Kakakin Ma’aikatar Wajen Iran Ya Jaddada Cewa: Babban Abin Da Suke Bukata Shi Ne Daga Takunkumi
Published: 21st, April 2025 GMT
Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ya bayyana cewa: Babban abin da suke bukata a duk wata tattaunawa shi ne a dage takunkumi
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran, Isma’il Baqa’i, ya jaddada cewa babban bukatar Iran a duk wata tattaunawa ita ce a dage takunkumin da aka kakaba mata ta hanyar da za ta kai ga samun sakamako mai ma’ana.
Isma’il Baqa’i ya bayyana hakan ne a yayin taron manema labarai na mako-mako da yake yi a yau litinin cewa: A kwanakin baya ministan harkokin wajen kasar Iran ya ziyarci kasar Rasha, sannan ya gana da ministan harkokin wajen kasar Italiya, a gefen shawarwari ba na kai tsaye ba tsakanin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da Amurka.
Ya kara da cewa: A gobe ne ministan harkokin wajen kasar Iran zai kai ziyarar aiki zuwa kasar China. Ya kuma kara da cewa, ana ci gaba da samun wasu ci gaba a daidai wadannan ziyarce-ziyarcen, yana mai jaddada cewa idan aka yi tambayoyi a kansu a yayin taron tambayoyi da amsa, zai ba da cikakkun bayanai.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: harkokin wajen
এছাড়াও পড়ুন:
Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kaduna Ya Yi Bikin Easter Tare da Al’ummomin Kiristoci
Makera, Jihar Kaduna – Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, Rt. Hon. Yusuf Dahiru Liman, ya halarci bukukuwan Easter tare da al’ummomin Kiristoci na Gundumar Makera, inda ya bukaci su yi amfani da lokacin wajen tabbatar sa saƙon bangaskiya, yabo, da sadaukarwa da ke tattare da bikin.
A jawabin da ya gabatar, Hon. Liman ya jaddada muhimmancin bikin Easter a matsayin lokaci na sabunta dogaro da Allah. Ya kuma bukaci mabiya addinin Kirista da su rungumi koyarwar hakuri, kauna, da kuma fifita bukatun wasu akan nasu.
Kakakin ya kuma yi kira ga daukacin jama’ar Jihar Kaduna da su ci gaba da bunkasa zaman lafiya da juna ba tare da la’akari da bambancin addini, kabila ko ra’ayin siyasa ba, yana mai cewa hadin kai shi ne ginshikin ci gaban jihar da kasa baki daya. Ya jaddada bukatar gudanar da addu’o’i don dorewar zaman lafiya da inganta sha’anin tsaro.
A kokarinsa wajen inganta kiwon lafiya, Hon. Yusuf Dahiru Liman ya dauki nauyin mutane 200 da suka hada da tsofaffi da mabukata daga Kakuri-Gwari da unguwar Television domin shiga tsarin inshorar lafiya na KACHMA wanda ke ba da damar samun kulawar lafiya mai araha.
Baya ga hakan, Kakakin ya bayar da guraben karatu ga dalibai 200 daga wadannan al’ummomi domin tallafa musu a harkar ilimi da gina al’umma mai wayewa.
Bikin na Easter ya samu halartar shugabannin addini da sarakuna, shugabannin matasa da mata, da sauran manyan masu ruwa da tsaki na al’umma.
A nasa jawabin, Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kaduna, Mr. James Kanyip ya yabawa nasarorin da aka samu wajen karfafa tsaro da inganta zaman tare a jihar. Ya bayyana cewa gwamnati na amfani da hanyoyin sasantawa da tattaunawa wajen magance matsalolin tsaro, tare da kira ga jama’a da su kasance masu lura da kuma sanar da hukumomi duk wani abin da ba su amince da shi ba.
Shugabannin al’umma su ma sun yi amfani da damar wajen yabawa Kakakin bisa kokarinsa na kawo ci gaba. Mista Monday Kazah daga Kakuri-Gwari da Mista Ishaya Amfani daga unguwar Television sun jinjinawa Hon. Liman saboda shirye-shiryensa na tallafawa jama’a ta hanyar bayar da guraben karatu, koyar da sana’o’i, da samar da ayyukan yi. Sun kuma tabbatar masa da goyon baya da addu’o’i domin samar da dokokin da za su bunkasa rayuwar jama’a.
Shamsuddeen Mannir Atiku