Hakazalika, kamfanoni 43 da aka bayyana sun ba da shawarar raba jimillar Naira tiriliyan 1.678 ga masu hannun jarinsu, tare da yaba wa abokan huldarsu.

A cikin 2024, bangarori na kasuwancin Nijeriya ya gamu da kalubale masu yawa na tattalin arziki da samar da ababen more rayuwa wadanda suka yi matukar tasiri ga ayyukansa.

Masana’antun sun fuskanci matsin lamba daga hauhawar farashin kayayyaki, faduwar darajar Naira, hauhawar kudin ruwa, karin kudin wutar lantarki, karancin tallace-tallace, yawan haraji da kuma tabarbarewar tsaro.

A cikin wannan babbana al’amari, kamfanoni a manyan sassan tattalin arziki sun ba da rahoton sakamako mai karfi na kamfanoni da kuma bayar da lada ga masu hannun jari.

Idan za a kimanta halin da ake ciki, babban jami’in gudanarwa (Shugaba) na HighCap Securities Limited, Mista Dabid Adonri, ya ce, “Ta hanyar samar da, bankunan sun sami kansu a karshen ayyuka na wasu manufofi, wanda ta haka ne suka fahimci faduwar canjin kasashen da ba a taba gani ba da kuma makudan kudaden shiga daga zuba jari a basussukan jama’a.

“Abin takaici shi ne, sauye-sauyen kasuwanni da matakan tsare-tsare na kudi wadanda ke samar da karuwar kudaden shiga na bankuna sun sanya yawancin masana’antun da suka dogara da shigo da kayayyaki zuwa cikin gida asara, wadanda babu shakka sun yi nasasar shawo kan lamarin, kamar masu samar da siminti, suna da kasuwancinsu na fitar da kayayyaki domin samun daidaito.”

Ya yi nuni da cewa, duk da rauni na kasuwancin kayan masarufi sakamakon hauhawar farashin kayayyaki, bangaren gwamnati na ci gaba da aiwatar da manyan ayyuka, wadanda ke cinye kayayyakin gini da dama. Don haka ne ribar da kamfanoni kamar Dangote Cement da BUA Cement suka bayyana.

“To kuwa tun da aka riga aka bayyana wadannan kamfanoni a bainar jama’a da kuma yadda tsarinsu yake, babu wani dalili da zai musanta ribar da suke samu a ce ba gaskiya ba ce.

Adonri ya ce “Yawancin kamfanoni na Nijeriya suna yin fatali da ci gaban tattalin arzikin kasar da ke tabarbarewa, suna ba da rahoton riba da kuma yawan kudaden da aka samu,” in ji Adonri.

Babban jami’in gudanarwa na InbestData Consulting Limited Ambrose Omordion, ya aminta da cewa “bankuna da sauran kamfanonin Nijeriya suna bayar da rahoton riba mai yawa da kuma kudaden da ake samu duk da tabarbarewar tattalin arzikin kasar da kuma karancin sayayyar kayayyaki.”

Ya lura cewa manyan kamfanoni, musamman a bangaren banki, na iya za su iya tsira daga manyan kalubalen tattalin arzikin da kananan ‘yan kasuwa da daidaikun mutane ke fuskanta.

Ya kara da cewa ” Alal misali, bankuna, na iya samun manyan kudaden shiga daga wasu kwamitoci ko ayyukan sanya hannun jari wadanda ba su da alaka da ainihin kasuwancin ba da lamuni,” in ji shi.

A halin da ake ciki, shugaban Kungiyar Masu Hannun Jari Mai Zaman Kanta ta Nijeriya (ISAN), Moses Igbrude, ya yi nuni da cewa, “Rabon da bankunan ke bayyanawa gaskiya ne, domin harkokin kasuwancinsu na bayar da hidima ne, wanda ke samar da jari don ciyar da tattalin arzikin kasa gaba.

“Ba tare da manyan kudaden da za a inganta tattalin arzikin kasa ba, to ba za a taba samar da wasu dabaru na farfado da shi ba. Tare da kowane ciniki, akwai farashi da ya shafi sakonnin rubutu zuwa riba akan lamuni da aka ba wa abokan ciniki, kuma hakan na ba da ayyuka da yawa ga abokan cinikinsu a duk fadin kasar,” in ji shi.

A halin yanzu dai, shugaban kungiyar masu Masana’antu ta Nijeriya (MAN), Otunba Francis Meshioye ya yi kira da a tallafa wa bangaren masana’antu.

Ya ce, “ A 2025, fannin masana’antu ya ta’allaka ne ga nasarar sauye-sauyen tattalin arziki da ake ci gaba da samu, wadanda suka hada da aiwatar da sauye-sauyen harajin da ake shirin yi, da daidaita muhimman alamomin tattalin arziki, da zuba hannun jari a fannonin ababen more rayuwa da fasaha.

“La’akari da jerin sauye-sauye na kasafin kudi na gwamnatin yanzu, ana sa ran samun saukin tabarbarewar tattalin arzikin da samun wasu ci gaba a wannan shekara tare da kwanciyar hankali a cikin tsarin musayar kudi a 2025.”

Meshioye ya kara da cewa, domin fannin ya dawo da karfinsa, dole ne a ci gaba da kokarin inganta ayyukan da ake yi da kuma kara yin gasa, domin hakan na da matukar muhimmanci wajen taimaka wa masana’antun Nijeriya su shawo kan kalubalen da suke fuskanta.

Meshioye ya ce, “Masana’antu na da muhimmanci wajen bunkasa da kuma dorewar ci gaban tattalin arzikin Nijeriya. Muna neman gwamnati ta daidaita tare da amincewarmu cewa samun nasarar masana’antu kai tsaye nasara ce ga tattalin arziki, da bin hanyar fadadawa, rayuwa mai kyau ga ‘yan kasa.”

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Haraji Matsin Rayuwa tattalin arzikin tattalin arziki hannun jari

এছাড়াও পড়ুন:

Kasar Sin Ta Mallaki Tasoshin Fasahar 5G Miliyan 4.4 A Halin Yanzu

Kazalika, Injiniya Xie ya kara da cewa, a cikin rubu’in farko na bana, sashen masana’antu na kasar Sin ya taka rawar gani wajen samun ci gaba ba tare da tangarda ba sakamakon ingantuwar tsari da zurfafa ayyuka wajen samar da sabbin ginshikan bunkasa ci gaba mai inganci. (Abdulrazaq Yahuza Jere).

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • China Na Neman Ƙasashe Su  Haɗe Wa Amurka Kai Sakamakon Ƙarin Haraji
  • Dalilan Da Suke Sa Masu Kiwon Kajin Gidan Gona Ci Gaba Da Tafka Asara A Halin Yanzu
  • Kasar Sin Ta Mallaki Tasoshin Fasahar 5G Miliyan 4.4 A Halin Yanzu
  • Ta Ya Ake Gudanar Da Nagartacciyar Rayuwa?
  • Wakilin Sin Ya Yi Kira Da A Yi Aiki Tare Don Daidaita Mummunan Yanayi A Yankin Manyan Tabkuna Na Afirka
  • Alkaluman Tattalin Arzikin Sin Sun Shaida Dorewar Ingancin Tattalin Arzikinta
  • Cibiyar Nazarin Jinsi (CGS) Da Jami’ar Bayero Kano Za Su Yi Aiki Tare
  • Mizanin Hada-hadar Tattalin Arzikin Kasar Sin Ya Karu Da Kashi 5.4% A Rubu’in Farko Na Bana
  • Gwamnonin Nijeriya Sun Nuna Damuwarsu Kan Kashe-kashen Mutane A Filato