Amurka : Ana ci gaba da zanga-zangar kyamar tsare -tsare da manufofin gwamnatin Trump
Published: 20th, April 2025 GMT
Ana sake gudanar da manyan zanga-zanga a manyan biranen Amurka a kan nuna adawa da tsare -tsare da manufofin gwamnatin Donald Trump.
Masu zanga-zangar na zargin gwamnatin da keta haddin kundin tsarin mulki da ‘yancin jama’a.
Wannan shi ne karo na biyu a wannan wata da dubban mutane suka yi tattaki a titunan Amurka domin nuna bacin ransu kan yadda Trump ke gudanar da mulkin kasar.
Korafe-korafen masu zanga-zangar sun hada da korar baki daga kasar da korar ma’aikata da gwamnati ke yi da kuma zargin tauye ‘yancin fadin albarkacin baki.
Kazalika masu zanga-zangar na nuna fishi kan irin ikon da Trump ya bai wa Elon Musk, attajirin duniya mai kamfanin Tesla – wanda ya kori ma’aikatan gwamnati sama da dubu 200, ya kuma rushe hukumomin agaji na Amurka da dama a duniya.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: zanga zangar
এছাড়াও পড়ুন:
Dalilai 12 Da Ke Nuna Malaman Makaranta Na Da Muhimmanci Ga Al’umma (2)
Bada shawara kan abinda ko abubuwan da su daliban suke bukatar zama da babban burin ko wane daga cikinsu,da yadda za su cimma burin abinda suke son zama a gaba.
Bada taimakon lokacin da ake fuskantar matsalolin rayuwa da kuma karatu.
Yin kwatance da Malamin makarnta wajen koyi da abubuwan da aka ga yana yi,irin hakan na karawa dalibai kwarin gwiwa, wajen daukar mataki kan irin abinda ya dace su yi,na taimaka masu daukar mataki daukar mataki na irin burin da suke bukatar cimmawa akan ilimi.
Samar da hanyar tafiya tare da kowa
Samar da hanyar da kowane dalibi zai gane tafiyar tare da shi ake yin ta,wannan ma wani abu ne da yake nuna babu wani bambanci kan yadda ake koyar da su daliban.
Sanya wadansu abubuwan da za su ja hankali cikin dabarun koyar da darussa.
Tabbatar da cewa kowane dalibi ya gane an dauke shi muhimmanci,ba tareda yin la’akari da yadda yake ba.
A yi maganin duk wata matsalar da ta taso hakan yana bada dama ganin darajar kowa da fahimtar juna.
Tafiya tare da kowae dalibi a aji hakan na taimaka masu wajen yadda za su fuskanci yin mu’amala da mutane daban- daban na sassan duniya.
Yin mu’amala kamar yadda ya dace tsaanin dalibai da Malamin makaranta hakan na tabbatar da cewa kowa ya san irin halin da ake ciki,da kuma irin taimako mai gamsarwa da dadadawar za a ba dalibi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp