Abubuwan da suka sa Fafaroma Francis ya yi fice a duniya
Published: 21st, April 2025 GMT
Da safiyar wannan Litin fadar Vatican ta sanar cewa da misalin ƙarfe 7.35 Agogon Vatican Fafaroma Francis, wanda sunansa na asali Cardinal Jorge Mario Bergoglio, ya rasu a yayin da al’ummar Kirista na duniya ke bikin Ista.
Ya mutu ne washegari da ya fito bainar jama’a a Dandalin St Peter’s, domin taya Kiristoci murnar zagayowar ranar Ista.
Fafaroma Francis ya yi fama da doguwar jinya, inda a watan da ya gabata ne aka sallame daga asibiti bayan ya shafe makonni biyar can sakamakon cutar sanyin haƙarƙari mai tsanani.
Ga wasu abubuwa da Fafaroman ya yi fice a kansu:
1. Nuna adawa a fili ga wasu manufofin Donald Trump.Ya yi Allah wadai da yunƙurin Trump a mulkinsa na farko na gina katanga tsakanin Amurka da ƙasar Mexico, inda ya ce hakan ba ɗabi’ar Kiristoci ba ce.
Ya kuma yi Allah wadai da shirin maida baƙi ƙasashensu, da gwamnatin Trump ke ƙoƙarin yi a mulkinsa na biyu.
2. Sumbatar ƙafafuwan fursunoni.Fafaroma Francis ya wanke tafin ƙafafuwan wasu fursunonin gidan yarin Rome, tare da sunbata, abun da ya ja hankalin duniya.
3. Kira a magance matsalar sauyin yanayi.Fafaroma Francis ya zargi manyan ƙasashen duniya da ƙin ɗaukar matakan kare muhalli da sauyin yanayi, inda a 2023 ya ce wasu matsalolin ba za su taɓa gyaruwa ba.
4. Jawo masu ɗabi’ar auren jinsi a jiki.Duk da kakkausan suka da ya sha, wasu na ganin yana da ƙoƙarin jawo masu raunin imani a jiki, ciki kuwa har da yarda da ya yi ake sanya albarka ga auren jinsi.
5. Shi ne Fafaroma na 266, kuma na farko daga nahiyar Arewa da Kudancin Amurka.Asalin iyayensa ’yan Italiya ne, da suka yi ƙaura zuwa ƙasar Argentina. An haife shi a Buenos Aires, ranar 17 ga watan Disamba, 1936.
6. Kakkausar suka ga kamfanonin ƙera makamai.Ya yi kira ga ƙasashen duniya da su rungumi masalaha wajen magance rigingimu, gudun kada rikice-rikice su haifar da Yaƙin Duniya na 3.
7. Alaƙanta kwararar ’yan ci-rani zuwa Turai, da tauye ci-gaban ƙananan ƙasashe.Ziyararsa ta farko, Francis ya je tsibirin Lampedusa, yankin da ’yan ci-rani suke bi wajen shiga nahiyar Turai, inda ya ɗora laifi kan yadda ake tauye ci-gaban ƙananan ƙasashen duniya.
8. Yana son ƙwallon ƙafa da kuma waƙe-waƙe.Francis shi ne Fafaroma da yafi mu’amala da matasa, wajen sauraron su, da kuma ƙaunarsa da ƙwallon ƙafa.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Fafaroma Fafaroma Francis Fafaroma Francis ya
এছাড়াও পড়ুন:
Ma’aikata Sun Kauracewa Fareti, Sun Gudanar Da Taron Goyon Baya Ga Dakataccen Gwamnan Ribas
Ma’aikatan jihar Ribas sun hallara a sakatariyar kungiyar kwadago ta kasa, NLC da ke Fatakwal domin bikin ranar ma’aikata ta 2025 a ranar Alhamis. Dama kungiyar ta NLC, tuni ta sanar da cewa, ba za ta gudanar da bikin murnar ranar ma’aikata ba kamar yadda aka saba yi a filin shakatawa na Isaac Boro, inda a al’adance kungiyoyin kwadago daban-daban ke gudanar da tattaki a filin domin murnar wannan rana ta 1 ga watan Mayu. Gobara A Haramtacciyar Wurin Ajiye Man Fetur Ta Ci Rayukan Mutane 5 A Jihar Ribas Aikin Gina Tashar Jirgin Ƙasa A Kano Yana Ci Gaba Gadan-gadan A maimakon haka, ma’aikatan sun taru ne domin nuna goyon bayansu ga Gwamna Siminalayi Fubara da mataimakinsa da ‘yan majalisar dokokin jihar Ribas a sakatariyar kungiyar NLC ta jihar. In ba a manta ba, LEADERSHIP ta rahoto cewa, Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara da mataimakinsa da ‘yan majalisar dokokin jihar, inda ya mika jihar karkashin kulawar tsohon shugaban sojin Ruwa na Nijeriya. Dukkan kungiyoyin NLC a jihar, sun yi taro a sakatariyar da ke kan titin Igboukwu, D-Line, Fatakwal, inda suka bayyana rashin amincewarsu da abin da suka kira zagon kasa ga mulkin dimokradiyya a jihar Ribas. A halin da ake ciki, Gwamnan Jihar Ribas da aka dakatar, Sir Fubara ya yi kira da a ci gaba da kare hakkin ma’aikata a jihar. Fubara, ya yi wannan kiran ne a cikin sakon hadin kai da jinjinawa da ya bayar a Fatakwal, a daidai lokacin da al’ummar kasar ke bikin ranar ma’aikata ta bana.Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp