HausaTv:
2025-04-19@12:09:50 GMT

Iran Tace Yarjeniya Da Amurka Mai Yuwa Ne Idan Da Gaske Take

Published: 18th, April 2025 GMT

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa Iran zata halarci zaman tattaunawa da kasar Amurka kan shirin kasar na makamashin Nukliya tare da fatan bangaren Amurla ma tana bukatar cimma yarjeniya da ita, matukar Amurka bata kawo wani abu wand aba zai yu Iran ta amince ba.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan yana fadar haka a yau Jumma’a a birnin Mosco a lokacinda shi da tokwaransa na kasar Rasha Sergei Lavrov suke amsa tambayoyin yan jarida.

Ministan ya kara da cewa tawagarsa zata je taron birnin Roma tare da fatan tattaunawar zata yi kyau.

Ya kuma kara da cewa takunkuman tattalin arziki mafi muni wanda Amurka ta dorawa kasar da kuma yin kalamai biyu dangane da tattaunawa da kuma barazana da take wa JMI ba alamu ne na kekyawar niyyar Amurka  ba, amma zamu ci gaba da tattaunawar don ganin inda za’a itsaya.

A ranar Asabar 12 ga watan da Afrilun da muke ciki ne aka gudanar da tattaunawa tsakanin Iran da Amurka zagaye na farko a birnin Mascat na kasar Omman.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Jagora: Iran a shirye take domin aiki kafada da kafada tare da  Saudiyya

Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya jaddada cewa, Iran a shirye take yin aiki tare da Saudiyya a dukkanin bangarori, domin cin gajiyar al’ummomin kasashen biyu da ma duniyar musulmi, tare da yin ishara da cewa, dukkanin ci gaban da Iran ta samu a dukkanin bangarori na ilimin kimiyya da fasaha, a shirye take ta taimaka ma  Saudiyya a wadannan bangarori.

Wannan na zuwa ne a lokacin da Ministan tsaro Yarima Khalid bin Salman dan uwa ga Yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman ya gana da Ayatollah Khamenei a Tehran da yammacin jiya Alhamis don mika sakon Sarki Salman na Saudiyya.

Jagoran ya ce: “Mun yi imanin cewa dangantakar da ke tsakanin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da Saudiyya za ta kasance mai amfani ga kasashen biyu, kuma kasashen biyu za su iya kara kaimi domin karfafa juna.”

Ya kara da cewa “Yana da kyau ‘yan’uwa a yankin su hada kai da taimakon juna fiye da dogaro da wasu.”

Ayatullah Khamenei ya jaddada cewa fadada alaka tsakanin kasashen biyu ba abu ne da makiya za su yi farin ciki da shi ba, amma ya zama wajibi a yi hakan domin amfanin al’ummomin kasashen yakin da kuma al’ummar musulmi.

Ministan tsaron Saudiyya ya bayyana matukar jin dadinsa game Na zo Tehran ne da ajandar fadada alaka da Iran da kuma yin hadin gwiwa a dukkan fannoni,” in ji Yarima Khalid,  

Ya kara da cewa “Kuma muna fatan wannan tattaunawar mai ma’ana za ta samar da kyakkyawar alaka tsakanin Saudiyya da Jamhuriyar Musulunci ta Iran fiye da kowane lokaci a tarihi.”

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Iran Da Amurka Za Su Ci Gaba Da Tattaunawa Kan Shirin Nukiliyar Tehran
  • Iran da Amurka na shirin tattaunawa ta biyu a birnin Rome
  • Iran ta yi tir da kakkausar murya da harin Amurka kan tashar mai ta Yemen
  • Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Ce: Za A Gudanar Da Zagaye Na Biyu Na Tattaunawar Iran Da Amurka A Birnin Roma Ne
  • Jagora: Iran a shirye take domin aiki kafada da kafada tare da  Saudiyya
  • Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Bayyana Makasudin Rubuta Sakon Jagora Ga Shugaban Kasar Rasha
  • Babban Jami’in Diblomasiyyar Iran Ya Je Birnin Mosco Don Isar Da Sakon Imam Khaminae Ga Putin
  • Iraki Ce Zata Amfana Da Tattaunawa Tsakanin Iran Da Amurka: Inji Sayyed Ammar Hakim
  • Araghchi: babu tattaunawa kan batun tace sinadarin uranium