New York Times : Amurka na son rage ofisoshin jakadncinta a Afirka
Published: 21st, April 2025 GMT
Wani rahoto da jaridar New York Times ta Amurka ta fitar ya nuna cewa Amurka na neman rage kasantuwarta a duk duniya musamman a Afirka.
Jaridar ta bayyana wani daftarin dokar shugaban kasa na sirri wanda ya tanadi “sake tsara tsarin ma’aikatar harkokin wajen Amurka.
Sai dai ministan harkokin wajen kasar Marco Rubio, ya musanta wadannan shirye-shiryen.
Batu na farko na shirin sake fasalin ma’aikatar harkokin wajen Amurka shi ne rage ofisoshin ma’aikatar harkokin wajen Amurka a bangaren sauyin yanayi, dimokuradiyya, da kare hakkin bil’adama, batutuwan da gwamnatin Trump ta shiga kafar wando guda dasu.
Rahoton ya ce rage kasafin kudin zai kai ga rufe ofisoshin jakadanci a kasashen waje, amma inda Amurka za ta rage yawan aikin diflomasiyya shi ne a Afirka.
Domin Washington ta yi imanin cewa akwai yankuna hudu kawai a duniya inda kasancewarta zai kasance mai mahimmanci: Eurasia, Gabas ta Tsakiya, Latin Amurka da Asiya-Pacific.
Don haka Afirka Amurka za ta samar da jakada na musamman kan harkokin Afirka.” wanda zai kai rahoto ga Majalisar Tsaro ta Fadar White House, ba Ma’aikatar Harkokin Wajen ba.
Kudirin ya kuma bayyana cewa “za a rufe dukkan ofisoshin jakadanci da karamin ofishin jakadancin da ba su da mahimmanci a yankin Saharar Afirka.” A ƙarshe, duk sauran ayyukan da suka rage za a hada su karkashin ikon manzo na musamman.
An shirya aiwatar da wadannan sauye-sauye a ranar 1 ga Oktoba, a cewar jaridar.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: aikatar harkokin wajen
এছাড়াও পড়ুন:
Ma’aikatar Kasuwancin Sin: Dole Ne Amurka Ta Daina Dora Laifi Kan Sauran Kasashe
Kazalika, ya ce, Sin za ta ci gaba da mai da hankali kan matakan da Amurka za ta dauka, kana za ta dauka matakin mai da martani don kare muradunta idan hakan ya wajaba. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp