Aminiya:
2025-04-21@17:56:40 GMT

An jingine wasanni a Italiya saboda mutuwar Fafaroma Francis

Published: 21st, April 2025 GMT

Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Italiya, FIGC, ta sanar da jingine wasannin gasar gasannin Serie A, B, da C, saboda alhinin rasuwar shugaban ɗarikar Katolika, Fafaroma Francis.

Shugaban hukumar FIGC, Gabriel Gravina ya ce, “Harkar ƙwallon ƙafa ta Italiya tana taya jimami ga miliyoyin al’umma kan rasuwar Mai Alfarma Fafaroma Francis.

Ƙungiyoyin da dakatarwar ta shafa sun haɗa da Juventus, Lazio, Parma Calcio, Cagliari, Fiorentina, Genoa, Torino, Udinese.

A safiyar Litinin 21 ga Afrilu ne Fadar Cocin Katolika da ke Vatican City ta sanar da rasuwar Fafaroma Francis mai shekaru 88, wanda ke shugabantar Cocin, kuma shugaban birnin Vatican City.

Miliyoyin mutane a Italiya da kuma faɗin duniya sun shiga alhini saboda rasuwar malamin adinin.

Wannan ya sa aka ɗauki matakin jingine duka lamuran wasanni don nuna girmamawa ga rasuwar.

An soke duka wasannin da aka shirya bugawa ranar Litinin ta Easter, inda a babbar gasar Serie A ta Italiya, Juventus za ta kara da Parma, Lazio da Genoa, Torino da Udinese, Cagliari da Fiorentina.

Haka ma a ƙananan gasannin Italiya na Serie B da Serie C su ma an soke buga wasannin da aka tsara a baya.

Hukumar ta FIGC ta fitar da sabon jadawali da ke nuna cewa za a buga wasannin a ranar 23 ga wannan watan.

A halin yanzu dai galibi ƙungiyoyin suna da sauran wasanni biyar ne kafin kammala kakar gasanni ta bana.

Tarihi ya nuna cewa ko a 2005 da Fafaroma John Paul II ya rasu, an ɗauki irin wannan mataki.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Fafaroma Francis Italiya Wasanni Fafaroma Francis

এছাড়াও পড়ুন:

Fafaroma Frasncis ya rasu yana da shekaru 88

Allah Ya yi wa Shugaban mabiya ɗarikar Katolika na duniya, Fafaroma Frasncis, rasuwa yana da shekaru 88.

Fadar Vatican ce ta sanar da rasuwar Fafaroma Francis a safiyar Litinin a yayin da al’ummar Kirista na duniya ke bikin Ista.

Ya mutu ne washegari da ya fito bainar jama’a a Dandalin St Peter’s,  domin taya Kiristoci murnar zagayowar ranar Ista.

A watan da ya gabata ne aka sallame daga asibiti bayan ya yi jinya na tsawon makonni biyar.

Shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron shi ne na farko wajen mika sakon ta’aziyya a cikin shugabannin duniya.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Abubuwan da suka sa Fafaroma Francis ya yi fice a duniya
  • Fadar Vatican Ta Sanar Da Mutuwar Paparoma Francis A Safiyar Yau Litinin
  • Fafaroma Frasncis ya rasu yana da shekaru 88
  • Fafaroma Francis ya Rasu
  • Demokradiyyar Kwango Ta Haramta Jam’iyyar Josept Kabila A Kasar Saboda Hulda Da Yan Tawaye
  • Karamar Hukumar Birnin Kudu Ta Bada Tallafin Kudi Ga Manoman Alkama
  • Amurka : Ana ci gaba da zanga-zangar kyamar tsare -tsare da manufofin gwamnatin Trump
  • Dalilai 12 Da Ke Nuna Malaman Makaranta Na Da Muhimmanci Ga Al’umma (2)
  • Makarantar Bare: Shekara 20 dalibai na karatu a matsanancin yanayi