HausaTv:
2025-04-19@12:04:02 GMT

Yawan Mutanen Da Suka Yi Shahada A Harin Amurka Na Jiya A Yemen Ya Kai 74

Published: 18th, April 2025 GMT

Hare-haren da jiragen yakin Amurka suka kaiwa lardin Hudaida ya karu zuwa 74.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar gwamnmatin kasar ta Yemen na fadar haka a yau Jumma’a ta kuma kara da cewa dukkan mutanen da suka mutu a hare-haren jiragen yakin Amurka a cibiyar man fetur na Ras Isa a birnin Hudaida fararen hula ne.

babu wani mayakin kungiyar Ansarulla ko guda a cikinsu.

Labarin ya kara da cewa jiragen yakin Amurka wadanda suka taso daga jiragen ruwa masu daukar jiragen sama na Amurka masu suna USS Harru Truman da kuma USS Carl a tekun red sea, sau kai hare kan ras Isa ne har sau biyu, hare na biyun ya fada ne kan ma’aikatan ceto da kuma yan kwana –kwana masu masu kashe wuta da cetun wadanda aka kaiwa hari na farko.

Majiyar Amurka ta bayyana cewa kayakin man fetur da ta kaiwa hari hukumar UNICEF ta MDD ce ta gina don haka kasar Yemen ba zata iya maida suba. Sannan kungiyar Ansarullah na samun kudaden tafiyar da kasar Yemen da su.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnatin ‘Yan Sahayoniyya Ta Sake Aiwatar Da Kisan Kiyashi A Sansanin Falasdinawa Na Jabaliya

Sojojin mamayar Isra’ila sun sake aiwatar da wani sabon kisan kiyashi kan Falasdinawa 5 a sansanin Jabaliya da ke arewacin Gaza

Fararen hula 5 da suka hada da yara biyu da mace daya ne suka yi shahada, wasu kuma suka bace sakamakon harin da rundunar sojin mamayar Isra’ila suka kai kan wani gida a sansanin ‘yan gudun hijira na Tal al-Za’atar da ke gabashin Jabaliya da ke arewacin Zirin Gaza.

A cewar majiyoyin yankin, gidan da aka kai harin na dangin Nasiyo ne, kuma yana dauke da ‘yan gudun hijira daga iyalai sama da biyar a cikinsa, inda harin ya turbude su a karkashin baraguzan gine-gine.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Amurka Ta Kaddamar Da Sabbin Hare-Hare Kan Garuruwan Sana’a, Sa’adah Da Al-Jawf Na Kasar Yemen
  • Iran ta yi tir da kakkausar murya da harin Amurka kan tashar mai ta Yemen
  • Amurka ta sanar da cewa za ta rage yawan sojojinta a Syria da rabi
  • Sojojin Kasar Yemen Sun Kai Hare Hare Kan HKI Da Jiragen Yakin Amurka
  • Amurka Ta Kashe Mutane 38 Tare Da Jikkata Fiye Da 100 A Harin Da Ta Kai Lardin Al-Hudaidah Na Yemen
  • Gwamnatin ‘Yan Sahayoniyya Ta Sake Aiwatar Da Kisan Kiyashi A Sansanin Falasdinawa Na Jabaliya
  • Yawan Kudaden Da Al’ummun Sin Suka Kashe Kan Kayayyakin Masarufi Ya Kai Yuan Triliyan 12.5 A Rubu’in Farko
  • Sojojin Haramtacciyar Kasar Isra’ila Sun Kona Yara Da Mata A Harin Da Suka Kai Khum Yunis Na Gaza
  • Iraki Ce Zata Amfana Da Tattaunawa Tsakanin Iran Da Amurka: Inji Sayyed Ammar Hakim