Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Ce: Za A Gudanar Da Zagaye Na Biyu Na Tattaunawar Iran Da Amurka A Birnin Roma Ne
Published: 18th, April 2025 GMT
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Za a gudanar da zagaye na biyu na tattaunawar ba na kai tsaye ba da Amurka a birnin Roma a ranar Asabar
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya sanar da cewa zai tafi birnin Roma a ranar Asabar domin halartar zagaye na biyu na shawarwari ba na kai tsaye ba da Amurka, yana mai jaddada cewa sakon da Jagoran juyin juya halin Musulunci ya aikewa shugaban kasar Rasha ya kunshi muhimman batutuwa.
A cewar kamfanin dillancin labaran IRNA, Araghchi ya ce: Roma ba ita ce mai masaukin baki ba, a’a, a maimakon haka, wajen da za a yi shawarwarin, gwamnatin Oman ce ta kasance mai daukar nauyin shawarwarin ba na kai tsaye ba tsakanin Iran da Amurka, kuma Iran za ta kasance a wurin da mai masaukin bakin ya kayyade, aikin shiga tsakani da kulla huldar da ba na kai tsaye ba, shi ne alhakin gwamnatin masarautar Oman.”
Ya kara da cewa, “Zai tafi Roma ranar Asabar kuma za a fara zagaye na biyu na tattaunawar ba na kai tsaye ba tsakanin Iran da Amurka.
Arakchi ya ce: Rasha da sauran kasashe sun bayyana aniyarsu ta taimaka wajen ciyar da shawarwarin gaba.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: ba na kai tsaye ba
এছাড়াও পড়ুন:
Nijar da Najeriya sun sha alwashin inganta dangantaka a tsakaninsu
Kasashen Nijar da Najeriya sun sha alwashin inganta dangantaka a tsakaninsu domin cin moriyar juna a matsayinsu na makobta.
Wannan bayyanin ya fito bayan tattaunawa data wakana tsakanin ministocin harkokin wajen kasashen biyu a birnin Yamai bayan kwashe watanni ana takaddama.
Yayin ziyarar da ministan harkokin wajen Najeriya ya kai Nijar an gudanar da wani babban taro tsakanin shugabannin diflomasiyyar kasashen biyu don sake farfado da hanyoyin hadin gwiwa a bangarori da dama da suka hada da tattalin arziki da tsaro.
Ministan harkokin waje da hadin gwiwa na Nijar Bakary Yaou Sangaré da takwaransa na Najeriya Yusuf Maitama Tuggar sun gana a ranar 16 ga ga watan nan, lamarin dake nuni da wani gagarumin sauyi na dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu da ta yi tsami tsawon watanni biyo bayan juyin mulkin da ya faru a ranar 26 ga watan Yulin 2023.
bangarorin biyu sun kuma tattauna kan barazanar ta’addanci a kan iyakokinsu, inda suka jaddada aniyarsu ta hada karfi da karfe wajen yakar kungiyoyin da ke dauke da makamai da ke kawo cikas wajen aiwatar da dukkanin shirye-shiryen ci gaba a kasashen biyu cikin shekaru da dama. Inda suka bukaci ma’aikatun tsaron kasashen biyu da su ci gaba da hadin gwiwa a fannin tsaro.
Dangantaka tsakanin kasashen biyu da ke makwabtaka da juna ta tabarbare ne a lokacin da Najeriya ta taka muhimmiyar rawa wajen daukar matakan kakabawa Yamai takunkumin da kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ta ECOWAS ta kakabawa kasar, wanda hakan ya bata dangantakar da ke tsakaninsu.