Sojojin Lebanon Sun Kama Wasu Mutanen Da Suke Shirin Cilla Makamai Kan HKI
Published: 20th, April 2025 GMT
Majiyar labarai daga kasar Lebanon sun bada sanarwa kama wasu mutane wadanda suke shirin Cilla Makamai kan HKI.
Jaridar Arab News ta yanar gizo ta kuma kasar Saudiya ta bayyana cewa a makon da ya gabata ma an kama wasu mutane wadanda ake zargi da cilla makaman roka kan HKI daga kudancin kasar ta Lebanon.
Amma dangane da kwance damarar kungiyar Hizbullah kuma shugaban kasar Lebanon Jesept Aun ya ce wannan al-amarin ba abu ne mai sauki ba, sai dai a jira lokacinda ya dace na yin hakan. Aun ya kara da cewa duk wani kokari na kwance damarar kungiyar hizbullah kawo karshen zaman lafiya a kasar Lebanon ne.
Kafin haka dai shugaban kungiyar Hizbullah Sheikh Na’im Kasim a jawabin da ya gabatar a ranar Jumma’a ya bayyana cewa ba wanda ya ida ya kwace, makaman kungiyar amma kungiyar zata iya tattainawa don kyautata tsaron kasar Lebanon tare da sauran jami’an tsaron kasar.
Wasu masana suna ganin da alamun wasu jami’an gwamnatin kasar Lebanon sun zama wakilan HKI da Amurka a kasar. Musamman ganin yadda HKI ta kai hare-hare har sau 2700 bayan tsagaita bude wuta da kungiyar Hizbulla, ba zakat aba jin wani yayi magana a kansa ba, amma suna maganar kwance damarar kungiyar ta Hizbullah.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: kasar Lebanon
এছাড়াও পড়ুন:
Sojojin Kasar Yemen Sun Kai Hare Hare Kan HKI Da Jiragen Yakin Amurka
Sojojin kasar Yemen sun bada sanarwan cilla makamai masu linzami kan birnin Telaviv da kuma kan jirgin yakin Amurka saboda tallafawa falasdinawa a Gaza, da kuma maida martani kan hare-haren Amurka kan kasar a jiya Alhamis.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kakakin sojojin kasar na Yemen Burgediya Janar Yahayah Saree yana fadar haka a yau Jumma’a ya kuma kara da cewa sojojin kasar ta yemen sun cilla makami mai linzami samfurin Zulfikar kan wani sansanin sojojin HKI a kusa da tashar jiragen sama na Bengerion dake birnin Yafa (telaviv.
Saree ya kara da cewa sojojin, har’ila yau sun kai wasu hare-hare kan jiragen yaki masu daukar jiragen saman yaki na Amurka Harry Truman da kuma USS carl awadanda suke tekun red sea da kuma wani jirgin yakin mai rakiyarsu.
Kakakin sojojin kasar ta Yemen yace wannan shi ne karon farko wanda sojojin kasar suka kaiwa jirgin ruwa mai daukar jiragen saman yaki mai suna USS carl, wanda ya shiga yakin daga baya-bayan nan,
Sannan ya kammala da cewa samuwar sojojin Amurka a yankin ba abinda zai amfana in banda kara rikicewar yankin gabasa ta tsakiya.