HausaTv:
2025-04-19@17:10:42 GMT

Iran ta yi tir da kakkausar murya da harin Amurka kan tashar mai ta Yemen

Published: 19th, April 2025 GMT

Iran ta yi tir da Allah wadai da kakkausan lafazi da harin Amurka na baya baya nan kan tashar mai ta kasar Yemen, wanda ya yi sanadin mutuwar gomman mutane tare da lalata dukiya mai yawa.

Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran, Esmail Baghai, ya kira harin da Amurka ta kai a matsayin keta kundin tsarin mulkin MDD da kuma dokokin kasa da kasa karara.

Misata Baghai ya ce : “Hare-haren da Amurka ta kai kan kasar Yemen, a matsayin cikakken goyon bayanta ga mamaya da kuma kisan kiyashin da gwamnatin sahyoniya ta ke yi a yankunan Falasdinawa, ya sanya Amurka ta zama mai hannu dumu-dumu a kan laifukan da Isra’ila ke aikatawa a Falastinu da kuma yankin.”

Akalla mutane 80 ne suka rasa rayukansu tare da jikkata wasu 150 a harin da Amurka ta kai kan tashar jiragen ruwan ta Ras Issa a Yemen.

Wannan dai shi ne hari mafi muni tun bayan fara farmakin na Amurka a Yemen yau sama da watanni 15.

Sojojin Amurka sun sanar da cewa sun kai hari tare da lalata tashar jiragen ruwa na Ras Issa da ke lardin Hodeida a ranar Alhamis da nufin hana ‘yan Houthi kudaden shiga da suke amfani da su wajen daukar nauyin ayyukansu da kuma ta’addanci a yankin.

Saidai ‘yan Houtsis, sun ce ‘’Ras Issa “tashar ruwa ce ta farar hula inda jiragen ruwa da ke dauke da mai da dizal da iskar gas ke isa domin raba mai ga dukkan yankunan Yemen.”

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Rasha ta ce tana bibiyar tattaunawar Iran da Amurka matuka

Rasha ta ce tana ta na sa ido sosai game da tattaunawa karo na biyu tsakanin Amurka da Iran kuma a shirye take ta taimaka wajen warware shirin nukiliyar Iran ta hanyar siyasa da diflomasiyya.

Makomar shirin nukiliyar Iran da kuma zaman lafiyar yankin na iya danganta ne kan ko Washington da Tehran za su koma kan teburin shawarwari.

Yayin da tattaunawar tsakanin Amurka da Iran ta tsaya cik a baya, manyan kasashen duniya musamman Rasha da China sun yi yunkurin ganin neman farfado da tattaunawar ta diflomasiyya.

Tunda farko a makon da ya gabata Majalisar Tarayyar Rasha ta amince da yarjejeniyar hadin gwiwa ta tsawon shekaru 20 a hukumance da Iran, wanda ke karfafa kawancen dogon lokaci tsakanin kasashen biyu a fannonin da suka hada da tsaro, makamashi da fasaha.

Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya sanar a yau Laraba cewa, zai je birnin Moscow domin kai  sakon Jagoran juyin juya halin musulinci Ayatollah Ali Khamenei ga shugaba Vladimir Putin.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Amurka Ta Kaddamar Da Sabbin Hare-Hare Kan Garuruwan Sana’a, Sa’adah Da Al-Jawf Na Kasar Yemen
  • Dakarun Gwagwarmayar Yemen Sun Kai Hare-Haren Daukan Fansa Kan Haramtacciyar Kasar Isra’ila
  • Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kaduna Ya Yi Bikin Easter Tare da Al’ummomin Kiristoci
  • Iran Tace Yarjeniya Da Amurka Mai Yuwa Ne Idan Da Gaske Take
  • Sojojin Kasar Yemen Sun Kai Hare Hare Kan HKI Da Jiragen Yakin Amurka
  • Yawan Mutanen Da Suka Yi Shahada A Harin Amurka Na Jiya A Yemen Ya Kai 74
  • Amurka Ta Kashe Mutane 38 Tare Da Jikkata Fiye Da 100 A Harin Da Ta Kai Lardin Al-Hudaidah Na Yemen
  • Jagora: Iran a shirye take domin aiki kafada da kafada tare da  Saudiyya
  • Rasha ta ce tana bibiyar tattaunawar Iran da Amurka matuka