Yadda ma’aikatan gidan ruwa 4 suka mutu a Bauchi
Published: 21st, April 2025 GMT
Ma’aikatan Hukumar Samar da Ruwan Sha ta Jihar Bauchi guda huɗu sun rasu a yayin da suke aikin tsabtace madatsar ruwa ta Gubi.
Wasu jami’ai da ke aiki a Madatsar Ruwa ta Gubi, sun bayyana cewa daga cikin mamatan har da wani uba da dansa da kuma wani wanda ke shirye-shiryen ɗaurin aurensa.
“Abin ya faru ne a lokacin da suke aikin tsaftace ruwan da ake kula da ruwan da ake yi wa babban birnin Bauchi.
“Ana cikin haka, wani abokin aikinsa da ya ga abin da ya faru ya yi ƙoƙarin ceto shi, shi ma ya mutu, kuma anyi musu jana’iza kamar yadda addinin Musulunci ta tanada,” kamar yadda wani abokin aikinsu ya bayyana.
Ambaliya ta kashe mutum 3 ta lalata hekta 10,000 na shinkafa a Neja Ango ya tsere tare da surukarsa Gobara ta ƙone gidaje sama da 100 a sansanin ’yan gudun hijira a BornoKakakin Rundunar ’Yan Sanda a Jihar Bauchi, CSP Mohammed Ahmed Wakil ya ce ma’aikatam da suka rasu sun hada Shayibu Hamza mai shekaru 48 da Abdulmalik Yahya mai shekaru 29 da Jamilu Inusa mai shekaru 29 da kuma Ibrahim Musa mai shekaru 42.
Ya ci gaba da cewa lamari mai ban tausayi ya auku a madatsar ruwa ta Gubi, wanda ya yi sanadin asarar ma’aikatan da suka sadaukar da kansu a yayin wani aikin yashe shara da ke cikin ramuka a madatsar ruwan ta Gubi.
Ya ce A lokacin da waƙi’ar ta auku, an yi ƙoƙarin ceto su, aka fito da su a sume daga cikin ramin tara ruwan da suke aikin, daga nan aka garzaya da su Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Ɓalewa da ke Bauchi, amma duk da kulawar gaggawa da aka ba su, sai Allah Ya karɓe su, likitoci suka tabbatar da rasuwarsu.
Wakil ya ce, a lokacin da ’yan sanda suka samu labarin faruwar lamarin, sun tura jami’ai zuwa wurin, yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike don gano ainihin abin da ya faru.
Ya ce akwai buqatar qara daukan matakai a vangaren kula da ruwa, yana mai jaddada muhimmancin dukkan ma’aikatan su kula da bin ƙa’idojin aminci da aka kafa don rage haɗari nan gaba.
Duk ƙoƙarin da muka yi na jin ta bakin Kwamishinan Albarkatun Ruwa ma Jihar Bauchi, Abdulrazaq Nuhu Zaki, da Babban Manajan Kamfanin Samar da Ruwan Sha na Jihar Bauchi, Injiniya Aminu Aliyu Gital, a game da lamarin ya ci tura.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Madatsar Ruwa a Jihar Bauchi mai shekaru
এছাড়াও পড়ুন:
An kashe sojoji, fararen hula da dama a Borno
Wasu ’yan ta’adda da ake kyautata zaton ’yan Boko Haram ne sun kai hari a sabuwar unguwar Yamtake da ke Ƙaramar hukumar Gwoza a Jihar Borno, inda suka kashe sojoji biyu tare da wasu fararen hula da ba a bayyana adadinsu ba.
Majiyoyin tsaro da na cikin gida sun tabbatar da harin, inda suka ce maharan sun mamaye unguwannin ne da misalin ƙarfe 11:15 na daren Alhamis.
Gwamnatin Yobe ta sayo hatsi don tunkarar kakar bana Matan da suka tsira daga Boko Haram na buƙatar tallafin musammanƊaya daga cikin majiyar sojojin ta ce, kafin a aike da wata tawagar sojoji daga Gwoza, maharan sun riga sun afkawa jama’a da sansanin sojan Yamtake.
“Muna jiran tawagar masu ƙarfafa musu su dawo, amma mun sami labarin cewa mutane biyu daga cikin jami’anmu da wasu fararen hula harin ya shafe su. Ina ba da shawarar mu jira har sai sun dawo,” in ji shi.
Sai dai Sanata Ali Ndume, ya ce tun lokacin da lamarin ya faru yana tuntuɓar al’ummar unguwar Yamtake.
“Abin takaici ne cewa mutanenmu a ƙauyen Yamtake sun fuskanci mummunan harin Boko Haram a daren ranar Alhamis, ɗaya ne daga cikin unguwannin da suka karɓi ’yan gudun hijirar kwanan nan, gwamnatin Jihar Borno ta sake tsugunar da su.
“Abin baƙin ciki ne yadda sojoji biyu suka rasa ransu a bakin aiki, yayin da wasu fararen hula da ba a san ko su wanene ba na daga cikin waɗanda suka jikkata, Allah Ya gafarta musu.
“Amma kuma na yabawa Birgediya Janar Nasir Abdullahi, Birgediya Kwamanda na runduna ta 26 Task Force da jiga-jigan sojojinsa kan sadaukarwar da suka yi ba tare da ƙaƙƙautawa ba wajen daƙile hare-hare da dama, musamman waɗanda aka yi yunƙurin kaiwa farmakin a garin Gwoza.