Aminiya:
2025-04-19@11:29:18 GMT

An kashe sojoji, fararen hula da dama a Borno

Published: 18th, April 2025 GMT

Wasu ’yan ta’adda da ake kyautata zaton ’yan Boko Haram ne sun kai hari a sabuwar unguwar Yamtake da ke Ƙaramar hukumar Gwoza a Jihar Borno, inda suka kashe sojoji biyu tare da wasu fararen hula da ba a bayyana adadinsu ba.

Majiyoyin tsaro da na cikin gida sun tabbatar da harin, inda suka ce maharan sun mamaye unguwannin ne da misalin ƙarfe 11:15 na daren Alhamis.

Gwamnatin Yobe ta sayo hatsi don tunkarar kakar bana Matan da suka tsira daga Boko Haram na buƙatar tallafin musamman

Ɗaya daga cikin majiyar sojojin ta ce, kafin a aike da wata tawagar sojoji daga Gwoza, maharan sun riga sun afkawa jama’a  da sansanin sojan Yamtake.

“Muna jiran tawagar masu ƙarfafa musu su dawo, amma mun sami labarin cewa mutane biyu daga cikin jami’anmu da wasu fararen hula harin ya shafe su. Ina ba da shawarar mu jira har sai sun dawo,” in ji shi.

Sai dai Sanata Ali Ndume, ya ce tun lokacin da lamarin ya faru yana tuntuɓar al’ummar unguwar Yamtake.

“Abin takaici ne cewa mutanenmu a ƙauyen Yamtake sun fuskanci mummunan harin Boko Haram a daren ranar Alhamis, ɗaya ne daga cikin unguwannin da suka karɓi ’yan gudun hijirar kwanan nan, gwamnatin Jihar Borno ta sake tsugunar da su.

“Abin baƙin ciki ne yadda sojoji biyu suka rasa ransu a bakin aiki, yayin da wasu fararen hula da ba a san ko su wanene ba na daga cikin waɗanda suka jikkata, Allah Ya gafarta musu.

“Amma kuma na yabawa Birgediya Janar Nasir Abdullahi, Birgediya Kwamanda na runduna ta 26 Task Force da jiga-jigan sojojinsa kan sadaukarwar da suka yi ba tare da ƙaƙƙautawa ba wajen daƙile hare-hare da dama, musamman waɗanda aka yi yunƙurin kaiwa farmakin a garin Gwoza.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Boko Haram Yamtake fararen hula

এছাড়াও পড়ুন:

Sojojin Haramtacciyar Kasar Isra’ila Sun Kona Yara Da Mata A Harin Da Suka Kai Khum Yunis Na Gaza

Hare-haren sojojin mamayar Isra’ila sun kona kananan yara a garin Khun-Yunis da ke kudancin Zirin Gaza

Hukumar tsaron fararen hula a Zirin Gaza ta fitar da wani faifan bidiyo a yau alhamis, inda ta ke nuna irin mummunan halin da ‘yan gudun hijiran Falasdinawa suka shiga a Khan Yunis, bayan da jiragen saman yakin gwamnatin haramtaciyar kasar Isra’ila suka yi luguden bama-bamai a kan tantunan ‘yan gudun hijiran Falasdinawa da suka rasa matsugunansu,

Tun da tsakar daren jiya ne jiragen suka fara luguden wutan kan tantunan ‘yan gudun hijiran zuwa wayewar garin yau Alhamis, inda wutar bama-baman suka kone gawarwakin yara da mata, bayan shahadan mutane da dama.

Rahotonni sun bayyana cewa: An hae-haren sun janyo shahadan yara da mata tare da kona gawarwakinsu sakamakon yin luguden makamai masu linzami kan sansanoninsu musamman wadanda suke rayuwa a cikin tantuna a yankin al-Mawasi da ke yammacin Khan Yunis.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • ’Yan sanda sun ceto ɗalibai 10 sun kashe ɗan bindiga a Edo
  • ’Yan sanda sun ceto ɗalibai 10 sun lashe ɗan bindiga a Edo
  • Yawan Mutanen Da Suka Yi Shahada A Harin Amurka Na Jiya A Yemen Ya Kai 74
  • Boko Haram Sun Kashe Sojoji 2 Da Wasu A Wani Sabon Hari A Borno
  • Amurka Ta Kashe Mutane 38 Tare Da Jikkata Fiye Da 100 A Harin Da Ta Kai Lardin Al-Hudaidah Na Yemen
  • Sojoji Sun Kashe ‘Yan Ta’adda a Sambisa da Kudancin Tumbun
  • Matan da suka tsira daga Boko Haram na buƙatar tallafin musamman
  • Sojojin Haramtacciyar Kasar Isra’ila Sun Kona Yara Da Mata A Harin Da Suka Kai Khum Yunis Na Gaza
  • Bai Wa Shanu Guba: Sojoji Sun Shiga Tsakani Domin Dakile Yunkurin Ramuwar Gayya A Filato