Aminiya:
2025-04-22@17:46:19 GMT

Hanyoyin da za a magance rikicin Filato — Masana

Published: 22nd, April 2025 GMT

Hare-haren da aka kai kan al’ummomin kananan hukumomin Bokkos da Bassa da ke Jihar Filato, sun sake jefa jihar cikin wani mummunan tashin hankali.

Sama da shekaru 20 ke nan wannan matsala ta ki ci ta ki cinyewa a jihar da ke yankin Arewa ta tsakiyar Nijeriya, inda take ci gaba da lakume rayukan mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba, tare da lalata dukiyoyi.

HOTUNA: Yadda Pantami ya kai wa Sheikh Jingir ziyarar ta’aziyya Gwamna ya dakatar da basarake kan satar mutane da yankinsa

Hare-haren baya-bayan nan, musaman daga ranar 28 ga watan Maris zuwa yanzu, a kananan hukumar Bokkos da Bassa da ke jihar Filato sun sun yi sanadiyar asarar rayukan mutane sama da 100 tare a jikkata wasu.

Daga ranar 28 ga watan Maris zuwa 2 ga Afrilu, 200 an kashe sama da mutum 50 tare da jikkata wasu da dama a Karamar Hukumar Bokkos.

A ranar Litinin din makon jiya ce kuma aka wayi gari da labarin cewa an sake kai wasu hare-haren a cikin inda mahukunta suka ce an aka kashe kusan mutum 50, wasu da dama kuma an garzaya da su asibiti, baya ga gidaje da sauran dukiyoyi da maharan suka banka wa wuta a cikin dare a gari a garin Zike da ke yankin Kwall a Karamar Hukumar Bassa.

Zuwa lokacin da muke kammala hada wannan ratoho hukumomin tsaro ba su ba su bayyana musabbabin hareharen da suka gano ba.

Ya zarce rikicin manoma da makiyaya — Gwamna Mutfwang

Tsawon shekaru, manoma da makiyaya suna zargin junansu da alhakin irin wadannan tashe-tashen hankula da suke faruwa.

Kungiyoyin al’ummomin da aka kai wa wadannan hare-hare sun zargi Fulani makiyaya da kai hare-haren, amma shugabannin makiyayan, sun musanta zargin.

Amma da yake jawabi a wajen taron baje kolin kayayyakin fasaha da aka gudanar a Abuja, Gwamnan Jihar Filato, Caleb Mutfwang, ya bayyana cewa hare-haren Bokkos sun wuce rikicin makiyaya da manoma, inda ya yi zargin cewa wasu mutane ne da suka himmatu wajen ganin sun tayar da rikici a jihar saboda son zuciya.

A wata hira da aka yi da shi a gidan Talabijin na Channels, Gwamna Mutfwang, ya ce shi ba mai nuna kabilanci ba ne, don haka ba ya son zargin wata kabila da laifin ta’asar da take faruwa.

 Dalilin da ya ki karewa

Bangarorin da ke zaman doya da manja sun bayyana cewa rashin gaskiya da siyasa ne matsalar farko, da ta sa rikicerikicen suka ci gaba da faruwa sama da shekaru ashirin da suka gabata a jihar.

Shugaban Kungiyar Raya Al’adu ta Bokkos (BCDC), Farmasum, ya yi zargin cewa, duk da cewa an sha kama wadanda ake zargi, amma ba a cika gurfanar da su ba a gaban kotu, shi ya sa matsalar ta ci gaba.

Ya ce, “Wannan batu zai ci gaba da lakume rayukan wadanda ba su ji ba, ba su gani ba, saboda babu bin diddigin wadanda ake zargi. Ko da mutum biyu kawai aka kama aka gurfanar da su a gaban kotu, hakan zai kawo sauki ga wadanda hare-haren suka shafa.

“Mutane na son ganin hukumomin tsaro sun dauki mataki, amma maimakon haka, masu aikata laifuka na ci gaba da aikata munanan laifuka, ba tare da an hukunta su ba, da sanin cewa za su tafi ba tare da an hukunta su ba.”

Yusuf Babayo Ibrahim, Shugaban Kungiyar Fulani Makiyaya ta Miyetti Allah (MACBAN) Reshen Jihar Filato, ya ce rashin adalci da hukumomi ke yi yana taimaka wajen yaduwar tashe-tashen hankula da sauran miyagun ayyuka a jihar.

“Babu wata manufa ta gaskiya a bangaren hukuma, laifi ana la’akari da shi ne idan ya shafi bangare daya, idan aka yi wa Fulani laifi, ba mai jin labari.

“Mu muna cikin jihar, amma ana mantawa da mu, babu wata manufa ta siyasa don magance matsalar, duk lokacin da wani laifi ya faru, nan take sai a ce Fulani ne. Babu adalci, wannan shi ya sa muke komawa baya, maimakon gaba,” in ji shi.

Abdullahi Garba, Shugaban Kungiyar Fulani ta Gan Allah (GAFDAN) Reshen Jihar Filato, Abdullahi Garba, ya ce kiran su baki da ake yi, shi ne ya kasance abin cece-kuce da ke haifar da rashin jituwa da makwabtansu.

“Wasu sun same mu ne a cikin yankunanmu daban-daban a wannan jiha, don haka me ya sa ake ce mana masu kwacen filaye? Wa muka kwace wa fili, ba za ka iya kira na dan kwacen fili ba, alhali a lokacin da nake cikin al’ummata, duk inda ka gani kasata ce, wannan batu na ci gaba da haifar da matsala.”

An yi zama fiye da sau 15

Masu ruwa da tsaki dabandaban sun sha yin kokari da bayar shawarwari don ganin an kawo karshen wannan rikicin, amma lamarin yana ci gaba da faruwa.

Mazauna al’ummomin da abin ya shafa, jami’an gwamnati, malaman addini, kungiyoyi masu zaman kansu, da sauransu sun hada kai, don maido da zaman lafiya tsakanin bangarorin da ke fada da juna. Amma duk da haka, kokarin ba ya haifar da sakamako a wasu wuraren.

Wani manomi a Mangu, Datu Mathias, ya bayyana cewa an gudanar da tarurruka da dama inda aka hada Mwagabul da Fulani a Mangu, domin gano matsalolin da kuma samar da mafitar da ta dace.

Ya ce sojoji da sauran jami’an tsaro sun hada su wuri guda, domin shawo kan lamarin. Su ma sarakunan gargajiya da jami’an gwamnati sun yi kokarin shawo kan matsalolin, amma duk da haka kalubale na ci gaba.

Ya ci gaba da cewa, bayan kowane taro, akan amince da matakan da suka dace, amma yawanci sukan kasa samar da sakamako mai dorewa.

Mathias ya ce, “Ba mu ji dadin lamarin ba, mun yi imanin cewa idan babu zaman lafiya, ba za a samu ci gaba ba, kuma mun yi imanin cewa zama tare da sauran jama’a, kuna amfana da juna, shi ne ya fi, lamarin yana shafar ci-gaba a yankinmu.”

Shi ma manomi Satmak Bala, ya ce sarakunan gargajiya na yawan kiran taron sulhu tsakanin bangarorin biyu. “Babban mai mulkinmu a Mangu ya ce mu rungumi zaman lafiya, mu guje wa tashin hankali.

“An yi kokari da dama wajen maido da zaman lafiya, hasali ma mun yi tarukan zaman lafiya sama da 15 a Mangu,” in ji Satmak.

Ya ce da ake fama da shi yana kawo cikas ga ayyukansu na noma. “Ba mu ji dadin hakan ba, a matsayina na manomi mai son yin noma, idan aka ci gaba da haka, ba zan iya zuwa gonata ba, wadda ita ce kadai hanyar samun kudin shiga, a wajena.

Wani makiyayi ne a Bokkos, Adamu Sa’idu, ya yaba da kokarin da kungiyoyi dabandaban da jami’an tsaro suka yi wajen magance matsalar.

Ya yaba wa kungiyoyi masu zaman kansu, da cewa, “Sun yi kyakkyawan aiki, sun sha kiran mu akai-akai don jin koke-kokenmu da ba da shawarwari.”

Sa’idu ya kara da cewa, a cikin shekaru biyu da suka gabata, kungiyoyi masu zaman kansu sun shirya tarukan zaman lafiya kusan 10. Rikicin na matukar shafar su, domin ba za mu iya yin kiwo a ko’ina ba, motsinmu yana da iyaka, kuma yana yin tasiri ga ci gaban yankin, idan babu zaman lafiya, babu ci gaba.”

Kawu Sabastine, manomi a Bokkos, ya yaba da kowarin masu ruwa da tsaki na ganin an shawo kan rikice-rikice a cikin al’ummarsu, inda “Wasu kungiyoyi masu zaman kansu, kamar Women for Women International, ECWA Peace Desk da sauransu, sun yi iya kokarinsu wajen wa’azin zaman lafiya a tsakanin ’yan asalin kasar da kuma Fulani, don a zauna tare ba tare da la’akari da kabila ko addinin mutum ba.

Yadda za a magance ta

Masana sun ba da haske, kan yadda za a warware rikicin, wanda suke ganin na makiyaya da manoma ne. John Danboyi, wani jami’in yaki da ta’addanci ne a Jos, ya ce, “Rikicin jihar nan yana ci gaba da ne saboda ba a taba magance tushensa ba,” inda ya kara da cewa yunwa da karancin damarmaki na sanya matasa shiga ayyukan ta’addanci.

“A duk lokacin da rikici ya barke, hukumomi suna raba kayan agaji ne kawai ga wadanda abin ya shafa, sannan su mance da batun, babu wanda yake bincikar hakikanin musabbabin lamarin, ko kuma masu da hannu a ciki.

“Idan aka ce rikicin addini ne gaba daya, ba gaskiya ba ne, addini na iya zama sanadi, amma galibi ana yin amfani da shi ne a matsayin hujja, don tayar da rikici,” in ji Danboyi.

Ya ce mafita ga kowane rikici ya ta’allaka ne ga wadanda abin ya shafa kai tsaye, inda ya bayyana cewa, “Wadanda abin ya shafa ne kawai za su iya fitar da hanyoyin magance matsalolinsu, idan aka kawo su kan teburin tattaunawa a kan rigima za su iya samar da mafita. Idan gwamnati ta bi wannan hanya, kuma da gaske ta magance matsalar rashin tsaro, zai taimaka sosai wajen magance rikici a Filato.”

Dokta Salisu Inusa Hassan, malami a Jami’ar Tarayya ta Kashere da ke Jihar Gombe kuma Ko’odinetan Nazarin Zaman Lafiya da Rikici na GST, ya bayyana cewa lalata gonaki da sace-sacen shanu ne manyan sabubban ta’azzarar rikice-rikice na manoma da makiyaya, kuma idan gwamnati ba ta dauki kwararan matakai ba, haka za a ci gaba da asarar rayukan wadanda ba su ji ba su gani ba.

“A wasu lokuta makiyaya kan lalata gonaki da gangan, lamarin da ke dagula al’amura, wani lokaci kuma, da gangan al’ummomin da suke noma sukan kashe shanun Fulani, lamarin da ke haifar da rikici tsakanin bangarorin,” in ji shi.

Dokta Salisu ya ce mafita ita ce, “Dole gwamnatoci su magance batun a aikace, ba tare da raba shi da kabilanci da addini.

“Muddin suka ci gaba da danganta shi da addini, matsalar za ta ci gaba ta haifar da tashin hankali, idan aka yi la’akari da yadda mutane suka fahimci addini.”

Dole ne kuma duk masu ruwa da tsaki da suka hada da gwamnati da na addini da na kabila su bi hanyar da ta dace tare da magance tushen matsalar.

Wani lauya mai zaman kansa kuma mai sharhi kan al’amuran yau da kullum da ke zaune a garin Jos, Barista Lawal Ishak, ya bayyana cewa “Duk wani rikici da yake faruwa a Jihar Filato, kashi 99 rashin adalci ne yake kawo shi.

“Matakan da suka kamata gwamnati ta dauka wajen kawo karshen wannan rikici sune kafa dokoki na musamman, kan idan abu ya faru ga hukumcin da za ayi.

“Kuma idan aka sami wani ya aikata laifin da aka ce ga hukumcin da za a yi, to a yi hukuncin. Idan ana samun irin wannan adalci, mutane za su daina daukar doka a hanunsu.”

Matakan da aka dauka don magance kashe-kashen Filato

A kokarin maido da doka da oda a yankunan da abin ya shafa, Babban Hafsan Sojin Kasa, Laftanar-Janar Olufemi Olatubosun Oluyede, a wani taron masu ruwa da tsaki a makon jiya a Bokkos, ya bayyana cewa, dole ne mutane su ajiye bambancin kabila da addini.

A cewar Oloyede, za a iya warware rikicin ta hanyar siyasa, “Gaskiyar magana, hukumomin tsaro za su iya tura dakaru zuwa Bokkos amma ba a samu zaman lafiya ba, jami’an tsaro ba su da yawan da za su kasance a ko’ina, don haka dole ne mu koyi zama tare.

“Zaman lafiya a Bokkos da Filato zai yiwu, amma fa idan muka amince da kawar da tashin hankali, muka rungumi zaman lafiya.”

A yayin wani zaman da ya yi da al’ummar da rikicin ya shafa, Gwamna Caleb Mutfwang ya jaddada muhimmancin mazauna su tashi tsaye su kare kansu daga mahara.

Ya ce, “Maharan mutane ne ba aljanu ko fatalwa ba, kuma masu rufa musu asiri su ma laifinsu daya. Ba zai yiwu mu zauna mu bar mutane su rika yi mana dauki dai-dai ba.

“Musamman matasanmu, wajibi ne al’umma mu rika lura abubuwan da ke kai komo a yankunanmu,” in ji gwamnan yana mai bayyana takaicin abin da ke faruwa, tare da alkawarin sake gyara yankunan da maharan suka lalata.

Kokarinmu na maido da zaman lafiya — Gwamnatin Filato

Kwamishinar yada labarai ta jihar, Joice Ramnap, ta ce tun a baya gwamnatin jihar ta yi kokari shawo kan rikicin, kuma har yanzu ba ta daina ba.

Ta ce, a kokarin da jihar ke yi na shawo kan rikicin a Bokkos da jihar gaba daya, ta hada kai da Gwamnatin Tarayya, inda ta ce an yi gyare-gyare ga ’yan gudun hijirar ta hanyar samar da kayan agaji, domin sake tsugunar da su.

Joice ta shaida wa wakilinmu cewa, “Ko da a sanar da kai hareharen na baya-bayan nan, Gwamna Mutfwang ya dauki kwararan matakan tabbatar da zaman lafiya kuma na tura jami’an tsaro zuwa yankunan da abin ya shafa, domin ganin irin wannan mummunan lamari bai maimaitu ba.

“A baya-bayan nan kuma, gwamnan ya kaddamar da wani kwamitin ba da shawarwari tsakanin addinai wanda zai jagoranci gina zaman lafiya a tsakanin kungiyoyin addinai a matsayin hanyar kawo zaman lafiya sannan ya koya wa mabiya addinai yadda za su kasance masu hakuri.

“Ana sa ran kwamitin zai ba gwamnati shawarwari kan yadda za mu samu zaman lafiya a tsakanin jama’ar Filato ba tare da la’akari da kabila ko addini ba,” in ji ta.

Kwamishinar ta kara jaddada bukatar jami’an tsaro su tabbatar da gurfanar da wadanda ake zargi da aikata laifuka, inda ta ce “idan an kama su a gurfanar da su a gaban kotu domin a kodayaushe ya zama darasi ga wasu da ke da niyyar aikata irin wannan laifin.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: hare hare Jihar Filato masu ruwa da tsaki da abin ya shafa ya bayyana cewa da zaman lafiya zaman lafiya A zaman lafiya a a zaman lafiya a gurfanar da jami an tsaro Jihar Filato jihar Filato an gwamnati la akari da

এছাড়াও পড়ুন:

Amurka : Ana ci gaba da zanga-zangar kyamar tsare -tsare da manufofin gwamnatin Trump

Ana sake gudanar da manyan zanga-zanga a manyan biranen Amurka a kan nuna adawa da tsare -tsare da manufofin gwamnatin Donald Trump.

Masu zanga-zangar na zargin gwamnatin da keta haddin kundin tsarin mulki da ‘yancin jama’a.

Wannan shi ne karo na biyu a wannan wata da dubban mutane suka yi tattaki a titunan Amurka domin nuna bacin ransu kan yadda Trump ke gudanar da mulkin kasar.

Korafe-korafen masu zanga-zangar sun hada da korar baki daga kasar da korar ma’aikata da gwamnati ke yi da kuma zargin tauye ‘yancin fadin albarkacin baki.

Kazalika masu zanga-zangar na nuna fishi kan irin ikon da Trump ya bai wa Elon Musk, attajirin duniya mai kamfanin Tesla – wanda ya kori ma’aikatan gwamnati sama da dubu 200, ya kuma rushe hukumomin agaji na Amurka da dama a duniya.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gina Al’umma Mai Kyakkyawar Makomar Bai Daya: Jigon Ziyarar Xi A Kudu Maso Gabashin Asiya
  • HOTUNA: An yi zanga-zangar adawa da matsalar tsaro a Filato
  • An Gayyaci Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran Abbas Aragchi Taron Makamashin Nukliya A Amurka
  • Amurka : Ana ci gaba da zanga-zangar kyamar tsare -tsare da manufofin gwamnatin Trump
  • Ruftawar gini ta kashe mutum 5 a Legas
  • Tawagar Gwamnati Ta Kai Ziyara Filato, Ta Sha Alwashin Kawo Karshen Kashe-kashe A Jihar
  • Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Yaba Da Zaman Tattaunawan Iran Da Amurka Zagaye Na Biyu A Birnin Roma
  • Ma’aikatar Lafiya Ta Yemen Ta Sanar Da Yawan Mutanen Da Suka Yi Shahada A Hare-Haren Amurka Kan Kasar
  • Kada Kanawa su bari rigingimun siyasa su hana su zaman lafiya — Shettima