Muna Ganin Kashe-kashe Ta Ko’ina – ‘Yan Gudun Hijirar Sudan
Published: 20th, April 2025 GMT
Labarin harin na zuwa ne kwana daya kafin cika shekara biyu da fara yakin basasar na Sudan tsakanin RSF da rundunar sojin kasar.
Da yake magana da BBC a safiyar Lahadi, wani mazaunin Zamzam da ke aiki da wata cibiyar da ke tallafa wa mutane da abinci ya ce an kashe “matasa da yawa”.
“An kashe masu aiki a cibiyar, haka ma an kashe likitocin da ke aikin kula da lafiya a cibiyar,” a cewar Mustafa mai shekara 34 cikin wani sakon murya ta WhatsApp.
“An kashe kawuna da dan dan’uwana. An raunata mutane kuma babu magani ko asibitin da zai kula da su – suna mutuwa saboda zubar jini.
“Har yanzu ana ci gaba kawo hari, kuma muna tunanin za a ci gaba da yin hakan har zuwa safiya.”
Ya kara da cewa an rufe dukkan hanyoyin fita daga sansanin “kuma dakaru sun zagaye duka bangarori hudu”.
Wani mutum mai suna Wasir ya ce “babu komai da ya rage a Zamzam”.
“Fararen hula masu yawa sun gudu, mu ma muna kokarin tafiya amma ba mu yi nasara ba, an rufe duka titunan, ga kuma yara a tare da mu.
Mutuwa ta ko’ina. Yanzu da nake magana da ku daga cikin wani rami, ana ta luguden wuta.”
Wasu daga cikin mazauna sansanin sun samu tserewa kuma suka yi tafiyar kilomita kamar 15 zuwa el-Fasher, a cewar Ministan Lafiya na Arewacin Darfur Ibrahim Khater.
“Na ga mutane da yawa suna barin Zamzam da kafa – akasarinsu yara, da mata, da tsofaffi,” in ji shi.
“An raunata wasu, wasu agajiye bayan an kashe ‘yan’uwansu. Lamarin ya ta’azzara.”
Jagorar tattara kayan agaji na Majalisar Dinkin Duniya a Sudan, Clementine Nkweta-Salami, ta ce “ta kadu sosai” da jin rahotonnin da ke fitowa daga Darfur.
“Wannan na nuna irin yadda ake tsananta hare-haren rashin imani kan mutanen da aka kora daga muhallansu da masu aikin agaji,” a cewarta cikin wata sanarwa.
Ita ma ma’aikatar harkokin Amurka ta yi “tir da rahotonnin hare-haren da RSF ta kai a Zamzam da kuma Abu Shouk”, tana cewa: “Muna yin Allah wadai da hare-haren RSF kan fararen hula marasa karfi.”
Kungiyar bayar da agaji ta Relief Organization ta ce ma’aikatanta tara “aka yi wa kisan rashin imani cikinsu har da likitoci, da direbobi, da wani jagoran tawaga” a harin da aka kai a Zamzam.
Kungiyar, wadda ta ce ita kadai ta rage da ke aikin kula da lafiya a sansanin, ta zargi RSF da aikata laifukan.
“Mun fahimci cewa wadannan hare-hare ne da gangan kan cibiyoyin lafiya a yankin domin hana ‘yan gudun hijira samun magani.
“Muna cikin zulumi ganin yadda aka hari daya daga cikin cibiyarmu da sauran cibiyoyin lafiya a el-Fasher.”
Kashif Shafikue, shugaban kungiyar, ya fada wa BBC cewa abin da ya faru da gangan aka aikata shi.
Kamar yadda wata ma’aikaciyar lafiya da ta tsira ta bayyana masa, ya ce mayakan RSF sun shiga wata maboyar mutane suka harbe mutum tara a ka da kuma kirjinsu.
CIkin wata sanarwa a ranar Asabar, RSF ta ce ba ita ce ta kai hare-hare kan fararen hular ba, kuma wai an shirya hare-haren ne domin a shafa mata kashin kaji.
Kwana daya bayan haka ne kuma ta ce “ta yi nasarar ‘yanta” sansanin daga hannun dakarun Sudan.
RSF ta zargi sojojin kasar da yin amfani da Zamzam “a matsayin sansanonin soji da kuma fararen hula a matsayin garkuwa”.
Wata tawagar kwararru a jami’ar Yale da ke Amurka ta ce hotunan tauraron dan’Adam da ta nazarta sun nuna “harin ya zama mafi muni da aka kai ta kasa a kan Zamzam…tun bayan fara yakin a el-Fasher cikin shekarar 2024”.
Ta ce ta lura da yadda “hare-haren amfani da wuta suka kona gine-gine da wurare da yawa a tsakiya, da kudanci, da kudu maso gabashin sansanin”.
Yakin da ake yi domin kwatar iko tsakanin RSF da sojin gwamnatin Sudan, ya jawo bala’i mafi girma a duniya a kan al’umma, inda ya tilasta wa sama da mutum miliyan 12 barin gudajensu da kuma jefa su cikin yunwa.
An fara gwabzawa a ranar 15 ga watan Afrilun 2023 bayan shugaban RSF da shugaban Sudan sun samu sabani game da makomar kasar.
El-Fasher ne gari mafi girma a yankin Darfur da ke karkashin ikon sojoji, wanda RSF suka kewaye tsawon shekara daya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Gudun hijira
এছাড়াও পড়ুন:
’Yan sanda sun ceto ɗalibai 10 sun lashe ɗan bindiga a Edo
Jami’an rundunar ’yan sandan jihar Edo sun ceto ɗalibai 10 da wasu ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a jihar Edo.
An kashe ɗaya daga cikin ’yan bindigan, a yayin musayar wuta da ’yan sanda a lokacin aikin ceto, yayin da sauran suka tsere da raunukan harbi.
Daily Trust ta ruwaito cewa an yi garkuwa da ɗaliban ne a ranar 16 ga Afrilu, 2025, a kan hanyarsu ta zuwa Jami’ar Babcock don taron shekara-shekara na GYC Africa.
Kakakin rundunar, SP Kontongs Bello, wanda ya tabbatar da ceton, ya ce da samu rahoton sace daliban, kwamishinan ’yan sandan jihar, Funsho Adegboye, ya tura ’yan sanda na musamman tare da ’yan banga da maharba cikin daji domin ceto su da kuma kama waɗanda ake zargi.
Ana kashe ’yan Najeriya amma Tinubu ya fi damuwa da Zaɓen 2027 — SDP Makarantar Bare: Shekara 20 dalibai na karatu a matsanancin yanayiYa ce a lokacin aikin, an kashe ɗaya daga cikin ’yan garkuwan, yayin da sauran suka tsere da raunukan harsashi.
“Jami’an sun yi taka-tsan-tsan don guje wa asarar rayukan fararen hula saboda ’yan garkuwan sun yi amfani da waɗanda aka sace a matsayin garkuwa.”
A cewarsa, wani Sufeton ɗan sanda ya samu raunin harbin bindiga a lokacin aikin, kuma yana samun kulawa a asibiti a halin yanzu.
Ya ce ana ci gaba da ƙoƙarin cafke ‘yan garkuwan da suka tsere.