PDP ba ta shirya yin zaɓen 2027 ba – Wike
Published: 18th, April 2025 GMT
Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya ce babbar jam’iyyar adawa ta PDP ba ta da wani kyakkyawan tsari da za ta iya kayar da jam’iyyar APC mai mulki a zaɓen 2027.
Ministan ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai kai tsaye a Abuja ranar Juma’a.
Benuwe: Har yanzu ba a gano wasu mutanen ƙauyuka ba – Gwamna Alia An kashe sojoji, fararen hula da dama a BornoDaily Trust ta ruwaito cewa, shugabannin adawa a faɗin ƙasar nan na ƙara zage damtse wajen ganin sun ƙulla alaƙa da nufin kawar da Jam’iyyar APC.
Sai dai kuma, mabambantan buƙatu tsakanin manyan masu ruwa da tsaki na ci gaba da kawo cikas ga ci gaban tattaunawar ƙawancen da suke yi.
Da yake bayani a yayin taron manema labarai, Wike ya ce: “PDP ba ta shirya zaɓen 2027 ba, a bayyane yake, misali ina da jarrabawa kuma zan je aji don karatu, shin ina yin karatun? Ina fahimtar karatun? Ba ka buƙatar ka yaudari wani da cewa kana karatu. Kana ƙoƙarin zuwa karatun ne kawai don mutane su ga cewa ka ɗauki jakarka zuwa aji.
“Halin da PDP ke ciki ke nan, don haka ba za su iya cewa tabbas sun shirya wa zaɓen 2027 ba, gwagwarmayar neman mulki ba za ta iya taimakawa jam’iyyar ba.”
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Babban Birnin Tarayya FCT Nigeriya zaɓen 2027
এছাড়াও পড়ুন:
Hukumar Alhazai ta Jigawa Ta Shirya Bitar Ga Malaman Bita na Kananan Hukumomi 27
A kokarin ta na ci gaba da inganta ayyukan ta, hukumar jin dadin alhazai ta jihar Jigawa ta gudanar da bitar sanin makamar aiki ga malaman bita na kananan hukumomin jihar 27.
Darakta Janar na hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo wanda ya jagoranci gudanar ta taron a shelkwatar hukumar dake Dutse, ya ce an shirya taron ne domin nusar da malaman ayyukan daya rataya a kawunan su domin cimma burin da aka sanya a gaba.
A cewar sa, hukumar zata sanya malaman bitar a cikin kwamitocin hukumar daban-daban domin samun nasarar gudanar da aikin hajjin bana.
Yana mai cewar, a matsayin su na jagororin maniyata aikin hajji, akwai bukatar su kasance da maniyata tare da fadakar dasu akan aikin hajjin da zasu gudanar a kasa mai tsarki.
Alhaji Ahmed Umar Labbo
Alhaji Ahmed Umar Labbo, yace tuni hukumar ta karbi fasfo na maniyata kuma sun shigar dasu cikin runbun yin biza.
Kazalika, Labbo yayi nuni da cewar, wannan shine karon farko da gwamnatin jihar ta dauki nauyin malaman bita zuwa aikin hajjin bana domin hidimtawa maniyatan aikin hajjin bana.
A nasa tsokacin, Daraktan fadakarwa da wayar da kai na hukumar, Alhaji Abdullahi Aliyu, yayi jawabi ga malaman bitar kan nauyin da ya rataya a kawunan su.
Yana mai kira a gare su dasu sadaukar kai domin taimakawa maniyyata a kowanne fannin da hukumar ta umarce su domin kwalliya ta biya kudin sabulu.
Wasu daga cikin malaman bitar da suka zanta da Radio Nigeria,sun yabawa Gwamna Umar Namadi da shugaban hukumar alhazai ta jihar, Alhaji Ahmed Umar Labbo bisa amincewa da daukar nauyin su domin jagorantar maniyatan aikin hajjin wannan shekarar.
Usman Mohammed Zaria