An tsinci gawar mabaraci mai shekara 75 a Neja
Published: 19th, April 2025 GMT
An tsinci gawar wani tsoho mai suna Haruna Abdullahi mai shekara 75 daga garin Gumel na Jihar Jigawa a ƙofar babbar kasuwar Kure Ultra Modern Market da ke Minna a Jihar Neja.
Babu wanda zai iya cewa ga musabbabin mutuwarsa, amma ’yan kasuwa sun shaida wa Daily Trust cewa, an tsinci gawarsa da safiyar ranar Juma’a a babbar ƙofar shiga kasuwar.
Kakakin rundunar ’Yan sandan Jihar Neja, SP Wasiu Abiodun ya tabbatar wa Daily Trust faruwar lamarin.
Ya ce, “A yau Juma’a 18/4/2025 da sanyin safiya, an tsinci gawar wani wanda aka bayyana sunansa da Haruna Abdullahi mai kimanin shekara 75 a ƙofar shiga kasuwar Kure.
“An ce mabaraci ne, kuma Bahaushe ne, ɗan jihar Gumel ne, kuma ba a ga wani alamar tashin hankali ba a jikinsa, an kai shi asibiti aka tabbatar da mutuwarsa.”
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
An Kashe Mutane Fiye Da 300 A Wani Kazamin Fada A Yankin Darfur Da Ke Yammacin Kasar Sudan
Mutane fiye 300 ne suka mutu a cikin kwanaki a wani kazamin fada a yankin Darfur da ke yammacin kasar Sudan
Hukumar kula da ayyukan jin kai ta Majalisar Dinkin Duniya ta watsa rahoton cewa: Sama da fararen hula 300 ne aka kashe a wani kazamin fada na kwanaki biyu a yankin Darfur na kasar Sudan mai fama da rikici.
Dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces sun kaddamar da hare-hare a ranakun Juma’a da Asabar a kan sansanonin ‘yan gudun hijira biyu da ke fama da matsalar yunwa a arewacin Darfur da kuma babban birnin da ke kusa, inda rahotannin farko suka nuna cewa sama da mutane 100 ne suka mutu, ciki har da yara 20 da ma’aikatan agaji tara, a cewar wani jami’in Majalisar Dinkin Duniya.
A halin da ake ciki kuma, ofishin kula da ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya (OCHA) ya sanar da samun karuwar adadin wadanda suka mutu a ranar Litinin, kamar yadda wasu majiyoyi na cikin gida suka tabbatar da hakan.