mai fashewa a kan gadar Mandafuma da ke kan hanyar Biu zuwa Damboa da tsakar daren wayewar garin ranar Talata.
Kamar yadda majiyar Zagazola Makama ke cewar, wannan harin na bam da waɗannan ‘yan ta’addan suka jefa ya lalata gadar ta Mandafuna gaba ɗayanta.
Dangote: Har yanzu gidajen mai ba su rage farashin mai ba ’Yan bindiga sun sace makiyaya 5, da shanu 1,200 a KadunaA cewar majiyar, wannan lalacewar gadar a halin da ake ciki ya kai ga katsewar hanyar da ke tsakanin ƙauyen Mandafuma da garin Biu wadda ita ce hanyar da ta haɗa garin Biu da Maiduguri Jihar Borno.
Kamar yadda majiyar ke cewar, wannan aikin ta’addanci an yi shi ne da nufin daƙile zirga-zirgar ababen hawa a kan hanyar, tare da hana masu ababen hawa da fasinjoji walwala akan wannan hanyar mota.
Har ila yau, wannan ɓarna za ta taimaka wajen hana ƙarfafa ayyukan sojojin da ke kai kawo a cikin wannan yankin don gudanar da harkokin tsaro.