Aminiya:
2025-04-21@15:18:59 GMT

Miji ya yi wa matarsa saki 3 a ofishin ’yan sanda

Published: 21st, April 2025 GMT

Wani magidanci ya ɗankara wa matarsa saki a ofishin ’yan sanda bayan an kama ta a wani otel.

Wani jami’in tsaro ya bayyana cewa an kama matar ce a yayin wani samame da ’yan sanda suka kai maɓoyar dillalan miyagun ƙwaya da ’yan sara-suka a wasu otel-otel a garin Minna.

Ya bayyana cewa sai bayan da aka kawo matar ofishin ’yan sanda, a yayin bincike suka gano cewa matar aure ce, bayan da suka tuntuɓi ’yan uwan mutanen da aka kama.

Ya ce, “Sakamakon yawaitar yadda matasa suke tayar da zaune tsaye ne mataimakin gwamna Kwamred Yakubu Garba, ya umarci jami’an tsaro su ɗauki mataki a kansu.

Yadda uba da ɗansa da wani ango suka rasu a bakin aiki a Bauchi Fafaroma Frasncis ya rasu yana da shekaru 88

“Shi ne muka kai samame, muka kama mutanen da ake zargi, cikinsu har da mata. Abin mamaki sai ga wani mutum ya zo, cewa ɗaya daga cikin matan da muka kama mai ɗakinsa ce,  kuma nan take ya yi mata saki uku.

“Ba mu san cewa matar aure ba ce, kuma ba mu da masaniyar abin da ya kai ta wurin, domin ’yan sanda ba su  kammala bincike ba lokacin da mutumin ya je ya ba ta takarda a ofishin ’yan sanda.”

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: ƙwayoyi matar aure

এছাড়াও পড়ুন:

Idan Shugaban Kasar Siriya Mai Ci Ya Taka Kasar Iraki Ana Iya Kama Shi

Shugaban kungiyar Asa’ib Ahl-Al-Hak, kungiya mai yaki da yan ta’adda a kasar Iraki, ya bayyana cewa idan shugaban kasar Siriya mai ci Abu Muhammad Al-Jolani ya kuskura ya taka kasar Iraki ana iya tsare shi sabuda gwamnatin kasar Iraki tana da sammashin kama shit un da dadewa.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ta nakalto shugaban kungiyar Qais Al-khazali yana fadar haka a shafinsa na X a jiya Asabar, ya kuma kara da cewa jita jitan da yake ji na cewa shugaban kasar ta siriya zai zo iraki a nan gaba, bai taso ba, lokacin zuwansa kasar Iraki bai yi ba saboda zarge-zargen da ake masa tun kafin ya kwace shugabancin kasar ta Siriya, akwai matsalolin doka sosai wadanda za’a fuskanta.

Khazali ya kara da cewa, kyautata dangantaka tsakanin kasashen biyu bai da wata matsala, kuma yana amfanar kasashen biyu, amma zuwansa kasar Iraki a nan kusa yana da  matsala, don tun shekara 2014 Jolani shi ne babban kwamnadan HTS, kuma dakarunsa sun yaki dakarunsa a yaki da suka yi da yan ta’adda a lokacin.

Yace bangaren shari’a na kasar Iraki yana cin gashin kansa ne, bangaren zartarwa ba zai hana bangaren shara’a aikinsa ba.

Kafin haka dai firai ministan kasar Iraki Muhammad Shia al-sudani ya hadu da Jolqni a kasar Qatar a cikin yan kwanakin da suka gabata a gaban sarkin Qatar Tamim bin ahli thani

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Idan Shugaban Kasar Siriya Mai Ci Ya Taka Kasar Iraki Ana Iya Kama Shi
  • Sojojin Lebanon Sun Kama Wasu Mutanen Da Suke Shirin Cilla Makamai Kan HKI
  • An Yi Mummunar Arangama Da ‘Yan Bindiga A Sakkwoto
  • NDLEA ta kama hodar iblis da aka ɓoye cikin littafai ana shirin kaiwa Saudiyya
  • Tashin Gobara A Kwale-Kwale Ya Lashe Rayukan Mutane 143 A Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango
  • ’Yan sanda sun ceto ɗalibai 10 sun kashe ɗan bindiga a Edo
  • An buɗe wa jami’an NDLEA wuta a Abuja
  • ’Yan sanda sun ceto ɗalibai 10 sun lashe ɗan bindiga a Edo
  • Ya kashe masoyin tsohuwar matarsa bayan sakinta a Neja