Sojojin Sudan Sun Kashe ‘Yan Tawayen Kasar Ciki Har Da Manyan Kwamandojinsu A Birnin El Fasher
Published: 19th, April 2025 GMT
Sojojin Sudan sun sanar da kashe mayakan dakarun kai daukin gaggawa 70, ciki har da kwamandojin mayakan a birnin a El Fasher fadar mulkin jihar Darfur ta Arewa
A ranar Alhamis ne rundunar sojin Sudan ta sanar da kashe mayakan da jami’an dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces fiye da 70 da suka hada da kwamandojin ‘yan tawaye a shiyar kudu maso gabas da arewa maso gabashin El Fasher.
Kamfanin dillancin labaran Sudan (SUNA) ya watsa rahoton cewa: A ranar Alhamis ne sojojin kasar Sudan tare da hadin da tallafin dakarun hadin gwiwa na kungiyoyin fafutuka, da hukumar leken asiri ta kasar da ‘yan sanda, suka dakile wani mummunan hari da dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces suka kaddamar kan shiyar kudu maso gabas da arewa maso gabashin El Fasher.
Majiyar ta tabbatar da cewa artabun ya yi sanadin lalata motocin yaki guda 15, da motocin dakon mai. Ta kuma tabbatar da cewa, an samu nasarar lalata da dama daga cikin motocin mayakan Dakarun Rapid Support Forces ciki har da manyan jami’an rundunar da yawansu ya haura 70 da suka hada da kwamandoji da dama baya ga wani adadi mai yawa da suka jikkata, yayin da sauran suka gudu, inda suka bar matattu da wadanda suka jikkata a filin daga.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Mayakan Kungiyar Ta’addanci Ta ISIS Sun Sake Kunno Kai A Garuruwan Deir ez-Zor Da Hasaka Na Siriya
Mayakan kungiyar ta’addanci ta ISIS sun sake kunno kai a garuruwan Deir ez-Zor da Hasaka na kasar Siriya
Yankunan Deir ez-Zor da Hasakah dake arewa maso gabashin kasar Siriya suna ci gaba da samun karuwar bullar ayyukan ta’addancin kungiyar ISIS tun daga farkon wannan wata. Hare-hare 13 sun kai sune kan Dakarun Syrian Democratic Foeces ta (SDF) ta Kurdawa masu samun goyon bayan Amurka da kuma fararen hulan yankunan, lamarin da ya janyo hasarar rayuka.
A cewar kungiyar kare hakkin bil- adama ta Syria, hare-haren sun bambanta wajen aiwatar da su, daga harin kwanton bauna zuwa na kai hari kai tsaye, wanda ke nuni da yadda kungiyar ta canza yanayin kai hare-hare a yankunan saboda matakan tsaron a garuruwan. Wadannan al’amura sun kuma nuna cewa kungiyar ta’addancin na ci gaba da yin barazana a arewaci da gabashin Siriya.