Masu garkuwa za su mutu ta hanyar rataya a Edo – Okepebolo
Published: 19th, April 2025 GMT
Gwamnan Jihar Edo, Monday Okpebholo ya bayyana cewa masu garkuwa da mutane da aka samu da laifi a jihar za su fuskanci hukuncin kisa ta hanyar rataya.
Okpebholo ya bada tabbacin a shirye yake ya sanya hannu akan sammacin kisa na waɗanda aka yankewa hukunci a jihar idan kotu ta same su da laifi.
An tsinci gawar mabaraci mai shekara 75 a Neja PDP ba ta shirya yin zaɓen 2027 ba – WikeGwamna Okpebholo ya bayyana hakan ne a wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a garin Uromi, inda ya tattauna da shugabanni da ’yan uwa na yankin unguwar ’yan Arewa mazauna Esan.
“Ku tuna cewa Majalisar Dokokin Jihar Edo (EDHA) ta zartar da wani ƙudiri na gyara dokar hana garkuwa da mutane (da wasu dokoki da suke da alaƙa da na shekarar 2013)”.
Ƙudirin dokar ya tanadi hukuncin kisa ga masu garkuwa da mutane sannan kuma ya ba da umarnin ƙwacewa da rushe dukiyoyin da ake yin amfani da su wajen aikata laifukan.
A cewar gwamnan, gwamnatinsa ba za ta lamunci rashin tsaro, kisan gilla da kuma garkuwa da mutane ba.
“Na ɗauki batun rashin tsaro da muhimmanci kuma ba zan karkatar da ƙa’idar ba sai dai a yi amfani da su sosai, sabuwar dokar jihar ta ba mu damar rusa kadarorinsu da ƙwace musu filayensu.
“Za mu kawo masu garkuwa da mutane a gaban jama’a, mu kashe su domin mu nuna muhimmancinmu a kan dokokin da Majalisar Edo ta riga ta yi, ba zan ji tsoron sanya hannu a kai ba,” in ji shi.
Gwamnan ya yi kira ga kowa da kowa da su ba gwamnatinsa haɗin kai don tabbatar da tsaron jihar, yana mai cewa “tsaro aikin kowa ne ba na hukumomin tsaro kaɗai ba”.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Gwamnan jihar Edo Hukuncin rataya Masu Garkuwa da mutane Monday Okpebholo garkuwa da mutane masu garkuwa
এছাড়াও পড়ুন:
Amurka ta sanar da cewa za ta rage yawan sojojinta a Syria da rabi
Amurka ta sanar cewa ta rage yawan sojojinta a kasar Syria da rabi, tana mai cewa ta yi nasarar yaki da kungiyar IS, duk da cewa kungiyoyin masu da’awar jihadi na ci gaba da fafutuka a wannan kasa mai rauni.
Wannan shawarar ta zo ne kusan watanni uku bayan hawan Donald Trump kan karagar mulki, bayan da ya dade yana adawa da kasancewar Amurka a can.
Amurka dai ta shafe shekaru da dama tana da sojoji a Syria, a matsayin wani bangare na kawancen kasashen duniya da ke yaki da ISIS.
A cikin wata sanarwa da kakakin ma’aikatar tsaron Amurka ta Pentagon Sean Parnell ya fitar, ya ce za a rage yawan dakarun Amurka a Siriya zuwa kasa da dakaru 1,000 a cikin watanni masu zuwa daga kusan 2,000.