Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta sanar da cewa za ta gudanar da atisayen harbe-harbe ga sabbin ‘yan sanda a karamar hukumar Birnin Kudu ta jihar Jigawa.

 

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Jigawa, Ahmad Tijjani Abdullahi ya bayyana haka a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Dutse babban birnin jihar.

 

Ya ce, atisayen zai fara ne daga ranar 19 ga Afrilu zuwa 11 ga Mayu 2025 a kauyen Tsohon Kafi da ke Birnin Kudu.

 

A cewarsa, makasudin bayar da horon shi ne don inganta shirye-shiryen gudanar da aiki, da dabarun sarrafa makamai, da kuma kwarjinin sabbin jami’an ‘yan sandan da aka dauka, a daidai lokacin da rundunar ‘yan sandan Najeriya ta himmatu wajen tabbatar da kwarewa da tsaron lafiyar jama’a.

 

Don haka rundunar ta bukaci mazauna kauyen Tsohon Kafi da kewaye da kada su firgita da jin karar harbe-harbe a yayin atisayen.

 

Abdullahi ya ce, za a sanya ido sosai a kan dukkan ayyukan da kuma gudanar da su a cikin yanayi mai aminci da kulawa.

 

Rundunar ta kuma yaba da ci gaba da goyon baya da hadin kan al’umma wajen tallafawa kokarin wanzar da zaman lafiya da tsaro a fadin jihar.

 

KARSHE/USMAN MZ

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Harbe Harbe Jigawa

এছাড়াও পড়ুন:

Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Ce: Za A Gudanar Da Zagaye Na Biyu Na Tattaunawar Iran Da Amurka A Birnin Roma Ne

Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Za a gudanar da zagaye na biyu na tattaunawar ba na kai tsaye ba da Amurka a birnin Roma a ranar Asabar

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya sanar da cewa zai tafi birnin Roma a ranar Asabar domin halartar zagaye na biyu na shawarwari ba na kai tsaye ba da Amurka, yana mai jaddada cewa sakon da Jagoran juyin juya halin Musulunci ya aikewa shugaban kasar Rasha ya kunshi muhimman batutuwa.

A cewar kamfanin dillancin labaran IRNA, Araghchi ya ce: Roma ba ita ce mai masaukin baki ba, a’a, a maimakon haka, wajen da za a yi shawarwarin, gwamnatin Oman ce ta kasance mai daukar nauyin shawarwarin ba na kai tsaye ba tsakanin Iran da Amurka, kuma Iran za ta kasance a wurin da mai masaukin bakin ya kayyade, aikin shiga tsakani da kulla huldar da ba na kai tsaye ba, shi ne alhakin gwamnatin masarautar Oman.”

Ya kara da cewa, “Zai tafi Roma ranar Asabar kuma za a fara zagaye na biyu na tattaunawar ba na kai tsaye ba tsakanin Iran da Amurka.

Arakchi ya ce: Rasha da sauran kasashe sun bayyana aniyarsu ta taimaka wajen ciyar da shawarwarin gaba.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • ‘Yan Sandan Sun Ceto Wasu Mutane Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Zamfara
  • Rundunar ‘Yansanda Ta Tuhumi Jami’anta Da ‘Yan Kasar Sin Ke Raba Wa Kudi A Wani Bidiyo Da Ke Yawo
  • Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Ce: Za A Gudanar Da Zagaye Na Biyu Na Tattaunawar Iran Da Amurka A Birnin Roma Ne
  • Hukumar NSCDC ta tura jami’an tsaro 415 domin aikin Easter a Zamfara.
  • Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Gombe Ta Bada Tabbacin Tsaro A Bukin Ista
  • An Fara Bada Horo Ga Masu Horas da Maniyatan Bana A Jigawa
  • An Fara Bada Horo Ga Masu Horas da Mabiyan Bana A Jigawa
  • Hukumar Alhazai ta Jigawa Ta Shirya Bitar Ga Malaman Bita na Kananan Hukumomi 27
  • Babban Jami’in Diblomasiyyar Iran Ya Je Birnin Mosco Don Isar Da Sakon Imam Khaminae Ga Putin