HausaTv:
2025-04-19@12:22:16 GMT

Amurka Na Shirin Rufe Ofisoshin Jakadancinta Kimani 30 A Duniya

Published: 18th, April 2025 GMT

Gwamnatin kasar Amurka ta bada sanarwan cewa zata rufe wasu daga cikin ofisoshin jakadancinta har kimani 30 a kasashen duniya, amma mafi yawansu a kasashen Afirka.

Shafin yanar gizo na labarai Afrika News ya nakalto ma’aikatar harkokin wajen kasar Amurkan na fadar cewa gwamnatin shugaban Trump tana son ta rage yawan kashe kudade a ma’aikatar don amfani da su a cikin gida.

Labarin ya kara da cewa gwamnatin tana son rage kudaden da ma’aikatar take kashewa a kan ofisoshin jakadunsu da kasha 50% da kuma rage tallafin da take bawa wasu kungiyoyi a wadan nan kasashe har da kasha 75%.

Labarin ya kara da cewa kasashen da shirin ya shafa dai akwai  Lesotho, Eritrea, Afrika ta tsakiya, Congo Brazavile, Gambia, Sudan ta kudu,. Banda wadannan za’a rufe kananan ofisoshin jakadanci da ke birnin Durban na Afrika ta kudu, da kuma na Douala, da ke kasar Cameroon. Labarin yace ayyukan wadannan ofisoshin jakadanci zasu kuma ga kasashe makobta.

A kasahen turai da Asiya kuma Amurka zata rufe ofisoshin jakadancinta a tsibirin Malta, Luxembourg, da kuma wasu kananan ofisoshin jakadancin kasar a tarayyar Turai da Asiya.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Iran Da Amurka Za Su Ci Gaba Da Tattaunawa Kan Shirin Nukiliyar Tehran

Iran da Amurka za su shiga zagaye na biyu na tattauna batun taƙaita shirin nukiliyar Tehran a yau Asabar.

Masu shiga tsakani za su haɗu a birnin Roma bayan zagayen farko na tattaunawar da aka yi a makon jiya a Oman.

Ministan harkokin wajen Iran ya ce za a iya cimma yarjejeniya idan Amurka ba ta gabatar da wasu sharuɗa da Tehran ba za ta yi bi ba.

Shugaba Trump ya sha yin barazanar yin amfani da ƙarfin soji idan Iran ta ƙi amincewa da wata yarjejeniya.

Ana ta samun bayanan da suka ci karo da juna game da abubuwan da Washington za ta gabatar da yarjejeniyar.

Tehran ta yi bayani ƙarara cewa ba za ta taɓa yadda da batun rushe shirinta na nukiliya baki ɗaya ba.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Mene Ne Shirin Nukiliya Na Iran Kuma Me Amurka Ke So Ta Yi?
  • Iran Da Amurka Za Su Ci Gaba Da Tattaunawa Kan Shirin Nukiliyar Tehran
  • Iran da Amurka na shirin tattaunawa ta biyu a birnin Rome
  • Amurka ta sanar da cewa za ta rage yawan sojojinta a Syria da rabi
  • Kasar Sin Ta Nemi Kasashen Duniya Su Taimaka Wa Libya Wajen Fita Daga Kangin Da Take Ciki
  • Batawa Sin Suna Ba Zai Taimaka Kawar Da Tambarin Amurka A Matsayin Daular Kutsen Intanet Ba
  • Araghchi: babu tattaunawa kan batun tace sinadarin uranium
  • Rasha ta ce tana bibiyar tattaunawar Iran da Amurka matuka
  • An Watsa Shirin Bidiyon “Bayanan Magabata Masu Jan Hankalin Xi Jinping” A Kasar Malaysia