Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta yi nasarar kubutar da wasu mutane shida da aka yi garkuwa da su, a wani samame da ta gudanar cikin gaggawa tare da tabbatar da ganin an dawo da zaman lafiya da tsaro a fadin jihar.

 

A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan, DSP Yazid Abubakar ya fitar, ya ce a ranar 16 ga Afrilu, 2025, da misalin karfe 1:45 na rana, tawagar hadin guiwa da ta kunshi jami’an ‘yan sanda da kuma jami’an kare hakkin jama’a (CPG) suna sintiri a kan babbar hanyar Anka-Gummi, inda suka gano wata mota samfurin Peugeot 206 da suka yi garkuwa da su a gefen hanya.

 

A cewar sanarwar, ba tare da bata lokaci ba, tawagar jami’an tsaro ta fara gudanar da wani bincike na hadin gwiwa, wanda ya kai ga ceto mutane shida da aka yi garkuwa da su, yayin da mutanen da aka ceto suka koma ga iyalansu.

 

Ta ce kwamishinan ‘yan sandan jihar Zamfara, CP Ibrahim Balarabe Maikaba, ya yabawa ‘yan sandan bisa gaggauwa da daukar matakin da suka dauka.

 

Ya nanata kwazon rundunar tare da sauran jami’an tsaro na ganin an ceto duk wadanda aka sace tare da tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi a fadin jihar.

 

CP Maikaba ya kuma yi kira ga al’ummar yankin da su sanya ido tare da gaggauta kai rahoton duk wani abin da ba su gane ba ga jami’an tsaro mafi kusa da su domin kawo dauki cikin gaggawa.

 

Sanarwar ta kuma jaddada cewa, rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta ci gaba da jajircewa wajen ganin ta wargaza maboyar barayi da kuma dawo da zaman lafiya mai dorewa a jihar.

 

REL/AMINU DALHATU.

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Tsaro Zamfara

এছাড়াও পড়ুন:

Zargin Ganduje: Za mu sanar da lokacin yanke hukunci —Kotu

Mai Shari’a Amina Adamu Aliyu ta Babbar Kotun ta Jihar Kano ta ce za ta yanke hukunci nan gaba a shari’ar cin hanci da rashawa da ake yi wa Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa, Abdullahi Ganduje, da matarsa Hafsat, da wasu mutane da kamfanoni shida.

Gwamnatin Jihar Kano ta tuhumi waɗannan mutane da kamfanoni da laifuka guda takwas da suka haɗa da karɓar rashawa, yin amfani da kuɗin jama’a ta haramtacciyar hanya, da kuma satar kuɗin gwamnati.

Ganduje ya yi gwamnan Jihar Kano daga shekarar 2015 zuwa 2023.

Lauyan Ganduje ya roki kotu da ta ba shi karin lokaci a shari’ar amma lauyan gwamnati ya soke wannan roko kuma ya bukaci kotu da ta yi watsi da shi.

Ka dawo Najeriya ka magance matsalar tsaro —Obi ga Tinubu Gwamnatin Tarayya ta buƙaci ’yan jarida su daina kawo rahoton ayyukan ’yan ta’adda Hisbah ta kama matashi yana ‘lalata’ da Akuya a Kano

Lauyoyin wasu mutane da kamfanoni da ake tuhuma a shari’ar sun kuma gabatar da wasu batutuwa kuma sun roki kotu da ta na su gaskiya tare da umartar gwamnati da ta biya su diyya.

Mai Shari’a Amina Adamu Aliyu ta dakatar da sauraron ƙarar kuma ta ce za ta sanar da dukkan waɗanda abin ya shafa ranar da za ta yanke hukuncinta daga baya.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • ’Yan sanda sun ceto ɗalibai 10 sun kashe ɗan bindiga a Edo
  • Rundunar ‘Yansan Nijeriya Za Ta Gudanar Atisaye Ga Jami’anta a Jigawa
  • ’Yan sanda sun ceto ɗalibai 10 sun lashe ɗan bindiga a Edo
  • Masu garkuwa za su mutu ta hanyar rataya a Edo – Okepebolo
  • Hukumar NSCDC ta tura jami’an tsaro 415 domin aikin Easter a Zamfara.
  • Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Gombe Ta Bada Tabbacin Tsaro A Bukin Ista
  • An Kashe Mutane Fiye Da 300 A Wani Kazamin Fada A Yankin Darfur Da Ke Yammacin Kasar Sudan
  • Zargin Ganduje: Za mu sanar da lokacin yanke hukunci —Kotu
  • An Kashe Mutane 7 A Yayin Da ‘Yan Ta’adda Suka Ƙaddamar Da Wani Sabon Hari A Adamawa