Aminiya:
2025-04-19@17:13:55 GMT

An buɗe wa jami’an NDLEA wuta a Abuja

Published: 19th, April 2025 GMT

Jami’an Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA) sun tsallake rijiya da baya da raunukan harbin bindiga bayan da ɓata-gari suka buɗe musu wuta a lokacin da suka kama miyagun ƙwayoyi a Yankin Banban Birnin Tarayya.

Mutum uku daga cikin jami’an sun samu raunuka an harbi, ɗaya a haƙari, biyu a gadon baya da kafafunsu, a yayin harin da aka kai musu a unguwar Jahi, bayan sun kama wasu miyagun ƙwayoyi a ranar Alhamis.

Kakakin NDLEA na ƙasa, Femi Babafemi, ya bayyana cewa an kwantar da jami’an guda uku a asibiti saboda raunukan harbin bindiga da suka samu.

“Lamarin ya faru ne a lokacin da tawagar jami’an NDLEA, bisa bayanan sirri, suka kai samame wani kwangon gini a yankin NNPC da ke unguwar Jahi inda aka ƙwato kwalaben codeine guda 74, codeine ta ruwa lita 10, gram 48 na tramadol mai milligram 225, da kilogiram 4.9 na skunk, wani nau’in tabar wiwi, da kuma wayoyin android guda biyar.

’Yan sanda sun ceto ɗalibai 10 sun lashe ɗan bindiga a Edo Makarantar Bare: Shekara 20 dalibai na karatu a matsanancin yanayi

“Yayin da tawagar NDLEA ke hanyarsu ta fita daga wurin kuma an kai musu harin bindiga,” in ji Babafemi a cikin sanarwar da ya fitar washegari da daddare.

Babafemi ya ce, an fara ba da kulawar gaggawa ga jami’an da suka ji rauni a asibitin ’yan sanda da ke Garki Area 1 kafin a mayar da su Babban Asibitin Abuja domin ƙarin kulawa.

Shugaban Hukumar NDLEA, Birgediya Mohamed Buba Marwa (Mai Ritaya), ya yaba wa ma’aikatan asibitin ’yan sanda bisa ga agajin gaggawar da suka bayar.

Ya kuma gode wa Shugaban Asibitin Ƙasa, wanda shi da kansa ya tuntube shi domin ya kula da jinyar jami’an da suka ji rauni.

Shugaban NDLEA, wanda ke Kano a kan ayyukan hukuma, ya kuma yi magana ta waya da jami’an da suka ji rauni domin yi musu fatan samun sauƙi cikin gaggawa.

Ya ba su tabbacin cewa hukumar za ta yi amfani da duk wata hanya da take da ita kuma za ta yi aiki tare da sauran hukumomin tsaro domin gano waɗanda ke da alhakin kai musu harin.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: ƙwayoyi

এছাড়াও পড়ুন:

Hamas ta gabatar da shawara kan yarjejeniyar musayar fursunoni da tsagaita wuta

Shugaban ofishin siyasa na Hamas Khalil al-Hayya ya sanar da cewa, kungiyar a shirye take ta shiga cikin tattaunawa don tabbatar da cimma cikakkiyar yarjejeniyar musayar fursunoni, da tsagaita bude wuta a Gaza, da janyewar Isra’ila daga yankin, da kuma kaddamar da yunkurin sake gina yankin.

A cikin wani jawabi da kungiyar ta fitar, al-Hayya ya bayyana cewa, kungiyar Hamas a shirye take ta sako dukkan fursunonin da ‘yan gwagwarmaya ke tsare da su domin samun adadin fursunonin Falasdinawa da aka amince da su a halin yanzu da ake tsare da su a gidajen yarin Isra’ila.

Ya jaddada cewa, dole ne irin wannan yarjejeniyar ta hada da dakatar da yakin gaba daya, da janyewar sojojin Isra’ila baki daya daga Gaza, da fara aikin sake gina yankin, da kuma kawo karshen killacewar da ake yi wa yankin.

Al-Hayya ya yi maraba da kalaman na baya-bayan nan da Adam Boehler, wakilin Amurka a karkashin Shugaba Donald Trump ya yi, wanda ya bayar da shawarar magance matsalolin fursunonin da yakin da ake yi.

Al-Hayya ya bayyana matsayar Boehler a matsayin shawara mai kyau kuma ta daidai da mahangar Hama,s sannan ya nanata shirin kungiyar na cimma cikakkiyar yarjejeniya a karkashin wadannan sharudda.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • ’Yan sanda sun ceto ɗalibai 10 sun kashe ɗan bindiga a Edo
  • ‘Yan Sandan Sun Ceto Wasu Mutane Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Zamfara
  • ’Yan sanda sun ceto ɗalibai 10 sun lashe ɗan bindiga a Edo
  • Rundunar ‘Yansanda Ta Tuhumi Jami’anta Da ‘Yan Kasar Sin Ke Raba Wa Kudi A Wani Bidiyo Da Ke Yawo
  • Hukumar NSCDC ta tura jami’an tsaro 415 domin aikin Easter a Zamfara.
  • Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Gombe Ta Bada Tabbacin Tsaro A Bukin Ista
  • Hamas ta gabatar da shawara kan yarjejeniyar musayar fursunoni da tsagaita wuta
  • ’Yan bindiga sun sace makiyaya 5, da shanu 1,200 a Kaduna
  • Bai Wa Shanu Guba: Sojoji Sun Shiga Tsakani Domin Dakile Yunkurin Ramuwar Gayya A Filato