Gwamnan Edo Ya Dakatar da Sarki Saboda Matsalar Tsaro A Yankinsa
Published: 22nd, April 2025 GMT
An kama shi ne sakamakon wani mummunan al’amari da ya faru kwanan nan, wanda ya yi sanadin mutuwar wani babban bafadan masarautar, John Ikhamate, lamarin da ya tayar da ƙura da kira na ganin an samu adalci.
Gwamna Okpebholo ya tabbatar wa da jama’a cewa gwamnatinsa na da niyyar yaƙar rashin tsaro a faɗin jihar, tare da ɗaukar mataki kan shugabannin al’umma da suka gaza yin abin da ya dace a yankunansu.
Ya kuma buƙaci sarakunan gargajiya da su mara wa gwamnatinsa baya wajen tabbatar da zaman lafiya da haɗin gwiwa da jami’an tsaro.
Gwamnatin jihar ta kuma buƙaci al’ummar Masarautar Uwano da su kwantar da hankalinsu tare da bin doka yayin da bincike ke gudana kan lamarin kisan.
Haka kuma ta gargaɗi duk wani shugaba da aka samu da hannu a aikata ko ɓoye laifuka zai fuskanci hukunci.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Dakatarwa Matsalar Tsaro Sarki
এছাড়াও পড়ুন:
Tinubu Ya Komo Nijeriya Bayan Ziyarar Mako 3 A Turai
A daren yau ne shugaba Bola Tinubu ya dawo Abuja bayan kammala ziyarar aiki ta makonni uku a Turai, inda ya gudanar da muhawara da manyan jami’an ƙasa da ƙasa don inganta dangantakar Najeriya a fannin tsaro da ci gaban tattalin arziki.
Jirgin shugaban ya sauka ne a Filin Jirgin Sama na Nnamdi Azikiwe a Abuja da misalin ƙarfe 9:50 na daren ranar, inda ya samu tarɓa daga manyan jami’an gwamnati, ciki har da Sakataren Gwamnatin tarayya, Sanata George Akume; Shugaban Ma’aikatan Shugaban ƙasa, Hon. Femi Gbajabiamila; Mai Ba da Shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu; Ministan Kasafin Kuɗi da Tsare-Tsare, Sanata Atiku Bagudu, da Ministan Birnin Tarayya, Barrister Nyesom Wike.
Zuba Jari Daga Kasashen Waje A Noman Zamani: Jigawa Ta Baje Kolin Aikin Noma A Abuja Gwamnati Ta Ware Wata 14 Don Kammala Aikin Hanyar Abuja Zuwa ZariyaShugaba Tinubu, wanda yayi tafiya tun a ranar Laraba, 2 ga Afrilu, ya fara ziyarar ne a Paris, Faransa, kafin daga bisani ya tafi Landan, Birtaniya.
Duk tsawon lokaci da yake wannan tafiya a Turai, shugaban ya ci gaba da tuntuɓar manyan jami’an gwamnati, yana bayar da umarnin aiwatar da muhimmancin al’amuran ƙasa, musamman ma na tsaro.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp