Cibiyoyin Hada-Hadar Kudi Na Ketare Suna Da Kyakkyawar Fata Game Da Kasuwar Lamuni Ta Sin
Published: 19th, April 2025 GMT
Bisa labarin da babban bankin jama’ar kasar Sin ya fitar, ya zuwa ranar 15 ga watan Afrilun shekarar 2025, jimillar cibiyoyin hada-hadar kudi na kasashen waje 1,160 ne suka shiga kasuwar hada-hadar lamuni ta kasar Sin, wadanda suka hada da cibiyoyin hada-hadar kudi masu zaman kansu da cibiyoyin hada-hadar kudi na kasuwanci a kasashe da yankuna fiye da 70, wadanda ke rike da takardun lamuni da yawansu ya kai yuan tiriliyan 4.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Sojojin HKI Suna Ci Gaba Da Kai Hare-hare A Kudancin Lebanon
Sojojin HKI suna cigaba da kai hare-hare a yankunan kudancin Lebanon da ya zama ruwan dare a cikin kwanakin bayan nan.
A jiya Laraba jiragen yakin HKI sun kai hare-hare a gari “Aytas-sha’ab. Haka nan kuma tankokin yakin ‘yan mamayar sun kai wasu hari a kan wasu gidaje a garin na Aytas-sha’ab.
Haka nan kuma sojojin mamayar sun gina wata Katanga da ta raba tsakanin Ayta da Khillatul-wardi.
Har yanzu sojojin na HKI suna ci gaba da zama a cikin wasu wurare biyar da ta ki ficewa daga cikinsu bayan zuwa karshen wa’adin kwanaki 60 daga tsagaita wutar yaki.
Kamfanin dillancin labarun Lebanon ya bayyana cewa; Jirgin yakin HKI maras matuki ya kai hari akan gidajen tafi da gidanka da wadanda aka rushewa gidaje suke ciki a kusa da garin Shaihin. Sai dai babu wani rahoto akan rashin rai,ko jikkatar mutane, sai dai gidaje da dama sun rushe.
Wadannan hare-haren suna a matsayin sabon bude wuce gona da iri na HKI a kudancin Lebanon.
Kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon din ta sha yin kira ga gwamnati da ta yi aiki da nauyin da ya rataya a wuyanta na tilasata wa ‘yan mamaya janyewa daga wuraren da suke ciki.