Leadership News Hausa:
2025-04-19@08:37:24 GMT

Bukatar Kawo Karshen Mamayar Da Kamaru Ke Yi Wa Yankunan Nijeriya

Published: 18th, April 2025 GMT

Bukatar Kawo Karshen Mamayar Da Kamaru Ke Yi Wa Yankunan Nijeriya

Akwai kuma Sanata Adeniyi Adegbonire dan jam’iyyar APC daga mazabar Ondo ta tsakiya, Sanata Seriake Dickson dan jami’yyar PDP, daga mazabar Bayelsa ta Gabas, Sanata Shehu Lawan Kaka, dan jam’iyyar APC, daga mazabar Borno ta tsakiya.

Sauran sun hada da; Sanata Banigo Ipaligo dan jam’iyyar PDP, daga mazabar Ribas ta Yamma, Sanata Jarigbe Jarigbe dan jami’yyar PDP, daga Koros Riba ta Arewa, Sanata Ekong Sampson dan jami’yyar PDP, daga mazabar Akwa Ibom ta Kudu, Sanata Sani Bello dan jami’yyarAPC, daga mazabar Neja ta Arewa sai kuma Sanata Aniekan Bassey, dan jam’iyyar PDP, daga mazabar Akwa Ibom.

Majalisar ta kafa wannan kwamtin ne, biyo bayan kudurin da Sanata Aniekan Bassey na mazabar Arewa da Gabas daga Akwa Ibom, ya gabatar mata wacce ta yi daidai da dokokin 41 da 51.

Bugu da kari, a cikin kudurin da Sanata Bassey ya gabatar wa da Majalisar Dattawan ya yi gargadi da cewa, kutsen na ‘yan ta’addar daga kasar Kamaru, zai iya shafar tattalin arzikin jihar ta Akwa Ibom

Sanatan ya shedawa Majalisar cewa, yankin na Efiat, da ke a karamar hukumar Mbo a Akwa Ibom, na daga cikin yankin da aka bai wa kasar Kamaru a shekarar 1913, biyo bayan yarjejeniyar Anglo-German ko kuma a hukuncin da yarjejeniyar Babban Kotun Koli ta Duniya Duniya ta yanke a watan Okutobar 2002.

A nan, muna jinjiawa Majalisar ta Dattawa bisa kafa wannan kwamtin mai mambi tara, musamman domin kwamitin ya gudanar da bincike, kan wannan batun, na zargin kutsen ‘yan ta’addar na kasar Kamaru,a wannan yankin.

Sai dai, a wannan lokacin, yana da kyau a ci gaba da tsimayin sakamakon binciken da kuma shawarwarin da kwamtitin zai gabatar wa da Majalisar ta Dattawa kan wannan batun, domin sanin mataki na gaba da za a dauka.

Batu na maganar rikicin kasa, akasari, yana da wuyar lamari, wajen warware wa, musamman duba da cewa, Nijeriya da kasar Kamaru, kasashe ne, da suka gaji iyakoin kasa daga turawan mulkin mallaka, wadanda kuma, tun a baya, ba a fayyace yadda suke ba.

Bugu da kari, wannan lamari ne, mai matukar mahimmanci da ya shafi kasar nan.

Kazalika, ya zama waji, ‘yan Nijeriya su hada kansu, domin kare iyakokin kasar ga dukkan wata barazana, da za ta iya shafar kasar.

Sai dai, damuwar da akasarin ‘yan Nijeriya ke ci gaba da nunawa kan batun shi ne, na rashin mayar da hankali a siyasance, domin lalubo da mafita kan lamari irin wannan.

Mu a nan, muna kira ga Gwamnatin Tarayya da ta kasance mai sanya ido sosai da kuma daukar kwararan matakai da za su kasance ba su kai ga zubar da kimar Nijeriya a idon duniya ba, wajen kare yiwa tattalin arzikin kasar nan.

Hakazalika, ya zama wajbi, Nijeriya ta tashi tsaye, wajen kare kasar daga dukkan wani na’ui na barazana daga kere domin kare kasar nan.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Kamaru Mamaya Nijeriya dan jam iyyar daga mazabar kasar Kamaru

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnatin ‘Yan Sahayoniyya Ta Sake Aiwatar Da Kisan Kiyashi A Sansanin Falasdinawa Na Jabaliya

Sojojin mamayar Isra’ila sun sake aiwatar da wani sabon kisan kiyashi kan Falasdinawa 5 a sansanin Jabaliya da ke arewacin Gaza

Fararen hula 5 da suka hada da yara biyu da mace daya ne suka yi shahada, wasu kuma suka bace sakamakon harin da rundunar sojin mamayar Isra’ila suka kai kan wani gida a sansanin ‘yan gudun hijira na Tal al-Za’atar da ke gabashin Jabaliya da ke arewacin Zirin Gaza.

A cewar majiyoyin yankin, gidan da aka kai harin na dangin Nasiyo ne, kuma yana dauke da ‘yan gudun hijira daga iyalai sama da biyar a cikinsa, inda harin ya turbude su a karkashin baraguzan gine-gine.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Shugaban Majalisar Neja Ya Mika Sakon Easter Ga Al’ummar Kirista.
  • Dokar-ta-baci: Shugaban Majalisar Wakilai Ya Gargadi Kantoman Ribas
  • Gwamnatin ‘Yan Sahayoniyya Ta Sake Aiwatar Da Kisan Kiyashi A Sansanin Falasdinawa Na Jabaliya
  • Majalisar Kasa Ta Rasha Ta Amince Da Yarjeniyar Dangantaka Ta Musamman Tsakanin Iran Da Kasar
  • Majalisar Dokokin Zamfara Ta Dawo da Dan Majalisa Basko da Aka Dakatar
  • MDD Ta Nuna Damuwarta Akan Kokarin Sake Raba Kasar Sudan Gida Biyu
  • Hamas ta bukaci hadin kan duniya domin kawo karshen kisan kiyashin da Isra’ila ke yi a Gaza
  • An naɗa mace ta farko mai magana da yawun rundunar sojin Nijeriya
  • Yadiot Ahranot: Amurka Ta Bayyana Lokacin Ficewarta Daga Syria