Faransa : An kama wata ‘yar Iran mai goyon bayan Falasdinu
Published: 20th, April 2025 GMT
A faransa ana ci gaba da tsare wata ‘yar Iran mai goyan bayan Falasdinu, bis azarginta da iza ta’addanci.
Mahdieh Esfandiari (mai shekaru 35) ana tsare da ita tun ranar 28 ga watan Fabrairu, bayan kama ta a binrin Lyon, inda ta ke da zama.
Iran ta bakin kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar, Esmail Baghai, ya yi Allah wadai da kama Mahdieh Esfandiari, yana mai yin Allah wadai da “manufofin kasashen Turai” wanda “ya kunshi murde adawa da “kisan kare dangi” da Isra’ila ta yi a Gaza.
Ya kara da cewa ba a sanar da ofishin jakadancin Iran da ke birnin Paris da kuma iyalan yarinyar ba.
A nasa bangaren, lauyan Mahdieh Esfandiari, Nabil Boudi, ya nuna rashin jin dadinsa kan kamun da aka yi wa wadda yake karewa.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
An kama matashi da kawunan mutanen a Legas
Rundunar ’yan sandan Jihar Legas ta cafke wani mutum mai suna Samson Oghenebreme a unguwar Odomola ɗauke da kawunan mutane.
Sanarwar da kakakin ’yan sandan Legas, Benjamin Hundeyin ya fitar, ta ce an kai kawunan da aka gano asibiti a Epe, yayin da ake ci gaba da bincike kan lamarin.
Indiya da Pakistan sun cimma yarjejeniyar tsagaita wuta Matsalar Tsaro: Zulum ya haramta sayar da man fetur a BamaAn kama matashin ne ɗan shekara 25 bayan da jami’an bijilanti da ke sintiri a yankin suka sanar da jami’an tsaro cewa ba su yadda da take-takensa ba.
Gidan Talabijin na Channels ya ruwaito cewa ’yan sandan sun yi zargin cewa matashin yana kai kawunan Jihar Edo wajen wani boka — wanda yake amfani da su don yin kuɗi.
Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Olohundare Jimoh ya yaba wa jami’an ’yan sanda da na bijilanti kan ɗaukar matakin da ya dace da sauri.
Ya kuma buƙaci duk mazauna jihar da su riƙa sa ido da kai rahoton abin da ba su yarda da shi ba zuwa ga ofishin ’yan sanda mafi kusa.