Bikin Easter : Paparoma Francis ya yi kira da a tsagaita wuta a Gaza
Published: 21st, April 2025 GMT
Shugaban mabiya darikar Katolika na duniya Fafaroma Francis, ya yi kira da a tsagaita wuta a Gaza.
A cikin sakonsa na bikin Easter, Paparoma ya yi tir da halin da ake ciki na jin kai a Gaza tare da yin kira da a tsagaita wuta.
Paparoma Francis ya halarci bukukuwan Ista a wannan Lahadi, inda ya yi tir da halin da ake ciki na jin kai mai daukan hankali a Gaza.
“Ina kira ga bagarorin da su tsagaita wuta, a saki wadanda aka yi garkuwa da su, a kuma kai kayan agaji ga al’ummar falasdinu da kuma fatan samun zaman lafiya a nan gaba,” in ji shi a cikin sakonsa, wanda wani na hanun damansa ya karanto daga cocin St. Peter’s Basilica dake binrin Rome.
Jawabin nasa wani bangare ne na bikin Easter kamar yakke ake a ko wacce shekara, saidai fafaroman bai samu karanto jawabinba sabo lalurar ta rashin lafiya da yake fama da ita.
Mabiya addinin Kirisita a fadin duniya kan gudanar da bukukuwan Easter duk shekara domin tunawa da gicciyewa da kuma tashin Yesu Almasihu daga cikin matattu.
Bikin dai a kan fara shi ne tun daga dare irin na Alhamis zuwa wayewar garin Juma’a a kuma kammala a ranar Litinin.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Paparoma Frasncis ya rasu yana da shekaru 88
Allah Ya yi wa Shugaban mabiya ɗarikar Katolika na duniya, Paparoma Frasncis, rasuwa yana da shekaru 88.
Fadar Vatican ce ta sanar da rasuwar Paparoma Francis a safiyar Litinin a yayin da al’ummar Kirista na duniya ke bikin Ista.
Ya mutu ne washegari da ya fito bainar jama’a Dandalin St Peter’s, domin taya Kiristoci murnar zagayowar ranar Ista.
A watan da ya gabata ne aka sallame daga asibiti bayan ya yi jinya na tsawon makonni biyar.
Shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron shi ne na farko wajen mika sakon ta’aziyya a cikin shugabannin duniya.