Wang Yi Ya Yi Bayani Kan Ziyarar Shugaba Xi Jinping A Vietnam Da Malaysia Da Cambodia
Published: 19th, April 2025 GMT
A yayin wannan ziyara har ila yau, shugaba Xi Jinping ya jaddada cewa, yakin cinikayya zai gurgunta tsarin cinikayyar kasa da kasa, da haifar da mummunan tasiri a kan tattalin arzikin duniya, da tarnake halaltacciyar moriyar kasashen duniya, musamman ma ta kasashe masu tasowa.
Sai dai kuma, yayin da ake fuskantar karuwar masu nuna ra’ayin kariyar ciniki a duniya, kasar Sin za ta tsaya kan kokarin tabbatar da ci gaban tattalin arziki, kuma za ta ci gaba da samar da dimbin gudummawa ga yunkurin raya tattalin arzikin duniya, in ji shugaban kasar Sin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Ka-ce-na-cen da ya biyo bayan ziyarar Tinubu a Katsina
Gwamnan Jihar Katsina Umaru Dikko Raɗɗa, ya ce ba shi da masaniyar wani allo da aka kafa mai ɗauke da saƙon ce wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu babu ƙorafi a Katsina ba kamar yadda ake ta muhawara a kai a ƙasar.
Hakan na ƙunshe cikin wani saƙon murya ta gwamnan da aka fitar da ke martani a kan ce-ce-ku-cen da ya kaure a Nijeriya kan wani allon saƙo da aka kakkafa a Katsina lokacin da Shugaba Tinubu ya halarci auren ‘yar gwamnan.
DAGA LARABA: Ɓoyayyun Dalilan Da ke Sa Faɗuwa Jarabawa A Najeriya Yaƙi ya ɓarke tsakanin Indiya da PakistanGwamna Raɗɗa ya ce yana da kyau a riƙa bincike kafin yanke hukunci kan abubuwa.
“Na saurari muryar da aka turo aka ce daga Alhaji Garba Dangida ne da kuma Janar Tsiga, kuma na yi godiya sosai da wannan voice da na ji, kuma ina fatan Allah Ya saka musu da alheri.
“Amma abin da nake so na ce shi ne ya kamata a riƙa bincike idan an ji labari a soshiyal midiya ko a zahiri kuma a riƙa tambaya,” in ji gwamnan.
Lamarin dai ya jawo zazzafar muhawara da ce-ce-ku-ce daga ko ina a faɗin Nijeriya, inda masu sharhi ke cewa jihar da ke fama da ƙalubalen tsaro bai kamata ta nuna wa Shugaban Ƙasa cewa ba ta da wani ƙorafi ba.
Sai dai Gwamna Raɗɗa ya ce sun tattauna matsaloli uku da ke damun Jihar Katsina da Shugaban Ƙasar da suka haɗa da matsalar rashin tsaro da aikin samar da lantarki daga iska na Rimi da ayyukan filin jiragen sama da aka tsaida.
“Maganar hanyoyi kuwa da kansa (Shugaban Ƙasa) dama ya yi kuma hanyoyin an ba da aikinsu kuma mun shaida wa Shugaban Ƙasa wannan.
Amma a kan batun allon talla da aka rubuta Katsina babu ƙorafi gwamnan ya ce “Maganar billboard da wani ya buga na cewa ‘Katsina Ba Ƙorafi’ ni a matsayina na gwamna ban ma san an buga shi ba sai da na gani a soshiyal midiya nake tunanin yaya aka buga shi, wa ya buga shi.”
Raɗɗa ya koka cewa kuskure ne idan aka dinga jam’i ana zargin mutane a kan abin da a zahirance sun tabbatar ba su yi ba.
“Amma ku manyanmu ne iyayenmu ne idan kun ga wani abu na kuskure kuna iya mana magana muna iya gyarawa, mu kuma mutane ne muma kamar kowa muna iya yin kuskure muna iya yin ba daidai ba.
“Amma dai don Allah a matsayin manya da iyaye idan kun ji abu a soshiyal midiya ku dinga kiranmu ku ji yaya abin ya kasance ba wai a tafi soshiyal midiya a dinga irin wadannan maganganun ba.
“Ina ga ba za su taimake mu ko kawo mana ci gaban da muke buƙata ba a Katsina,” a cewar gwamnan.
A ƙarshen saƙon muryar na ranar Talata mai tsawon minti 2.48, Raɗɗa ya ce “shugabancin nan idan Allah Ya ba ka shi kowa na iya kuskure yana iya daidai.
“Muna fatan Allah ya dora mu bisa daidan. Amma dai a wannan labarin da aka ba da ba haka yake ba.
Ka-ce-na-cen da ya biyo bayaGwamna Raɗɗa ya fitar da wannan jawabin ne bayan ka-ce-na-cen da ya kaure game da ziyarar kwana biyu ta Shugaba Tinubu a Katsina, ɗaya daga jihohin Arewa maso Yamma da ke cikin masifar rikicin ‘yan fashin daji.
Ka-ce-na-ce ya ɓarke ne har a shafukan sada zumunta tun lokacin da aka fara ganin wasu manyan allunan da aka kakkafa ɗauke da saƙon ‘Katsina Ba Ƙorafi’, a yayin ziyarar Tinubu.
Saƙon “Katsina Ba Ƙorafi” ga alama ya jefa ɗimbin mutane cikin mamaki, inda suke neman sanin hikimar nuna wa Tinubu cewa jihar ba ta da wani ƙorafi.
Mutane masu yawa ba kawai a Katsina ba, har ma a Arewacin Najeriya na ganin ziyarar wata gagarumar dama ce ta yi wa Tinubu gamsasshen bayani kan matsalolin tsaro da na tattalin arziƙi da suka fi addabar jihar.
Da dama a yanzu na cike da wasu-wasi. Suna tunanin ko saƙon “Katsina Ba Ƙorafi” ne ainihin jawaban da manyan ’yan siyasar jihar suka yi wa Tinubu a tsawon kwana biyu da ya kwashe a can.
Yayin da wasu ke kallon saƙon a matsayin tumasanci, ba-ni-na-iya da bambaɗancin ’yan siyasa da ke son burge Tinubu, duk da al’ummominsu na ci gaba da shan azabar tsananin talauci da yunwa da kuma hare-haren ’yan fashin daji.
BBC ya ruwaito yadda mutane da yawa sun yi ta bayyana ra’ayoyi mabambanta a shafukan sada zumunta game da batun.
Wani Abdullahi Mansir Gafai ya yi tambaya a shafinsa na Facebook cikin Ingilishi cike da kaɗuwa cewa ‘Katsina Ba Ƙorafi?’.
“Wane irin cin fuska ne wannan. Wannan wata zolayar rashin kunya ce ga mutanen da ke kwarma ihu a zuci da kuma a sarari yayin da suke dulmiya cikin tsoro da yunwa da kuma ƙaƙa-ni-ka-yin rayuwa.
“Don a sani, ban da masifar hare-haren ’yan fashin daji, Katsina na ɗaya daga cikin jihohi mafi talauci a Najeriya.”
Ya ƙara da cewa: “Yayin da Shugaba Tinubu ke sharɓar liyafar ƙasaita a Katsina rahotannin ”yan fashi sun auka wa garuruwa a Faskari da Bakori da Dutsin Ma da Ƙanƙara da Ɗan Musa, tuni sun cika gari.
“Wani zai cika da murna kan irin wannan dama wadda ba a cika samu ba da ta faɗo wa Gwamna Raɗɗa don ya zayyana ‘ƙorafe-ƙorafen’ al’ummarsa, amma maimakon haka sai ya zaɓi nuna ƙwambo da wadaƙa.
Haka zalika, wani mai suna Kabiru Garba ya wallafa cewa: “Amma fa wannan wulaƙanci ne na ƙarshe wallahi.
“Da a ce Jagaban (Shugaba Tinubu) yana jin Hausa, kuma ya ga wannan shirmen to tabbas sai ya ce mu wawaye ne ko da a ransa ne.”
Za a kai mu a baro — Dattawan KatsinaIta dai muryar dattijan da aka ce saboda tsokacinta ne Gwamna Raɗɗa ya mai da martani ta zargin dattijan jihar Katsina da zuba ido kawai, ba tare da yunƙurin taka wa Dikko Raɗɗa burki ba.
Ɗaya daga cikin muryoyin ta nuna takaici kan yadda dattijan suka gaza haɗuwa su fito da matsalolin al’ummar jihar, don tunkarar Tinubu su yi masa jawabi.
“Mutane manya su sadu da shi, su yi masa magana. Ai zai je wajen sarki ko, sarki ma ya yi mishi magana.
“Ya ga cewa duk inda ya isa, ya ga gwamna ya yi mishi magana, elders (dattijai) sun mishi magana, dole ya samu abin da zai yi.”
Ya ƙara da cewa: “Mu akwai abin da yake damun mu irin…. rashin tsaro (insecurity) da talauci mai kassara al’umma?
Ya kuma ce kamata ya yi su iya ƙarfin hali da nuna dattakon da za su tunkari haƙiƙanin matsalolinsu na rayuwa.
Ɗaya muryar ta zargi Gwamna Raɗɗa da “sakarcin” shaida wa Tinubu cewa Katsina ba ta da ƙorafi, inda ya ce kamata ya yi dattijan jihar su kira taron manema labarai domin nisanta kansu da wannan iƙirari.
Ya ce da sun yi haka, gwamnan zai san idanun mutane na kansa, kuma zai shiga taitayinsa.
“Maganar gaskiya, wannan abin damuwa ne. In ba mu tashi ba tsaye, wallahi Katsina za a kai mu a baro mu.”