Shugaban Kasar Iran Ya Bayyana Manufar Kasarsa Da Shirin Kare Muradunta A Duk Wata Yarjejeniya
Published: 22nd, April 2025 GMT
Shugaban kasar Iran ya jaddada cewa: A shirye suke su cimma yarjejeniya yayin da suke kiyaye muradun kasarsu
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya jaddada cewa: Iran a shirye take ta cimma matsaya bisa kayyade tsare-tsare tare da kiyaye moriyar kasarta, amma idan ba ta son yin shawarwari da ta daga kan matsayinta, tare da ci gaba a kan tafarkinta.
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian da yake jawabi a taron da gwamnonin kasar suka yi a ma’aikatar harkokin cikin gidan kasar a yau, ya yi jawabi kan shirin tattaunawa ba na kai tsaye ba da Amurka, yana mai cewa: Tun da fari gwamnatin Iran ta jaddada cewa tana kokarin karfafa dangantakar siyasa da tattalin arziki da kimiyya da al’adu da sauran kasashe, musamman ma kasashen musulmi da na makwafta. Iran tana kuma neman kyakkyawar mu’amala da sauran kasashe bisa mutunta juna.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Shugaban kasar Iran
এছাড়াও পড়ুন:
Ministan HarkokinWajen Iran Ya Tattauna Da Takwarorinsa Na Swaitzerland Da Pakistan Ta Wayar Tarho
Ministan harkokin wajen Iran ya tattauna ta hanyar wayar tarho da takwarorinsa na Switzerland da Pakistan
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya yi wata ganawa ta hanyar wayar tarho guda biyu a yammacin jiya Lahadi tare da ministocin harkokin wajen kasashen Switzerland da Pakistan.
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya gana da ministan harkokin wajen kasar Switzerland Ignazio Cassis ta hanyar wayar tarho a yammacin jiya Lahadi, inda suka tattauna kan alakar da ke tsakanin kasashen biyu da kuma wasu batutuwan kasa da kasa tare da yin musayar ra’ayi a kansu.
A yayin wannan tattaunawa, ministan harkokin wajen na Iran ya bayyana jin dadinsa ga rawar da kasar Switzerland ta taka a shawarwarin nukiliyar kasar cikin shekaru 10 da suka gabata, tare da bayyana wa takwaransa na kasar Switzerland sabbin ci gaba da suka shafi tattaunawar da ba na kai tsaye ba tsakanin Iran da Amurka.