HausaTv:
2025-05-12@18:49:14 GMT

Iran ta yi ta’aziyya game da rasuwar Paparoma Francis

Published: 22nd, April 2025 GMT

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya mika ta’aziyya game da  rasuwar shugaban ‘yan darikar katolika na duniya Paparoma Francis.

A wani sako da ya aike a jiya Litinin, Pezeshkian ya ce Paparoma Francis a matsayinsa na shugaban darikar Roman Katolika ya sadaukar da rayuwarsa gaba daya wajen yada koyarwar Yesu Almasihu.

Shugaban ya ce Paparoma ya yi kokari wajen samar da zaman lafiya a duniya, da yekuwar samar da adalci, da ‘yanci, da mu’amala da tsaro a tsakanin addinai.

Daya daga cikin shi ne bayyanannen matsayinsa na yin Allah wadai da kisan gillar da gwamnatin Isra’ila ke yi a Gaza da kuma kiran da ya yi na kawo karshen kisan kiyashin da ake yi wa mata da kananan yara Falasdinawan da ba su ji ba ba su gani ba.

A jiya Litini ce Cocin Vatican ta sanar da rasuwar shugaban majami’ar katolika na duniya, Fafaroma Francis yana da shekaru 88 a duniya.

A shekarar 2023 ne cocin ya zabi Fafaroman, wanda asalin sunansa shi ne Cardinal Jorge Mario Bergoglio a matsayin wanda zai jagorance ta, bayan saukar Fafaroma Benedict XVI daga kan mukamin.

Fafaroman ya rasu ne bayan fama da doguwar jinya, inda a baya ya shafe makonni a wani asibiti, inda aka bayyana cewa yana fama da sanyin hakarkari mai tsanani.

Francis, shi ne Paparoma na 266 na Cocin Roman Katolika, kuma an bayyana cewa ya rasu ne sakamakon bugun jini.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Jagora Ya Jaddada Wajabci Daukan Matakan Kalubalantar Zaluncin ‘Yan Sahayoniyya

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Dole ne duniya ta dauki matakin kalubalantar laifukan ‘yan sahayoniyya da magoya bayansu kan zaluncin Gaza

Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei, yayin da yake karbar bakwancin dimbin ma’aikata a yau Asabar, a daidai lokacin da ake gudanar da bukukuwan “Makon ayyuyka da Ma’aikata” ya bayyana cewa: A yau duniya ta shaida yadda ake daukar manufofin son zuciya kan wasu kasashe.

Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya ci gaba da cewa daga cikin wadannan manufofi na son zuciya da ake aiwatarwa a yau akwai kokarin mantar da al’umma batun da suka shafi Falasdinawa, yana mai cewa: Kada al’ummar musulmi su kuskura wannan kyale hakan ya faru, domin ko dan bai cancanci a karkatar da hankulan al’umma daga kan al’amuran da halin tsaka mai wuya da Falasdinawa suke ciki a wannan rayuwa musamman ta hanyar yada jita-jita da maganganu iri-iri, ta hanyar bullo da sabbin lamurra da kuma amfani da sabbin kalmomi da ba su da alaka da batun Falastinu, sannan suma Falasdinawan bai kamata a dauke hankulan su muhimman hakkokin da suka doru kansu ba.

Jagoran ya ci gaba da cewa: Laifukan da yahudawan sahayoniyya suka aikata a Gaza na Falastinu, ba wani abu ne da za a yi watsi da shi ba. Dole ne duk duniya ta tsaya kyam wajen kalubantarsa.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Sin Ta Fitar Da Takardar Bayani Game Da Matakan Cimma Nasarar Sassan Tsaron Kasa
  • Fafaroma Leon na 14 : Ina matukar bakin cikin abinda  ke faruwa a Gaza
  • Putin  Na Rasha Ya Gana Da Shugabannin Afirka Akan Batun Tsaro
  • Shugaban Putin Ya Gana Da Sisi Don Karfafa Harkokin Kasuwanci Tsakanin Kasashen Biyu
  • Kaduna Ta Gano Ma’adanai 73, Yayin Da Take Neman Masu Zuba Jari
  • Jagora Ya Jaddada Wajabci Daukan Matakan Kalubalantar Zaluncin ‘Yan Sahayoniyya
  • Shugaban Amurka Ya Ce An Cimma Yarjejeniyar Tsagaita Bude Wuta Tsakanin Pakistan Da Indiya
  • Sin Ta Nemi Indiya Da Pakistan Su Muhimmanta Zaman Lafiya Da Kwanciyar Hankali
  • Ra’ayin Al’umma Game Da Iyaye Masu Furta Muggan Kalamai A Kan ‘Ya’yansu
  • Sin Da Rasha Sun Fitar Da Sanarwar Hadin Gwiwa Game Da Zurfafa Dangantakar Abokantaka Ta Hadin Gwiwa Bisa Manyan Tsare-tsare A Sabon Zamani