Radio Nigeria Kaduna Hausa:
2025-04-19@09:15:38 GMT

BUK Ta Shirya Taron Na Shekara-shekara Akan Malam Aminu Kano

Published: 18th, April 2025 GMT

BUK Ta Shirya Taron Na Shekara-shekara Akan Malam Aminu Kano

Cibiyar Nazarin Dimokuradiyya ta Aminu Kano a Jami’ar Bayero Kano (BUK) ta shirya taron shekara-shekara karo na 23 don tunawa da cika shekaru 42 da rasuwar Malam Aminu Kano.

 

 

A nasa jawabin, Shugaban jami’ar Bayero, Farfesa Sagir Adamu Abbas, ya jaddada muhimmancin taron shekara-shekara wajen kiyaye manufofin da Malam Aminu Kano ya tsaya a kai.

 

Farfesa Haruna Musa wanda mataimakin shugaban jami’ar kula da harkokin ilimi ya wakilta, ya bayyana cewa jerin laccoci an yi niyya ne don ba da damar fahimtar juna dangane da yanayin tarihi.

 

“A ci gaba da kokarin da jami’ar mu ke yi na karfafa al’adun dimokuradiyyar Najeriya, muna gayyatar manyan mutane duk shekara don gabatar da laccoci a gidan Mambayya kan batutuwan da suka shafi kasa baki daya.

 

Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabiru Yusuf, ya bayyana Malam Aminu Kano a matsayin wani hamshakin mai neman sauyi na Afirka, kuma dan gwagwarmayar siyasa mai jajircewa, wanda rayuwarsa ke ci gaba da zaburar da al’umma.

 

 

Wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo, ya jaddada cewa taken taron ya dace saboda halin da kasar nan ke ciki.

 

A nasa jawabin, Farfesa Kabiru Isa Dandago ya gabatar da kasida mai taken “Siyasar Gyaran Haraji a Najeriya: Tsammani da Gaskiya.

 

Gidan rediyon Najeriya ya ruwaito cewa taron tunawa da marigayin ya hada masana, masana siyasa, da shugabannin kungiyoyin farar hula, inda suka yi bita a kan rayuwar marigayi dan kishin kasa, malami, dan juyin juya hali.

 

KHADIJAH ALIYU

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

GORON JUMA’A

Ina gaida Ummi da Baba sai ‘yan uwana yaya Zahra, Yaya Aminu, Yaya Hadiza, Yaya Maimuna, Yaya Rashida, Iman, Amir Da Nurain, sannan kawayena Badi’a Kabir Kwallo, Jamila Sa’ad, Zainab Garba Goro, Yahanasu Imam, Saddika Junaid, Hauwa Uwaisu, da fatan sun yi Juma’a lafiya.

Sako Daga Fatima Zahra Jihar Kano:

Ina gaida Mamana da Abbana da kawaina kamar Rafi’a Kamal, Walida Sadik, Maryam Aliyu, Amina Idris, Khadija Baba, A’isha Fahat, Kursiyya Hamisu, Fiddausi da dai sauransu.

Sako Daga Wasila Adam Nuhu Jihar Kaduna:

Ina gaida Anti A’isha, Anti Ladidi, Anti Balaraba, Uncle Zubair, Uncle Jafar, Uncle Kamalu, Uncle Tajuddeen, Anti Kubra, Anti Sadiya, Uncle Yakub, sai kawayena kamar su; Shaheedah, Yasmin, Zeenat, Meenah, Mahmah, Hanan, Afnan, Fauzy, Ruky, Rumaisa.

Sako Daga Maryam Murtala, Jihar Kano:

Ina gaida Mamy, Maryam Abdullahi, ina gaida kawayena kamar, Khurthum Nasir, Zainab A. Mudi, Halima Saleh, Fatima Kabir Kanwa, Asma’u Muhammad Bello, Muhammad Abdullahi Aminu Mudi, Anwar, Baby Maryam, Anti Fauziyya, Bulun-bulun, Anti Sidiya, Ameerah, Amina, Esha, Anti Safiyya, Mama, Khairiyya, Uncle Hassan, Ibrahim, Uncle Aminu da fatan za su yi juma’a lafiya.

Sako Daga Maryam’s Bakery:

Ina gaida Mum da Dad nawa sannan ina gaida Sisters da brothers dina sai students dina irin su; Deejah, Meerah, Yusra, Nahnah, Zee, Fati, Husna, Priciliar, Kueen Billy, Zainab (first lady), princess Mahmah, Glory, Faith, Maryam Sha’aban, da dai sauran su.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Makarantar Bare: Shekara 20 dalibai na karatu a matsanancin yanayi
  • An tsinci gawar mabaraci mai shekara 75 a Neja
  • Minista Ya Sake Jaddada Ƙudirin Sabunta Kayan Aikin Watsa Labarai Na Gwamnati
  • PDP ba ta shirya yin zaɓen 2027 ba – Wike
  • APC Ta Gaza Gudanar Da Taron NEC Cikin Shekaru Biyu – PDP Ta Zarge Su
  • Gwamnatin Trayya Zata Zamantar da Kayayyakin Watsa Labaran ta
  • GORON JUMA’A
  • Cibiyar Nazarin Jinsi (CGS) Da Jami’ar Bayero Kano Za Su Yi Aiki Tare
  • Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar Da Taron Ƙarawa Ma’aikatan Jinƙai Sani A Jihar Kano