Kafafen watsa labarun HKI sun ambaci cewa sojansu daya ya halaka a Gaza yayin da wasu 4 su ka jikkata bayan da aka kai wa motar da take dauke da su mai sulke hari.
Majiyar ta kuma ce ana ci gaba da yin fada mai tsanani a tsakanin sojojin Isra’ilan da kuma ‘yan gwagwarmaya a yankunan daban-daban na zirin Gaza.
Majiyar Falasdinawa ta ce; ‘yan gwgawarmaya sun tarwatsa wata tankar yakin HKI ta hanyar tashin wani bom da aka ajiye a kan hanya.
An ga jiragen yakin HKI masu saukar angulu suna jigilar daukar wadanda su ka jikkata sanadiyyar harin.
A gefe daya, Falasdinawa da dama sun yi shahada a wasu hare-hare da ‘yan sahayoniya su ka kai akan yankin na Gaza. Tun da safiyar yau Asabar ne dai ‘yan sahayoniyar su ka rika kai hare-haren wanda ya yi sanadiyyar shahadar Falasdinawa 30.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Kasar Pakistan Ta Kara Jaddada Dokar Rashin Amincewa Da HKI A Matsayi Kasa
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Pakisatan ta kara jaddada matsayinta na rashin amince da HKI a matsayin kasa tana kuma goyon bayan Falasdinawa a gwagwarmayan da suke yi na kwatar yencinsu da kuma kasarsu daga hannun HKI da kuma kasashen yamma musamman Amurka masu goya mata.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran wannan sanarwan tazo ne bayan da hukumar kare hakkin bil’adama ta MDD ta samar da wani kuduri dangane da rikicin da ke faruwa a gabas ta tsakiya. A dai-dai lokacinda aka kara yawan tashe-tashen hankula a kasar Falasdinu da aka mamaye tsakanin HKI da kuma Falasdinawa masu gwagwarmaya. Kungiyar kasashe masu musulmi mafi rinjaye wato OIC ta yanke shawara kan cewa bai kamata kasashen su samar da huldar Diblomasiyya da HKI ba. Ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Pakisatn ta bayyana cewa, kafafen yada labarai da dama sun watsa labaran cewa kasar ta Canza matsayinta dangane da kudurin hukumar kare hakkin bil’adama ta MDD dangane da rikicin nag abas ta tsakiya, ta kuma kara da cewa wannan labarin ba gaskiya bane. Saboda kasar Pakistan tana tare da kungiyar OIC dangane da goyon bayan al-ummar Falasdinu. Don haka Pakisatan bata amincea da samuwar HKI ba. Har’ila yau majalisar kasa ta kasar Pakisatn ta amince da babban rinjaye ko kuma gaba dayan yan majalisar da rashin amincea da HKI da kuma goyon bayan Falasdinawa.