Aminiya:
2025-04-19@21:22:15 GMT

Shin Mataimakin Gwamnan Bauchi ya ‘mari’ Ministan Tinubu?

Published: 19th, April 2025 GMT

Rahotanni na cewa Mataimakin Gwamnan Bauchi, Auwal Mohammed Jatau, ya zabga wa Ministan Harkokin Waje, Yusuf Maitama Tuggar, mari saboda kalaman suka da ya yi kan gwamnatin jihar.

Wasu rahotanni na cewa Ministan ya yi wasu kalamai na caccaka ga Gwamna Bala Mohammed, lamarin da ya fusata mataimakinsa ya ɗauke Ministan da mari.

An shiga ruɗani kan satar al’aurar maza a ƙasar Chadi JAMB ta sauya ranar soma jarrabawar bana

Bayanai sun ce lamarin ya faru ne a cikin motar da ke dakon wasu manyan jami’an gwamnati, ciki har da Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, yayin da suke kan hanyar zuwa naɗin sarauta da kuma ɗaurin auren ’yar tsohon gwamnan jihar, Muhammad Abdullahi Abubakar SAN.

Aminiya ta ruwaito cewa, a Juma’ar da ta gabata ce manyan jami’an gwamnati suka halarci ɗaurin auren Khadija Muhammad, da kuma naɗin sarautar Makama Babba I da aka gudanar a Fadar Sarkin Bauchi.

Sai dai cikin wata sanarwar mayar da martani kakkausa kan lamarin, kakakin mataimakin gwamnan, Muslim Lawal, ya musanta labarin, yana mai nanata cewa ubangidansa mutum ne mai mutunci da kamala da ba zai taɓa tsoma kansa cikin irin wannan hauragiya ba.

Amma wani da abin ya faru kan idonsa kuma ya buƙaci a sakaya sunansa, ya shaida wa Aminiya cewa, Mataimakin Gwamnan ya fusata ne bayan Ministan Harkokin Wajen ya riƙa jifar Gwamna Bala Mohammed da kalamai marasa daɗi. Majiyar ta ce wannan ce ta sanya rikicin ya hautsine a cikin motar da ke dakon manyan jami’an gwamnatin zuwa Fadar Masarautar Bauchi. Aminiya ta yi ƙoƙarin jin ta bakin Minista Yusuf Tuggar ya ci tura har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton.

Sai dai ɗan gwamnan jihar, Shamsuddeen Bala Mohammed na daga cikin waɗanda suka yi farin ciki da faruwar lamarin wanda ya riƙa tashe a dandalin sada zumunta na X.

Cikin wata wallafa mai tashe da ɗan gwamnan ya ƙara yaɗawa, mai ɗauke da saƙon cewa, “Mataimakin Gwamna na farko da ya mari Minista a Bauchi. Mista Taka ka sha mari….” da sauran saƙonni makamancin wannan da suke tashe.

Ana iya tuna cewa, wannan tsamin dangantaka ya samo asali ne tun bayan da Gwamna Bala Mohammed ya riƙa sukar Shugaba Bola Tinubu kan rashin shugabanci nagari.

A cewar gwamnan, manufofin da gwamnatin Tinubu ta ƙaƙaba sun jefa al’ummar ƙasar nan cikin ƙangin talauci da tsadar rayuwa.

Sai dai a martanin da Ministan ya mayar, ya ce gwamnan na fakewa da manufofin Tinubu domin ɓoye gazawarsa da zummar samun karɓuwa wajen neman kujerar shugabancin Nijeriya a Zaɓen 2027.

Wannan dai na zuwa ne a yayin da ake zargin cewa shi kansa Ministan na fafutikar zama Gwamnan Bauchi a 2027.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Jihar Bauchi mari Ministan Harkokin Waje Yusuf Tuggar Mataimakin Gwamnan Mataimakin Gwamna

এছাড়াও পড়ুন:

Kada Kanawa su bari rigingimun siyasa su hana su zaman lafiya — Shettima

Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima ya shawarci Kanawa kan kada su bari bambance-bambancen aƙidu na siyasa su zama silar hana su zaman lafiya da haɗin kai.

Ya faɗi hakan ne a jawabinsa lokacin da ya je yi wa Shugaban APC na Kano, Abdullahi Abbas, ta’aziyar rasuwar mahaifinsa — Galadiman Kano, Abbas Sunusi.

Shin Mataimakin Gwamnan Bauchi ya ‘mari’ Ministan Tinubu? An shiga ruɗani kan satar al’aurar maza a ƙasar Chadi

Shettima ya jaddada muhimmancin zaman lafiya da haɗin kai, yana mai bayyana Kano a matsayin madubin Arewacin Nijeriya.

Yayin da yake nanata muhimmancin zaman lafiya, ya bayyana cewa kada a yi sake da Kano, inda ya buga misali da yadda rashin zaman lafiya ya ɗaiɗaita Jihar Borno.

Shettima ya yi kira ga dukkan masu ruwa da tsaki a fannin siyasa da su ajiye banbancin aƙidu, su bai wa ci gaban Kano fifiko a kan komai.

Ya tunatar da cewa Jihar Kano wata cibiya da kusan duk jihohin Arewa suka kewaye kuma ta zama tamkar wata ƙofa da ta zama mahaɗar jihohin

“Idan za ka je Borno ko Bauchi ko Sakkwato, dole ne sai ka bi ta Kano. Saboda haka Kano jiha ce ta kowa.

Aminiya ta ruwaito cewa, Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya yi Mataimakin Shugaban Ƙasar rakiya a yayin ziyarar ta’aziyyar da ya kai gidan marigayi Galadiman Kano.

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kada Kanawa su bari rigingimun siyasa su hana su zaman lafiya — Shettima
  • Shin Ziyarar Bazata Zuwa Gidan Budurwa Daga Saurayi Na Bata Wa ‘Yanmatan Rai?
  • Manyan jami’an gwamnati sun halarci auren ’yar tsohon Gwamnan Bauchi
  • Fadar Shugaban Kasa Ta Yi Watsi Da Zargin Takurawa Mataimakin Shugaban Kasa Shettima
  • Gwamna Abdulrazaq Ya Bukaci Kiristoci Da Su Tuna Da Darussan Lokacin Ista
  • Gwamna Umar Namadi Ya Dauki Matakan Kai Jihar Jigawa Babban Matsayi
  • Neja Za Ta Kaddamar da Ayyukan Jiragen Sama Daga Filin Jirgin Sama na Bola Ahmed Tinubu.
  • Ba a taɓa Dimokraɗiyya mai tsafta a Najeriya kamar mulkin Tinubu ba – Matawalle
  • Ka dawo Najeriya ka magance matsalar tsaro —Obi ga Tinubu