Aminiya:
2025-04-22@04:50:21 GMT

Motar hatsi ta kashe masu bikin Ista 5 a Gombe

Published: 22nd, April 2025 GMT

Hatsarin mota ya yi ajalin mutum biyar tare da jikkatar wasu takwas a yayin da suke bikin Ista a garin Billiri da ke Jihar Gombe.

Hatsarin ya faru ne a safiyar ranar Litinin, lokacin da direban wata babbar mota mai ɗauke da buhunan hatsi daga Jihar Adamawa ya auka kan dandazon jama’a da ke tsaka da shagalin bikin Ista.

An jingine wasanni a Italiya saboda mutuwar Fafaroma Francis An kama tsohuwa kan zargin lalata da almajiri a Bauchi

A wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na ‘yan sandan jihar, DSP Buhari Abdullahi ya fitar, ya bayyana cewa jami’an tsaro sun yi gaggawar kai ɗauki, inda suka kwashe waɗanda suka jikkata zuwa asibiti.

Sanarwar ta kuma ce bayan faruwar hatsarin, wasu fusatattun matasa sun cinna wa motar wuta tare da sace kayayyakin da ta ɗauko.

“Lokacin da ‘yan sanda suka kai ɗauki, matasan sun yi musu ruwan duwatsu, sai dai an shawo kan lamarin, kuma an dawo da zaman lafiya a yankin.”

Kwamishinan ‘yan sanda na Jihar Gombe, Bello Yahaya, ya bayyana jimami kan faruwar lamarin tare da miƙa ta’aziyya ga iyalan mamatan.

Shi ma Gwamnan Jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya, ya bayyana damuwa kan wannan iftila’i.

A cikin wata sanarwa da Babban Daraktan yada labarai na gidan gwamnati, Isma’ila Uba Misilli ya fitar, gwamnan ya bayyana cewa lamarin abu ne mai girgiza zuciya.

Gwamnatin jihar ta yi alƙawarin ɗaukar nauyin magani ga waɗanda suka ji raunuka, tare da tabbatar da cewa za a ɗauki matakan kare faruwar irin wannan matsala a nan gaba.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: hatsarin mota jihar Gombe

এছাড়াও পড়ুন:

Mai Ba Da Shawara Ga Jagora Ya Bayyana Cikakken Ikon Tawagar Masu Tattaunawan Iran A Zaman Shawarwari Da Amurka

Mai ba da shawara ga Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Masu sasantawa Iran a birnin Roma suna da cikakken ikon gabatar da shawara kan matsayin kasarsu

Ali Shamkhani mai ba da shawara ga Jagoran juyin juya halin Musulunci ya yi nuni da cewa: Masu gudanar da shawarwari na Iran sun tafi birnin Roma ne domin yin shawarwari karo na biyu da Amurka kan batun makamashin nukiliyar kasar Iran. Ya ce masu yin shawarwari na Iran suna da cikakken ikon gabatar da shawara kan matsayin kasarsu.

Shamkhani ya yi nuni da cewa: Masu shiga tsakani na Iran suna neman cimma cikakkiyar yarjejeniya bisa ka’idoji guda tara: tsanani, samar da lamuni, dage takunkumi, yin watsi da tsarin Libya/UAE, kaucewa barazana, gaggauta yin shawarwari, dakile masu shirga karya kan Shirin makaman nukiliyar Iran -irin haramtacciyar kasar Isra’ila- da saukaka zuba jari. Iran ta zo ne domin cimma daidaiton yarjejeniya, ba ta mika wuya ga bakaken manufofin Amurka ba.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Motar hatsi kashe masu bikin Ista 5 a Gombe
  • Bikin Ista: Hatsarin mota ya laƙume rayuka 5 a Gombe
  • Babu Wata Suka Da Za Ta Hana Gwamna Dauda Lawal Aiwatar da Ayyuka.
  • Ambaliya ta kashe mutum 3 ta lalata hekta 10,000 na shinkafa a Neja
  • Tawagar Gwamnati Ta Kai Ziyara Filato, Ta Sha Alwashin Kawo Karshen Kashe-kashe A Jihar
  • Mai Ba Da Shawara Ga Jagora Ya Bayyana Cikakken Ikon Tawagar Masu Tattaunawan Iran A Zaman Shawarwari Da Amurka
  • Putin ya umarci tsagaita wuta a Ukraine albarkacin bikin Ista
  • ‘Yan Sandan Sun Ceto Wasu Mutane Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Zamfara
  • Gwamna Abdulrazaq Ya Bukaci Kiristoci Da Su Tuna Da Darussan Lokacin Ista