HausaTv:
2025-04-21@10:07:15 GMT

Wani Harin Amurka kan Yemen ya kashe fararen hula akalla 12

Published: 21st, April 2025 GMT

Amurka ta sake kai wani hari ta sama kan babban birnin kasar Yemen, Sana’a, inda ta kashe fararen hula akalla 12 tare da jikkata wasu fiye da 30 na daban.

Mummunan harin na Amurka an kai shi ne a wata kasuwa mai cike da cunkoson jama’a a unguwar al-Farwa da ke gundumar Sha’ub a safiyar ranar Litinin.

Ana fargabar adadin wadanda suka mutu zai karu yayin da mutane da dama ke makale a karkashin baraguzan gine-gine da aka wargaza a harin.

A gefe guda kuma, Amurka ta kai hare-hare a yankunan lardin Sa’ada, a arewa mai nisa na kasar, da tsakiyar Ma’rib, da yammacin Hudaydah.

Dama kafin hakan a ranar Lahadi, Amurka ta kai wasu hare-hare ta sama a Yemen, ciki har da Sana’a, inda aka kashe akalla uku.

A cikin watan da ya gabata ne dai sojojin Amurka suka zazafa kai hare-hare a kasar Yemen, bisa ikirarin dakile hare-haren kungiyar Ansarullah dake kai farmakin goya bayan falasdinu kan jiragen ruwa masu alaka da Isra’ila.

Fiye da mutane 200 ne aka kashe a harin da Amurka ta kai kan Yemen tun cikin watan Maris.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Dakarun Gwagwarmayar Yemen Sun Kai Hare-Haren Daukan Fansa Kan Haramtacciyar Kasar Isra’ila

Dakarun gwagwarmayar Yemen sun kaddamar da hare-haren daukan fansa kan yankin Jaffa da ke kusa da birnin Tel Aviv na Isra’ila

Dakarun gwagwarmayar Yemen sun sanar da aiwatar da wasu matakan soji masu inganci kan yankin Jaffa da aka mamaye, da kuma kan jiragen ruwan Amurka masu dauke da jiragen saman yaki na Truman da Vinson, gami da harbo jirgin sama kiran MQ-9.

Dakarun gwagwarmayar sun bayyana a cikin wata sanarwa da Birgediya Janar Yahya Sar’ie ya bayyana a tsakanin miliyoyin mutane a dandalin Al-Sabeen a ranar Juma’a cewa: Sun kai wani harin soji a kusa da filin jirgin saman Ben Gurion a yankin Jaffa da aka mamaye da makami mai linzami na “Zulfiqar”. Dakarun kasar ta Yemen sun tabbatar da cewa suna ci gaba da gudanar da mummunan arangama a tsawon kusan watanni biyu da kuma kalubalantar hare-haren da Amurka ke kaiwa kasar Yemen a matakin mayar da martani da kalubalantar hare-haren wuce gona da iri kan kasarsu.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Najeriya : Mutum 56 suka mutu a harin Benue
  • Yeman : Sojojin Amurka sun kai wani gagarumin farmaki kan lardunan Sanaa da Hudaidah
  • Ma’aikatar Lafiya Ta Yemen Ta Sanar Da Yawan Mutanen Da Suka Yi Shahada A Hare-Haren Amurka Kan Kasar
  • Amurka Ta Kaddamar Da Sabbin Hare-Hare Kan Garuruwan Sana’a, Sa’adah Da Al-Jawf Na Kasar Yemen
  • Dakarun Gwagwarmayar Yemen Sun Kai Hare-Haren Daukan Fansa Kan Haramtacciyar Kasar Isra’ila
  • Iran ta yi tir da kakkausar murya da harin Amurka kan tashar mai ta Yemen
  • Yawan Mutanen Da Suka Yi Shahada A Harin Amurka Na Jiya A Yemen Ya Kai 74
  • An kashe sojoji, fararen hula da dama a Borno
  • Amurka Ta Kashe Mutane 38 Tare Da Jikkata Fiye Da 100 A Harin Da Ta Kai Lardin Al-Hudaidah Na Yemen