Mayaƙan ISWAP sun tarwatsa gada a Yobe
Published: 20th, April 2025 GMT
’Yan ta’addar ISWAP sun tarwatsa wata gada da ta haɗa garin Ngirbuwa da garin Goneri a Ƙaramar Hukumar Gujiba da ke Jihar Yobe.
Wannan na zuwa ne ƙasa da mako guda da ‘yan ta’addan suka lalata gadar nan ta Mandafuna da ta haɗa garin Biu da Damboa a Jihar Borno.
JAMB ta sauya ranar soma jarrabawar bana Manyan jami’an gwamnati sun halarci auren ’yar tsohon Gwamnan BauchiMajiyar leƙen asiri ta shaida wa Zagazola Makama cewa harin ya afku ne da misalin ƙarfe 10:30 na daren ranar ranar Alhamis ɗin da ta gabata, ta hanyar amfani da wani bam wajen lalata sauran sassan gadar.
Wannan aikin ta’addanci ya kawo cikas ga zirga-zirga tsakanin al’ummomin biyu da ma sauran al’ummomin yankin, lura da cewar gadar na kan hanyar Katarko ne zuwa garin Goneri.
Masana tsaro na nuna cewar, lalata wannan gadar mota na iya kawo cikas ga harkokin tsaro a wannan yanki, lura da cewar yankin na da iyaka da wasu dazuzzukan da ke da iyaka da dajin Sambisa da ya zama maɓoyar ‘yan ta’addan a wasu ɓangarorin.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: ISWAP Jihar Yobe
এছাড়াও পড়ুন:
Matar gwamna ta ɗauki nauyin ragon suna da hidimar duk matar da ta haifi ’yan uku a Sakkwato
Uwargidan Gwamnan Sakkwato Hajiya Fatima Ahmad Aliyu ta ɗauki nauyin ragon suna da abinci da kayan barka ga duk wata mata da tahaifi ’yan uku a jihar.
Hahiya Fatima ta sanar da haka ne a ranar Laraba nan a lokacin da ta yi takakkiya takanas zuwa garin Ƙaurar Yabo da ke Ƙaramar Hukumar Yabo domin kai ragunan suna da kayan barka da na suna ga wata mai jego mai suna Malama Bela’u, wadda ta haifi ’yan uku a garin.
Daga cikin kayan da ta kai wa mai jego kyauta, har da buhun abinci goma da akwatunan tufafi da tsabar kudi Naira dubu dari biyar.
A bayanin da mataimaka wa gwamna kan harkokin kafofin sada zumunta, Nasir Bazza, ya fitar, ya ce mutanen ƙauyen sun yi farin cikin ganin matar gwamna a garin, wanda shi ne karo na farko da suka ga matar gwamna a yankin nasu.
Ya ce matar gwamna ta yi alkawalin ci gaba da bayar da irin wannan tallafi ga duk wata mata da Allah ya albrkace ta da samun karuwar ’yan uku a lokaci guda a jihar.