NAJERIYA A YAU: Me ya sa matsalar tsaro “ta gagari gwamnati” a Najeriya?
Published: 21st, April 2025 GMT
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
A daidai lokacin da ake tunanin samun sauƙi daga tarin matsalolin tsaro da na tada ƙayar baya a Najeriya, sai ga wasu sabbin matsalolin na ƙara kunno kai.
Yayin da a wannan lokaci ake fuskantar hare-haren da ake zargin na ƙungiyar Boko Haram ne a Arewa maso Gabas, da kuma sabbin kashe-kashe a sassan jihohin Filato da Binuwai, sai kuma ga wata sabuwar ƙungiya da ake zargin ta ’yan ta’adda ce mai suna Mahmuda ta ɓulla a Jihar Kwara.
To ko mene ne ya haddasa wannan koma-baya ta fuskar tsaro?
Shin a ganinku, me ya sa matsalar tsaro “ta gagari gwamnatin” Najeriya?
NAJERIYA A YAU: Sabbin dabarun hana matasa aikata laifi DAGA LARABA: Dalilan Ɓaraka A Tsakanin Iyayen Riƙo Da Ƴaƴan RiƙoShirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan dalilan ƙara ƙazancewar matsalar tsaro da hanyoyin magance su a Najeriya.
Domin sauke shirin, latsa nan
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Binuwai matsalar tsaro
এছাড়াও পড়ুন:
Tawagar Gwamnati Ta Kai Ziyara Filato, Ta Sha Alwashin Kawo Karshen Kashe-kashe A Jihar
“Mun zo nan ne a madadin gwamnatin tarayya domin ganowa da kuma jajanta muku rashin da aka yi, muna so mu tabbatar muku da cewa jami’an tsaro za su kawo karshen wannan kashe-kashen na rashin hankali.
“An yi mini cikakken bayani, kuma ina so in tabbatar muku cewa mun fahimci tushen wannan batu. Zamu kama wadanda suka aikata wannan aika-aika.
“Shugaban kasa ya damu matuka, kuma ya umarce mu da mu nemo wadanda suka aikata wannan aika-aika domin su fuskanci shari’a, muna aiki tare da gwamnatin jihar domin daukar tsarin da zai hana faruwar wannan mummunan lamari, lokaci ya yi da za a kawo karshen wannan hauka,” inji shi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp